← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 28

Sashe 20

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan fitar Mubeenah ita ma ta, tashi ta shiga bathroom tayi brush ta fice, kitchen ta nufa, amma taga Mami da su Mubeenah har sun gama komai sun jere a dining, ɓangaren fadilah ta nufa inda ta sameta ita da Mubeenah suna ta labarin abinda ya faru, a gurin get together da sukayi, zama itama tayi a falon, tana kallon TV idon tane kawai yake kan TVn amma hankalin ta ya tafi Madina, to ita rabonta da Amjad tun yana Nigeria ta kirasa, kusan 4 bayan tafiyarsa in several times amma baya picking, tana zaune can wani tunani yazo mata, ta buɗe datar ta, ta shiga Whatsapp tayi searching numbern Jaddah, ai kuwa tayi sa'a Jaddah tana online batayi wata-wata ba, ta kirata vedio call, bayan Jaddah tayi picking tace "Assalamu alaikum". Maya tace "wa alaikissalam kyakkyawar tsohuwa". Jaddah tace "to idan ma gatse kike min kin tadda gaskiya Maryam dan kema a kyawun nawa ne kika samu ka ɗan". Maya tayi murmishi tace "ai kuwa kam". Jaddah tace "yakike to?". Maya tace "lafiya alhamdulillah". Jaddah tace " ya su Mamin naku da su Mubeenah?". Tace " suna lafiya". Jaddah tace "ina kishiya ta da mijin ta?". Ai kamar jira fadilah take, ta taso ta wafce wayar a hannun Maya tace "mijina yafi ƙarfin ki Jaddah gara ma ki daina cemin kishiya dan babu abinda mijina zaiyi dake". Jaddah tayi dariya tace" to ai shi kuma yana sona". Mubeenah ta leƙo tace " faɗa mata dai Jaddah amaryar yah Ahmad". Jaddah tace "turamin account numbern ki, Mubeenah dole na saka Miki wani abu". Fadilah tayi dariya tace " Jaddah amma dan Allah ga Yah Amjad a gurin ki, ga Yah Ammar ki rasa wa zaki ce kina so sai mijina". Jaddah tace "to ai mijin naki duk yafi su nutsuwa da hankali, shi Ammar magana ma wani lokacin wahala take masa, kuma ba'a kallon dariyar sa kullum fuskarsa a murtuƙe". Fadilah tace "to ai shikkenan sai ki auri Yah Amjad". Jaddah tace "gaskiya bazan iya auren sa, ba saboda wannan bai min ba kwata-kwata shima ai banbancin sa da Ammar ɗin kaɗanne". Har fadeelah zatayi magana, Mubeenah tayi saurin cewa " Jaddah dan Allah ki nuna min Yah Amjad". Jaddah tace "baya nan ya fita gurin aikin da yakeyi ku dai kuci gaba da kula masa da Company yana aiki tuƙuru a nan saboda cigaban Company". Mubeenah tace "insha Allahu Jaddah". Jaddah tace "karku cika ni da surutu sai anjima ". Tana faɗan haka ta kashe wayar ta, suka miƙawa Maya da take zaune tana sauraron duk hirar tasu da Jaddah, wayar ta, Maya ta karɓi wayar ta, ta ajjiye ta akan kujerar, ta tashi ta nufi bathroom ɗin falon alwala ta ɗauro ta fito, ta shiga ɗakin fadeelah ta gabatar da Sallah bayan ta fito bata ga Mubeenah ba, itama wayar ta, ta ɗauka ta fice, ta nufi ɗakin su.......

*AYRAH*

Washe gari da safe da wuri ta, tashi ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast ta jere a dining, ta koma kitchen ta wanke duk wasu abubuwan da tayi amfani da su, ta gyare kitchen ɗin, kamar ba ayi amfani da shi ba, ta wuce ɗakin su Liyana ta taimaka musu suka shirya, tana zaune tana sakawa Khalil riga, tace "zanyi kewar ka Khalil". Khalil yace "aunty ai zamu dawo da wuri". Tace " to Allah ya dawo min da ku lafiya". Daga nan bata ƙara cewa komai ba, tace " ku fito kuje dining kuci abinci". Suka ce to, suka fito suka nufi dining, ita kuma ta koma ɗakin ta, tayi wanka ta shirya cikin ɗaya daga cikin bluen abaya wacce Amjad ya siya mata, tunda ta ciro kayan acikin kayanta, take hawaye, a bayyane tace "nayi kewarka Yah mufaddhal ɗina, ina fatan duk inda kake kana lafiya ta share hawayen da yake bin fuskar ta, tace " Ni kuma kalan tawa ƙaddarar kenan, rasa wa 'yanda nake so a rayuwa ta". Hijabi ta ɗakko maroon babba ta saka, ta nufi ƙofar fita, a dinning ta samesu kusan kowa ya hallara, tana zuwa ta ɗebi nata abincin ta faraci, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci tayi kuka sosai saboda yadda idon ta, ya kumbura, ba tare da ta kalli Abubakar ba, tace "good morning uncle ". Yace "morning ". A taƙaice, tanajin idanunsa suna yawo akan ta, tace " good morning aunty ". Jiddah tace"good morning Ayrah ". Ta maida kallon ta kan Jabeer tace "good morning uncle Jabeer ". Yace "morning " shima a taƙaice, abincin ta, tafaraci, bayan sun gama Abubakar ya fice shi da su Liyana zai ajjiye su a school sai ya wuce gurin aiki, basu daɗe da fita ba, shima Jabeer ya fita hannun sa riƙe da lab coat ɗayan Kuma riƙe da bakar jaka, shima ya fice, Ayrah bayan ta tattare komai ta kai kitchen ta, Jiddah ta fito itama zata wuce gurin aiki, Ayrah ta kalle ta, tace " aunty akwai wani surprising ɗin da zan miki, idan kin dawo ki shiga ɗaki na kan mirror zan ajjiye Miki abu ko menene kika gani, ki buɗe ke ka ɗai kuma ina fatan kiyi amfani da shi, Jiddah bata kawo komai a ranta ba, tace "tom shikkenan na Miki alƙawari". Ayrah tace "Nagode". Jiddah bata ce komai ba ta fice, misalin ƙarfe 2 na rana tana gurin aiki, Abubakar ya kirata, Yace " mata ya dawo ya duba ko ina bai ga Ayrah ba, cikin tashin hankali ta nufo gida ko da ta, ta iso sun duba ko ina agidan nan basu ga Ayrah ba, tuna abinda Ayrah ta faɗa mata kafin ta fita da safe, ya saka ta, nufar ɗakin Ayrah da sauri, tana shiga ta rufe ƙofar ɗakin, ta nifi gaban mirrorn Ayrah taga wata farar fefar Please cap ɗauke da rubutu, ta buɗe ta fara karantawa kamar haka:-.........

*Dan Allah ku daure mutanena ku shiga BAYAN DUHU DISCUSSION FORUM 📚 kuna comments domin karfamin guiwa, sannan dan Allah kuna liking da reacting, Love You all, thank you*.........

___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________

FEATURE WRITERS ASSOCIATION....

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*MER'EESHER ✍️*

Book 1

Page 18..........

_______ Jiddah ta fara karantawa kamar haka:- *Assalamu alaikum aunty nasan lokacin da zaki riski lattern nan nayi nisa da gidan ki, da farko ina so na fara da gode Miki, saboda taimaka min da kikayi kema ina Miki addu'ar Allah ya taimaka miki, kamar yadda kika taimake ni, aunty akwai abubuwan da na gani a gidan ki, kuma nakeso na taimaka miki kamar yadda kika taimaka min, kin banzatar da rayuwar yaranki da na mijinki bayan Manzon Allah da kansa yace duk kan ku ma kiwata ne kuma za'a tambaye ku akan abinda kuke kiyo, yanzu idan kika mutu Ubangiji ya tambaye ki ya kikayi da kiyon da ya baki, na yaranki da mijinki wace amsa zaki bashi? Aunty karki nemi duniya fiye da lahirar ki, idan har uncle ya miki rantsuwar bazai Miki kishiya ba, bakya tunanin zai iya neman matan banza saboda banzatar da shi da kikayi, aunty mijinki yana ƙaunarki shiyasa har ya miki rantsuwar bazai miki kishiya ba, amma ke da kanki kina neman kai mijinki wuta bayan kinkai kanki, aunty yaranki suna buƙatar ki, sosai basu san daɗin uwaba ko kaɗan, dan Allah aunty ki zauna ki gyara auranki kibar fifita neman duniya akan lahirar ki, and ni babu abinda yasaka na bar gidan ki sai alkhairi saboda inaso naga kin gyara rayuwar ki da ta mijinki da kuma ta yaranki, kuma ina fatan zakiyi hakan, daga ƙarshe ina mai ƙara gode miki da taimaka min da kikayi, kina cikin mutanen da bazan taɓa manta alherin su ba, a gareni Nagode sosai ki gaishe min da su Khalil zanyi kewarku sosai kuma ina fatan Allah ya ƙara haɗa fuskokin mu watarana*
Chapter 20 · 0% Book details