← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 28

Sashe 18

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai tunda suka fito ta lura ba hanyar gida ya nufa ba, amma bata da 'yan cin yin magana saboda Yah Ammar bashi da sanyin hali, a ƙofar wani gida yayi horn gateman ya huɗe musu gate suka shiga, ita dai tana son ta, tambaye shi amma takasa, saboda bai bata fuskar yin tambayar ba, bayan ya gama parking ya kalle ta, Yace "fita muje". Cikin sanyin murya tace "ina ne, nan ?". Ya wani kalle ta ya haɗe rai Yace "ban sani ba". Tace "dan Allah ni kam Ya Ammar ka kaini gida". Ya juyo ya kalle ta, kamar bazaice komai ba, sai kuma ya haɗe rai Yace "zaki fita ko sai na bigeki". Ta tura baki ta buɗe motar ta fice, shi dariya ma ta bashi yadda ta tura bakin, shima fita yayi, ya wuce tabishi a baya, knocking yayi basu da daɗe ba, wata mata ta buɗe ƙofar tana kallon su, fuskar ta, ɗauke da fara'a tace "Yah Ammar bissimillah ku shigo mana". Ta faɗa yayinda ta juya ciki, suka shiga suka zauna akan kujera, ta juya da fara'a tana kallon Maya tace "sannu sis Yakike?". Maya tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ta maida kallon ta kan Ammar tace "Yah Ammar ai da kasanar da mu da baƙuwa zaku zo, sai mu shirya mata abubuwa". Yah Ammar yace "karki damu hafsat". Hafsat ta kalli Maya tace "Maya ko?". Maya tace "Erh nice". Hafsat tana murmushi tace "ina zuwa ". Bata daɗe da tafiya ba, sai ga mijin ta ya shigo hannun sa riƙe da na, 'yar su Amal, suna shigowa ya yarinyar ta sake hannun Daddyn ta tafi da gudu ta rungume, Yah Ammar tace "i miss You uncle". Ya ɗago fuskantar ta Yana dariya Yace "miss You too Amal". Fahad ya zauna yana kallon, ta sunkuyar da kanta ƙasa tace "ina yini" Yace "lafiya Madam ya gida". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ya kalli Yah Ammar Yace "itace Maya ko?". Yah Ammar yace gata nan ka tambaye ta mana". Maya tace "nice" tana miƙa hannu a Amal, Amal ta je ta gunta, can wayar Maya tayi ƙara alamar shigowar massage, ta duba bayan ta karanta massage ɗin, ta ɗaga kai ta kalleshi, ita wallahi bata taɓa tunanin ma yana da numbern ta ba, ta tashi ta kama hannun Amal tace "muje mu ɗakko saƙo a mota". Suka fita basu daɗe ba suka shigo da ledoji har guda biyu, suka zauna Amal tana kallon ta, tace "aunty wannan duka nawa ne?". Maya ta ɗaga mata kai tana mata murmushi, hafsat ta kawo musu abinci da drinks hadda snacks sosai, Amal ta sake da Maya har tana tambayar ta yaushe zata dawo, lokacin da Maya zasu tafi, hafsat ta bawa Maya turaruka masu ƙamshi da tsada, ta mata godiya, sannan suka wuce gida.........

*AYRAH*........

Tana zaune akan sallaya tunda ta idar da sallar azahar bata, tashi a gurin ba, sai tunane-tunane take, ta rasa meyake mata daɗi a zuciyar ta, taji an buɗe ƙofar ɗakin ta, an shigo da sauri ta tashi tana kallon ƙofar gaban ta na faɗuwa, ƙarisowa yayi ya zauna a bakin gadon yana kallon ta, ita kuwa sai ja da baya take kamar wacce ta kalli mutuwa, tajinginu da bangon ɗakin, tana kallon sa, hawaye ya fara zirya a idanun ta, ya gyara zama yace "bazan Miki dole ba Ayrah amma inaso ki amince da kanki, ki mallaka min kanki, zan iya fitar da ke daga gidan nan, na mallaka Miki gida naki na kanki, na siya Miki mota da duk wasu abubuwan more rayuwa amma idan kin amince zakina biya min buƙata ta ko wani lokaci ". Ayrah tace "dan Allah uncle kayi hakuri ka fice min daga ɗaki, uncle wallahi ko duniyar nan zaka bani bazan iya aikata zina ba". Ta faɗa tana share hawayen da yake bin ƙuncinta, Ya kalle ta kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya fice daga ɗakin, Yana fita, ta shiga bathroom ta rufe ƙofar ta jingina da ƙofar tana kuka, cikin kuka tace "wannan wace irin rayuwa ce ƙaddara ta jefo ni ciki, Yanzu haka zan cigaba da zama ana farautar mutunci na?". Ta ma kanta tambayoyin da bata da amsoshin su, sai da tayi kukan ta mai isar ta, kafin tayi wanka, ta fito, ta shirya cikin doguwar rigar material, ta saka hijabin ta, Yanzu kam babu abinda ta shafa a fuskar ta, ta fita, tana fita ta sameshi a main falo, shi da wani saurayi, kallon sa tayi, ta kauda kai kamar bata ga mutane a gurin ba, ta wuce, kitchen ta shiga ta fito da warmers ɗin da ta zuba abincin da ta girka na rana, ta fito da su ɗaya bayan ɗaya ta jere a dining, ta juya zata wuce, tana zuwa dai-dai inda suke saurayin ya ɗago ya kalle ta, ya yatsine fuska, Yace "ke baki iya gaisuwa bane? Ko gidan ku babu manya?". Maganar gidan su babu manyan ne ya tsaya mata a ranta, ta juyo ta kalle shi, kamar zatai magana sai kuma ta juya ta wuce, ya juya ya kalli Abubakar Yace "wacece ita?". Abubukar Yace "zamuyi magana akan ta daga baya, amma yanzu ka ɗauka sistern Jiddah ce". Baice masa komai ba ya tashi yana kallon Abubakar ɗin, Yace "barin shiga inyi wanka". Abubakar Yace "ok". Daga nan ya wuce. Ayrah tana shiga ɗakin ta, ta rufe ƙofar a ranta tana addu'ar Allah ya dawo da Jiddah yanzu, kwanciya tayi a kan gadon zuciyarta cike da tunane-tunane kala-kala har Bacci ya ɗauke ta, bata farka ba sai ƙarfe 5 na Yamma a mugun zabure ta tashi ta diro daga kan gadon, ta wuce bathroom wanka tayo ta ɗauro alwala bayan ta fito, ta shirya cikin riga da scate na Atamfah na Sa'adatu wanda mama ta bata, bayan ta shirya tana kallon kanta, a mirrow tace "Allah sarki mama Allah sarki Sa'adatu na Wallahi nayi kewarku sosai, ina ma nasan inda kuke yanzu da ban kasance cikin gidan nan ina fuskantar wannan mummunar barazanar ba". Ta ƙarisa maganar hawaye na bin ƙuncinta, tunawa da tayi batayi sallah ba, ya sakata saka hijabin ta brown, ta shimfiɗa sallaya ta fara gabatar da Sallah, bayan ta idar ta fice ta nufi kitchen, tana tsaye a kitchen ɗin tana girki, taji motsin shigowar mutum a mugun tsorace ta juya sai kuma taga wannan saurayin ɗazun, cup ya ɗauka ya fice, with out looking at her, sai 6:30 tagama girkin, lokacin Abubakar ya tafi ɗakko su, Liyana a school, har zuwa lokacin basu dawo ba, sai da tattare komai ta kai dining ta jera, ta kwaso na ɗazun, ta dawo da su, ciki, ta wanke ko ina, ta gyare kitchen ɗin kafin ta fice, taje tayi sallah,.........

***** Mama abu tana zaune a cikin gida ta zuba uban tagumi sai bin gidan take da kallo, tun lokacin da ma'u sukayi faɗa da Tanko har yau bata dawo gidan ba, tunanin ta duk ya tafi kan ma'u saboda kayan abincin ta ya kusa ƙarewa kuma dama Ma'un ce me siya mata kayan abincin, tunda suka dawo gidan nan, tana cikin wannan tunanin Ma'u ta shigo ko sallama babu, Mama Abu ta kalle ta, tace "ina kika shige ne 'yar albarka kwana biyu shiru?". Ma'u ba tare da ta kalli Mama Abu ba, tana cire gyalen kan ta, tace "tunda dai na dawo lafiya ai shikkenan, ni ba yarinya bace da za'a tsareni ana tambaya ta, ko ina naje". Mama Abu tace " Allah ya baki hakuri 'yar nan". Ma'u tace "Ameen"........

*AYRAH*

misalin ƙarfe 9 na dare tana zaune a falo tana kallo, ita da Liyana dan sauran yaran duk sunyi bacci, Ya shigo falon yana kallon Liyana yace "ke tashi kije ki kwanta dare yayi". Zuciyar Ayrah tai mugun bugawa saboda ita wallahi ba fahimtar kallon take ba, kawai dai tana yi ne, saboda bata son tafiya ɗakin ta, Abubakar ya bita, Liyana ta miƙe ta lalle shi tace "uncle Jabeer sai da safe". Bai kalle ta ballantana ya amsa, ita dai Ayrah still tana zaune akan kujera tana kallon da bata fahimta, Jabeer ya zauna a falon da system ɗin sa yana ta danne-danne, after some minutes ya ɗago ya kalle ta, yaga still idon ta yana kan TV suna zaune a gurin, har 11 ya kalle ta Yace"Madam marar gaisuwa ba zakije ki kwanta ba ne". Ta kalle shi, tace " sunana Ayrah kuma banjin bacci ne shiyasa". Yace "ok". Daga nan bai ƙara ce mata komai ba, har 12:00 wayar sa ce ta fara wringing yayi picking tare da sallama, daga ɗaya ɓangaren yace "mutanen US Yakake". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ɗayan yace " ɗazu Abdul yake faɗa min aika dawo Nigeria shine nace barin kira mu gaisa, Jabeer yace"ok thank you good night ". Tare da kashe wayar, bayan ya kashe wayar ya tashi ya ɗauki system ɗin sa, batare da ya kalli Ayrah ba ya kashe TVn yace"maza kije ki kwanta". Ba musu Ayrah ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin ta, jikin ta a sanyaye, ya bita da kallo, sai kuma shima ya wuce nasa bangaren..... Abubakar kuwa da sallamar sa ya shiga ɗakin Jiddah ya sameta, a kwance a kan gado, ya kalle ta, ya zauna a bakin gadon yace "baby inaso muyi magana ne". Ta buɗe ido ta kalle shi sai kuma ta rufe idon tace " kayi hakuri dan Allah, kabar maganar nan, sai gobe da safe, ni agajiye nake kuma bacci nake ji". Yace " amma Jiddah kinsan a matsayina na mijinki ina da haƙƙi a kan ki ko?". Tace " nasani but dan Allah kayi hakuri ka tafi ɗakin ka, ka kwanta darling, bacci nake ji". Tana faɗan haka ta ja duvet ta juya masa baya, jiki a sanyaye ya tashi ya fice daga ɗakin,.....
Chapter 18 · 0% Book details