Sashe 22
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Likitan ya ɗan yi shiru, sannan Yace"zai iya dawowa,Amma ba za mu iya cewa ga lokacin da zai dawo ba, Wasu abubuwa na iya dawowa a hankali, musamman idan ta samu natsuwa, Wani lokaci ko wani wuri, suna, magana ko wani abu da ya shafi abubuwan da ta taɓa fuskanta a baya zai iya tayar mata da wani ɓangare na tunaninta".Abbie Yace"Kenan ta manta da mutanen da ta sani?". Likita Yace" Erh Hakan na iya faruwa, Amma ba lallai ne ta manta da kowa ba, Tana iya tuna wasu mutane sosai, ta kasa tuna wasu, ko kuma ta tuna wani abu amma takasa tuna lokacin da abun ya faru".
Likita ya ɗaura da cewa "Abu mafi muhimmanci yanzu shi ne kada ku matsa mata da tambayoyi, Kada ku tilasta mata ta tuna abin da ba ta iya tunawa,Ku ba ta lokaci, da kulawa da kwanciyar hankali, Idan tunaninta zai dawo, ya fi kyau ya dawo a hankali, saboda haka, idan tace ba ta san wani abu ba, ku yadda da ita kada ku ɗauka cewa tana yi ne don ta ɓoye wani abu. Ƙwaƙwalwarta ce ke buƙatar lokaci".
Abbie Yace "insha Allahu zamu kula kuma zamu kiyaye da dukkanin abubuwan da ka faɗa, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ". Dukkanin su suka amsa da "Ameen ". Daga nan suka masa godiya tare da sallama suka fice, Abbie ne ya wuce zaije yayi making payment, bayan yayi, Ya dawo ya wuce room ɗin da likitan Yace suje Ayrah tana can, Abbie ya shiga bakinsa ɗauke da sallama ko da ya shiga, ya samu Maya tana zaune abakin gadon, ita kuma farhan tana zaune akan kujera, ko da ya ƙarisa ya tsaya yana ta kallon Ayrah can kuma ya kalli Maya yace " Yanzu ni zan wuce gida ɗaya daga cikin ku tazo muje, ta tafo muku da abubuwan da zaku buƙata sai Aliyu ya dawo da ita, dan ya kamata Ku kwana a gurin ta, bai kamata a barta ita kaɗai ba". Maya tace "Abbie ku tafi da farhan". Yace "Tom shikkenan farhan ɗin Abbie tashi mu tafi". Farhan tace "Tom shikkenan aunty Maya sai na dawo". Maya tace "Tom Abbie sai da safe". Yace "sai da safe, Maryam Allah ya bata lafiya". Tace "Ameen" daga nan suka fice suka nufi gida shi da Farhan, Maya kuwa ta zubawa Ayrah ido tana ta bin ta da kallo, a ranta tana jin ƙaunar yarinyar sosai kamar wacce ta daɗe da sani,................. Kwanan su biyu aka salla mesu suka koma gida, a kwana biyun da sukayi kaf gidan babu wanda bai zo ya zauna da Ayrah ba, duk da bata tambayar su, wacece ita da kuma matsayin ta agurin su ba, amma ta sake da su sosai, ......ta na kitchen tana girki ita da Farhan da yake Farhan itace age mate ɗin ta, amma Maya ta girme su, Maya zata kai 26 su kuma baza su wuce 21 ba, Farhan ta kalle ta, tace "sis kinsan menene?". Ayrah tace "no sai kin faɗa". Farhan tace "anjima zamuje mu miki registration na Neco, mu dawo nasan kafin a fara zaki warware sosai". Ayrah ta juya ta kalli farhan bayan ta rufe towan da take girkin, tace "Masha Allah sis gaskiya Nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairi ". Farhan tace"Ameen ya Allah, amma na tambaye ki mana?". Ayrah tace "ok Allah yasa dai nasani ". Farhan tace "kiyi hakuri idan kinji tambayar tawa wata iri". Ayrah tace "karki damu ki tambayeni kawai". Farhan tace "zaki iya tuna gidan ku da kuma iyayenki?". Ayrah tace "bana da iyaye bansan inda suke ba". Farhan tace "amma kin taɓa makaranta?". Maya da yanzu shigowar ta tace "Farhan kin taƙurawa ƙanwata da tambayoyi fah". Ayrah tace "ƙyale ta dai aunty ". Maya ta ɗauki cup ta buɗe pridge ta ɗauki goran ruwa, tace "dan Allah Farhan ki daina taƙurawa ƙanwata da tambayoyi ". Farhan tace "insha Allahu bazan ƙara ba aunty Maya". Maya tace"better". yayinda take ficewa". A ranar suka je suka yiwa Ayrah registration ɗin Neco, bayan sun dawo Maya tana zaune a ɗakin ta, tana vedio call da mubeenah, Maya tayi murmushi tace "Ni na manta ma ban tambaye ki ba ina Yah Ammar fah?". Mubeenah tace "ai shima ya tafi tun ranar ya koma gun aiki pass ɗin sa ya ƙare". Maya tace "ayya Allah sarki". Dai-dai nan Ayrah ta tura ƙofar ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, Maya ta amsa mata, tana murmushi, Mubeenah tace "ƙanwar taki ce ta shigo?". Maya tace "Erh mana". Mubeenah tace "bazaki nuna min ita ba". Maya tace "barin nuna Miki ita wallahi kuwa kuna kama". Tana faɗan haka ta kalli Ayrah tace " kizo ku gaisa". Ayrah ta, taso ta zauna a gefen Maya tana kallon Mubeenah, Mubeenah tana kallon Ayrah ta miƙe da sauri ta fara cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Maya tana tambayar ta Lafiya amma, ko tsayawa amsa mata, ba tayi ba ta fashe da kuka, Maya tace "why are crying Mubeenah what happened ?". Sosai Mubeenah take kuka ko sauraron Maya bata yi ba, ta kashe wayar...............
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
Book 1
Page 19...........
______ Mubeenah na kashe wayar Ayrah ta tsaya tana kallon Maya, tace " meyasa take kuka?, ko dai ta Sanni ne?". Maya tace " kawai taga yadda kuke kama ne may be ya saka ta tsoruta". Ayrah tayi murmushi tace "aunty to ai ance kowa ma yana da masu kamar sa guda 7 a duniya". Maya tace "hakane kam". Haka Maya ta zauna a Abuja ta gagara komawa Kano, saboda Ayrah da kuma yadda suka shaƙu kwana biyun nan, babu abinda bata siyawa Ayrah ba tunda ga kan kayan sakawa, shower gels masu kyau da tsada , turaruka da dai sauransu, idan ka kalli Ayrah yanzu bazaka ce Ayrahn mama Abu bace, saboda yadda tasamu nutsuwa da kwanciyar hankali kuma daula da arziki suka zauna a jikin ta, tayi wani fresh kyaun ta ya ƙara fitowa hasken ta ya ƙara gyaruwa,.......