Sashe 21
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiddah tasaka hannu ta share hawayen ta bayan ta gama karantawa, a fili ta furta "Nagode Ayrah Nagode sosai da taimakawa rayuwa ta sa kikayi ina fatan Allah ya tsare ki a duk inda kike Allah yasa ki faɗa hannu na gari". Tana gama faɗan haka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya a ranta, tace"lallai na yadda da duk wanda ka taimaka indai kayi da zuciya ɗaya, shima watarana zai taimake ka". Sai da ta gama kukan ta kafin ta tashi ta fito, ta samu Abubakar da Jabeer a zaune a falo, fuskokin su ɗauke da damuwa, suna kallon ta suka fara tambayar ta "Lafiya?". Ta yi murmishin ƙarfin hali tace "Ayrah ta barmin saƙo tace ta tafi bazata dawo ba tana fatan Allah ya haɗa fuskokin mu watarana". Take Abubakar ya fara gumi, Yace "bayan nan babu abinda ta faɗa miki?". Jiddah tace "shikkenan ko dai dama akwai wani abu ne?". Yace "babu komai ina nufin ko ta faɗa miki gurin da taje ne?". Jiddah tace "bata faɗa min ba". Tana faɗan haka ta wuce ɗakin ta, wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigar Atamfah ta fito ta nufi kitchen zata ɗaura musu abinci kamar wacce akace ta juya tana juyawa ta kalli dinning sai taga warmers a jere, batasan lokacin da fara hawaye ba, kawai ta juya ta nufi ɗakin ta, a ranar haka ta yini jikin ta babu ƙarfi, misalin ƙarfe 5 na yamma tana kitchen tana girki Liyana ta shigo da gudun ta, turus tayi ta tsaya tana kallon Jiddah tace "momy yau kuma kece me mana girki mommy ina aunty?". Jiddah ta juyo tana murmishi tace "nice me muku girki yau, aunty kuma yau maman ta, ta kirata ta tafi gidan su amma zata dawo". Liyana tace "to Allah ya dawo da ita lafiya". Jiddah tace "Ameen". Ta juyo tana kallon ta, tace "muje na taimaka muku kushirya sai kuzo muyi dinner daga nan mu muje mu sha ice cream". Leenah da basu da daɗe da ƙarisowa ba, suka rungume Jiddah suna farinciki, ta rungume su tayi tana hana hawayen idonta zubowa saboda kar su gani, bayan sun shirya sun fito Sunyi dinner, Jiddah tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar shadda light blue, sai ƙamshi take yi da veil ɗin ta white, tayi kyau sosai, ta fito daga ɗakin ta, ta wuce ɗakin Abubakar, ta sameshi yana zaune a bakin gado yana danna system ɗin sa, da mugun mamaki ya ɗago yana kallon ta har ta ƙariso ta zauna a gefen sa tace "Barka da aiki Darling". Yace "Barka dai sweetheart". Tace "dama magana nake so muyi". Ya ɗago kansa yana kallon ta yace "ina jinki sweetheart ". Hawayen da take riƙewa ne suka fara zubowa, ta zame ƙasa tace " nasani na cutar da kai sosai na cutar da yaran mu, ban kasance uwata tagari ba kuma ban kasance mata gari a gareku ba, wallahi nayi da nasani kuma ina roƙon ka dan Allah kayie hakuri ka yafe min , nayi maka alƙawarin zan kasance muka mata tagari kuma uwa tagari, zan kula da kai kuma zan kula da yarana". Ya saka hannun sa ya ɗago ta ya dawo da ita kan gadon ta zauna a gefen sa, ya juyo yana facing ɗin ta, ya saka hannu ya share mata hawayen fuskar ta, yace "na yafe miki sweetheart dan Allah ki daina kuka kinji, Allah ya miki albarka". Tace"Ameen Nagode ". Sai kuma ta fara murmushi tace "zamuje shan ice cream da yarana kaima kabar aikin nan sai mun dawo". Yace " da dare nan". Tace "wani dare shiyasa ma mukayi dinner nan mu da wuri yanzun fa duka-duka 8 ne". Yace "ok barin shirya ". Tace " barin taimaka maka ka shirya da wuri mu tafi". Ta faɗa tana tashi ta nufi wardrobe tana duba masa kaya, ya bita da ido yana jin wani sanyi da nutsuwa suna ratsa zuciyar sa, a ransa ya na yiwa Allah godiya da baibarsa ya aikata zina da Ayrah ba, kuma yana ƙarayiwa Allah godiya da ya canzawa matar sa ra'ayi, ta juyo ta kalle shi, tace "gobe zan ajjiye aiki ". Yace" Meyasa ". Tace "saboda kula da ku yafi min aikin muhimmanci, kuma ai dama babu abinda na nema na rasa agidan nan, gara na fara business ". Yace"Tom shikkenan Allah ya taimaka kuma Allah ya Miki albarka". Tace "Ameen mijina farinciki na"..........
*MAYA*
Suna zaune a dining suna dinner ta kalli daddy tace "daddy gobe insha Allahu idan su Abbie suka zo zan bisu mu tafi Abuja". Daddy yace "Allah ya kaimu amma yaushe zaki dawo". Tace "bazan daɗe ba daddy ". Mubeenah tace" sisy yanzu tafiya zakiyi ki barni". Maya tace "to kishirya mu tafi mana". Mubeenah tace "ki bar waye a Company?". Maya tai shiru bata ce da ita komai ba, ai kuwa haka akayi, bayan su Abbie sun zo anyi Engagement ɗin Mubeenah da Aliyu, ta shirya kayan ta tabisu Abbie zuwa Abuja,........... Maya tana zaune a falo ta zubawa photon Amjad da Aliyu ido wanda tun suna yara akayi photon, farhan ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, ta ƙariso ta zauna a gefen Maya, Maya ta juya ta kalle ta, tace " Meyasa babu photon yah Amjad ko guda ɗaya a palon nan sai wanda suke yaran can". Farhan tace "shiya ɗebe su kaf gidan nan babu palo ko ɗakin da yake ɗauke da photon sa idan ba nasa ba, sai ɗakin Abbie, Maya tace "ok". Daga nan bata ƙara cewa komai ba.........
*AYRAH*
bayan ta bar gidan direct tashar mota, ta nufa, duk da batasan inda zataje ba, hannun ta ɗaya riƙe da akwatin ta tanaja ɗaya kuma ɗauke da jakar kayan ta, wacce ta baro gidan Mama Abu da ita, tana zuwa taji ana Abuja saura mutum ɗaya, mutumin ya tambaye ta yace"Madam Abuja ko Kaduna?". Tace "Abuja ". Yace "shiga mota ta cika". Ta shiga, ya saka mata akwatin ta a Boot jakar ta kuma ta shiga da abunta, motar su ta tashi sai Abuja.......... Ranar da suka isa dai a tasha ta kwana, anan ma aka sace mata, akwatin ta, ya zama daga ita sai jakar kayan ta, yanzu ma da yake misalin ƙarfe 9:00 na dare tafiya kawai take yi ba tare da tasan inda zataje ba, ta biyo ta wani layi inda maza suke zazzaune kana kallon su kaga 'yan iska 'yan shaye-shaye, sai da ta ƙariso sai tin su, ɗaya daga cikin su, yace "kunga wata cika" wani yace" gata kuwa kamar ita tai kanta, lallai kuwa yau zamu more". Tana jin haka ta fara sauri, ɗayan yace "ku tashi mu bita kar ta gudu". Ayrah najin haka ta fara gudu sosai kamar ƙafarta zata cire, su kuwa tuni sun tashi sun fara Binta da gudu, sosai take gudu amma basu kamota ba, ta juya tana kallon su, tana gudu ai kuwa ta gwaru da wani gini ta faɗi a gurin, sukuwa suna kallon haka suka ƙara gudu........
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
Book 1
Page 19.........
Ga nin sun ƙara gudu suna ƙoƙarin cin mata, ya saka ta saurin miƙewa, ta dafe goshin ta da yake zubda jini, ta cigaba da gudu, batayi gudu mai yawa ba ta ƙarisa bakin titi, ganin suna tun karota yasaka ta gyara goyon jakar da take bayan ta, motar da take tafowa ta fara tsayarwa, a ranta tana addu'ar Allah yasa motar ta tsaya, amma motar bata tsaya ba, ta wuce ta, take ta fara tsaida ta bayan ta, tanayi tana juyawa tana kallon su, hannun ta ɗaya dafe da goshin ta, ai kuwa taci sa'a ta tsaya, da sauri ta tsallako tana nufowa Maya tana cewa "dan Allah ki taimake ni Marainiya ce bani da kowa bansan kowa ba, wasu ne suka biyoni zasu min........". Bata ƙarisa wata mota da fito a da mugun gudu ta ɗeba ta, faɗi, sosai gaban Maya ya faɗi ta fito tana kuka, kafin kace me mutane sun taru agurin tuni me motar da ya bigeta kuma ya gudu, ganin Maya tana ta kuka suka tambaye ko ta san tane, tace "sistern ta ce". Tuni aka saka mata ita a mota suka wuce asibiti wani na miji guda ɗaya kuma ya wuce police station, ai kuwa sai da police suka shiga kafin aka fara aiki a Ayrah, Maya tana tsaye a bakin room ɗin da aka shiga da Ayrah, tana ta kaiwa da komawa, wayar hannun ta ce tafara wringing picking tayi tare da sallama, daga ɗaya ɓangaren Abbie Yace "Maryam kina ina ne, har yanzu dare yayi baki dawo gida ba?". Tace" Abbie na ina asibiti ne". Yace "subhnallahi Maryam lafiya dai ina?". Tace "lafiya ƙalau Abbie wata yarinya ce ta samu accident a hanya shine na kawo ta hospital". Yace "ayya Allah ya bata lafiya barin zo nima sai naga jikin na ta". Tace "to Abbie barin tura maka address ɗin". Yace "ok". Tare da kashe wayar, ita kuma ta tura masa address ɗin,bayan wani lokaci sai ga Abbie da farhan sun ƙariso, farhan ta ƙarisa ta rungume Maya tace "aunty Maya ya jikin nata?". Maya tace "alhamdulillah sun fito da ita ma sun kai ta wani room". Farhan tace "ayya Allah ya bata lafiya". Likita ne ya ƙariso ya gaida Abbie tare da sanar musu yana buƙatar ganin su, a office ɗinsa, yana tafiya dukkanin su suka bishi a baya zuwa office ɗin nasa, Abbie ya zauna akan kujera , Maya ma ta zauna farhan kuma ta tsaya, Likitan yana zaune a gabansu, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya fara magana. “Alhamdulillah, yanayin lafiyarta ya fara daidaituwa. Amma akwai wani abu da ya kamata ku sani".dukkanin su suka maida hankali gareshi, Yace" Raunin da ta samu a kanta ya shafi ƙwaƙwalwarta,a yanzu tana fama da abin da ake kira partial amnesia, wato wani ɓangare na ƙwaƙwalwarta ya samu matsala, Ba wai ta manta komai ba ne, Za ta iya tuna wasu abubuwa, amma akwai wasu abubuwan da ba za ta iya tunawa ba". Abbie Yace "Shin za ta iya dawo da tunaninta?".