Sashe 3
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan ta gama da ka yajin ta tattara wanke-wanke ta fara, bayan ta gama tayi alwala ta shiga ɗaki domin lokacin sallah yayi, ɗan kwalin ta, ta shimfiɗa ta fara sallar ta, tana idarwa ta juya ta kalli ma'u tace "ma'u wai Meyasa bakya sallah ne, ma'u kiji tsoron Allah ki tsaida sallah wallahi idan kika gyara sallar ki Allah zai gyara miki dukkanin al'amuranki". Ma'u tace "wallahi idan baki rufe min baki ba na tashi sai nayi ƙasa -ƙasa dake a gurin nan shegiya karuwar banza". Shiru tayi bata ƙara cewa da ita komai ba, mama abune ta shigo ɗakin, hannun ta ɗauke da kwanon abinci, ta miƙawa ma'u tace "gashi kici idan kin ƙoshi ki rage mata". Ma'u tace "mama zan iya cinye abincin nan fah". Mama tace"shikkenan bari a tsakuro mata ka ɗan". Ma'u bata ƙara cewa komai ba, haka itama Ayrah mama ta nufi ƙofar fita, taje ta ɗibo mata abincin ka ɗan hakan ma ba'a saka mai ba ruwa kawai aka saka kaɗan aciki a madadin mai sai yaji, Ayrah ta karɓa tace "mama Nagode".
Mama ta miƙa mata 5k in data bata ɗazu tace "gashi kina gamawa kije shagon lauwali ki haɗo mana kayan abincin siyar wa yau jollof in taliya zamuyi ta siyar wa". Tana kaiwa nan ta fice bata jira amsar da Ayrah zata bata ba,
Ayrah tana gama cin abincin ta sharuwa ta fice, bayan ta siyo abubuwan tazo ta ɗaura girkin, ka fin ta ɗibi ruwa ta shiga wanka, har lokacin da fito, ma'u tana zaune tana faman danne- danne a wayar ta, kallon ta Ayrah tayi tace " aunty ma'u dan Allah ki bani vassiline mana na shafa idan kina da shi". Ko kallo bata isheta ba, ballantana ta amsa mata, jin shiru ya saka ta miƙe tasaka wata tsohuwar doguwar rigar material, da wani koɗaɗɗen half Sunnah black abinka da farar mace sai tayi kyau abinta,
Fita tayi ta É—auki roban tallen nata ta fice daga gidan, bata dawo ba sai 5:00pm, ta siyar duka, tabawa mama abu kuÉ—in, sannan tayi shara tayi wanke-wanke ta É—aura abincin dare.....
**** Tunda suka rabu da yarinyar nan idan ya rufe idonshi ita yake kallo ya kasa goge photon yarinyar nan a idanuwansa, yauma kamar kullum yana zaune ita ɗin dai yake tunani, knocking akayi yace "shigo". Maya ta shigo tasha abaya mai kyau da tsada black, abinka da farar fata tayi kyau sosai, sai ƙamshi take yi hannun ta riƙe da babban plate wanda yake ɗauke da jug da kuma 2 cups, "good evening yah Amjad". Yace "evening a daƙile". Ta ajjiye masa plate in tace "mami tace na kawo maka". Yace "ok thank you". Ta gyara tsawuwar ta tace "kamar akwai abinda yake da munka?". Yace "nothing and you can go". Jiki babu ƙwari ta nufi ƙofa ta fita,
A main falo ta tadda mubeenah tana zaune tana chatting, zama tayi a gefen ta, dagowa mubeenah tayi ta kalle ta tace" sis lafiya?" Tace "ina kuwa lafiya mubeenah a tunani na da yah Amjad yana sona ne kamar yadda nake son shi so na aure amma yanzu na fahimci son da yake min so ne kawai na 'yan uwan taka". Mubeenah tace "why you said that?". Tace"mubeenah you know everything tun lokacin da aka fara maganar auren mu ya canza min baya da lokaci na kwata-kwata ". Ta ƙarisa maganar tana share hawayen da suka zubo mata, mubeenah ta ajjiye wayar ta tace"kiyi hakuri Maya ki dage da addu'a insha Allahu everything will be alright ".
Maya tace "Allah yasa amma wallahi har na fara tsoron rayuwar da zamuyi bayan aure". Mubeenah tace "karki damu ke dai ki dage da addu'a insha Allahu nima zan tayaki ". Tace "thank you "............
Ayra ta samu mama ta sanar mata zataje gidan su Sa'adatu, bata hanata ba dan haka ta fice ta nufi gidan su Sa'adatu bakin ta ɗauke da sallama, a tsakar gida ta samesu sun shinfiɗa taburma suna zaune itama zaman tayi tana miƙawa mama gaisuwa, mama ta amsa tace "Sa'adatu jeki ɗebo mata tuwo" Sa'adatu ta tashi ta ɗebo mata tuwo ta kawo mata taci, ta sha ruwa tana miƙawa mama godiya, mama tace "karki damu Ayrah Allah ya muku albarka" . Tace "Ameen mama". Shiru ya biyo baya sai kuma tace " mama da ma nazone akan maganar kuɗin nan dan Allah ki bawa Sa'adatu ko dubu 5 ne taje ta ɗinko mana hijabai ni da ita". Mama tace "to shikkenan badamuwa". Tace "mama dan Allah kema ki ɗauki wani abu acikin kuɗin kinji". Sa'adatu tace "gaskiya mama zata taɓa ko biyar a kuɗinki ba bestie kiyi hakuri gobe zamu koma makaranta kuma insha Allahu zanje na miki registration na Neco".
Ayrah ta kalli Sa'adatu tace "kema kin san muddin mama abu tana raye ta sha alwashin babu ni babu karatun boko ko na addini sai dai talle saboda haka kawai ki bar wannan maganar nasan bazata taɓa bari na nayi ba". Sa'adatu tace " insha Allahu zakiyi karki damu akwai yadda zamuyi"....
Sai da tayi sallar Isha ta fito ta nufi gida, tunda ga bakin ƙofa ta fahimci abban ta ya dawo, da sauri ta ƙarisa fuskar ta ɗauke da farinciki,
Amma sai dai farincikin ya tsaya saka makon sauƙar marin da taji a fuskar ta, bata ankara ba taji an ƙara sauƙe mata wani, sai da ta zauna,...............
________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*Ma'eesher*âœï¸
Feature writers association
F.U.W.A
3. ...
Ta dafe ƙuncin ta da duka hannayen ta biyu, tana jin kanta na mugun sara mata, ta ɗaga kai ta kalleshi hawaye na gangarowa daga idanun ta, tace "Abba". Yace "daga ina kike?". Tace "Abba naje gidan su Sa'adatu ne". Yace " ƙarya kike munafuka ai Abu ta sanar min kwanan ki huɗu rabonki da gida ko kin tashi dawowa ma cikin dare kike dawowa". Hawayen idanun ta ne suka ƙara gudu tace "Abba kayi hakuri". Bai ƙara cewa da ita komai ba ya juya ya nufi ɗakinsa da yake jikin ɗakin mama abu, a hankali ta miƙe tana hawaye ta nufi ɗakin su, tana zuwa kwanciya kawai tayi tanajin zazzaɓi yana sauƙa mata, ba ta daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ta, lokacin ana kiran sallar asuba Abba yazo ya ƙwanƙwasa musu ƙofa, Ma'u ce ta tashi ta buɗe kofar yace "su tashi suyi sallah". Yana faɗan haka ya juya, Ma'u ta dawo tayi kwanciyar ta taci gaba da baccin ta, duk abinda yake faruwa tanaji amma ta gagara tashi saboda zazzaɓin daya gama sauƙa mata,
Tafi minti goma a kwance kafin daga bisani ta tattara jarumtar ta, ta miƙe , ta fita ta ɗauro alwala ta dawo ta shimfiɗa kwalin ta, ta tada sallah, bayan ta idar ta ƙara kwanciya wasu hawaye masu zafi suna bin ƙuncin ta, tana tuna da idan bata da lafiya yadda ummin ta take tattalin ta, amma yanzu gata a jefe akan ta burma, tunda aka nemi ummi aka rasa mama abu ta kwashe kayan ummi duka ta siyar bata bar komai ba sai taburmar da ta barmata wani abun mamaki Abba bai taɓa tambayar ummi ba har yau,
Tana cikin wannan tunanin hawaye na bin ƙuncin ta sai rawar sanyi jikin ta yake yi, har gari ya waye 8am ma'u ta farka ta kalle ta sai rawan sanyi take yi, fuskarta ta kumbura abinka da farin fata shatin hannun Abba ya fito a fuskar ta, duk rashin imanin ma'u sai da taji jikin ta yayi sanyi, tace "sannu Ayrah ki tashi ki dawo kati fa ta, ai ƙasan da sanyi". Ko maganar bata gama ba mama ta banko ƙofar ta shigo tana masifa, wai Ayrah bata fito ta ɗaura musu ɗumame ba, ma'u ta kalleta tace" mama Ayrah fa bata da lafiya ne". Mama abu tace "to ni ina ruwana a wannan zamanin dama waye yake da lafiya ?,Ai kowa ma bashi da lafiya a wannan zamanin?". Ma'u tace " mama kawai ki ɗaura ɗumamen". Mama tace "ban ɗaura ba kuma ko zata mutu sai ta min aiki waya sani ma ko cikin shege taje tayo a yawon karuwancin nata".
Wasu zafafan hawaye ne, suka gangaro a fuskar Ayrah, ta buɗe hajabin da ta lulluɓun ta miƙe da kyar kanta na sara mata, ta fice ɗumamen kawai tayi ta dawo ta kwanta , kanta na mugun sara mata , ko minti 30 batayi ba, da kwanciya sai ga inna ta shigo da tiren goro wai ta tashi ta tafi talle, wani baƙin ciki taji ya tsaya mata a zuciyarta, yanzu kam hawayen ma yaƙi zuwa abubuwa da yawa duk akanta ita ka ɗai, ga wahalar da take sha agidan nan, ga baƙin cikin rashin ummin ta, ga jinya, ga kuma babban tashin hankalin ta yanzu Abban ta ma ya juya mata baya yana zargin ta da karuwanci,.
Haka ta miƙe jiki babu ƙwari ta karɓi tiren ta fice kowani taku ɗaya ji take kamar ana kwaɗa mata guduma akan ta saboda ciyon da yake mata, gidan su ƙawarta Sa'adatu ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, Sa'adatu bata nan ta tafi makaranta, mamace kawai a zaune tana ƙulla kayan miyan da take siyarwa, kallo ɗaya mama ta mata taji zuciyar ta, ta karye, kwanciya tayi akan taburmar da mama take, da sauri mama ta kai hannun ta kan fuskar Ayrah tace "Ayrah ai baki da lafiya kuma meya samu fuskar ki ta kumbura haka?".