← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 28

Sashe 10

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mama tace "abu har kun ƙariso kenan". Mama Abu tace" Erh" . A ɗaƙile, Mama ta tashi tace " to ni zan wuce Allah ya bashi lafiya". Su Ayrah suka amsa da "Ameen".

Mama ta fice tabar Ma'u da mama Abu da kuma su Ayrah da Sa'adatu a É—akin,
Babu wanda ya cewa É—an uwansa wani abu, suna ta zaune, Ma'u sai kallon banza takeyi wa Sa'adatu, Sa'adatu kuwa ko ajikin ta, dan bata ma san tanayi ba,

Nurse ce ta shigo ta kalli Ayrah tace "kije Dr kamal nason ganin ki".
Ayrah ta miƙe ta kama hannun Sa'adatu suka fita daga room ɗin,

Bayan sun ƙarisa Dr. Kamal ya kalle su yace " lokacin da jinyar nan ta sameshi yana iya cin abinci ne?". Ayrah tace " jiya aka dawo mana da shi a halin da yake ciki, nayi ƙoƙarin bashi kunu ma amma ya gagara sha".

Likita Yace " Gara da baki bashi ba, idan da kin bashi saka makon larurar da yake É—auke da ita, abincin zai iya bin huhun sa ya haifar da wata cutar, saboda haka zamu saka masa NG tube, saboda abinci da magun-guna".

Ayrah tace " to shikkenan likita asaka masa kawai".
Sa'adatu tace "kuma nawa ne NG tube É—in?".
Yace "15k ne ".
Sa'adatu tace" amma gashi ina tunanin mama ta tafi da kuÉ—in sai dai anjima idan ta dawo".
Dr. Kamal yace "karku damu zan je nayi making payment É—in tunda naga kamar ba wani kuÉ—ine da ku sosai ba".

Sa'adatu tace" mun gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ". Yace "Ameen ". Ayrah dai sai kallon sunan da ke kan table ɗin nasa take, tana son tuna a ina ta taɓajin kalan sunan amma ta manta, Dr. KAMAL A SARAKI, cikin sanyin murya tace " mungode".

Sai kuma ta, tashi tabi bayan Sa'adatu da ta fara fita.....

MAYA.......

Cikin ta shin hankali take driving ɗin kana kallon ta zaka san da damuwa kwance a zuciyar ta, a gidan su fadilah ta kutsa hancin motar ta, ko gama gyara parking batayi ba ta fice, ta nufi ɓangaren Hajjah da sauri, tana shiga ta sameta , falo taga Dr. Ahmad yana zaune, tace "yah Ahmad ina Hajjahn kuma ya jikin nata?". Dr. Ahmad yace " ki kwantar da hankalin ki jikin ta da sauƙi tana ciki". Da sauri Maya ta shige bedroom ɗin, ta samu Jaddah tana kwance, fadilah da Mami suna zaune a gefen ta, Maya ta ƙarisa da sallamar ta, ta zauna abakin gadon, tana kallon Mami tace " Mami ya jikin nata?". Mami tace "jiki alhamdulillah". Maya ta kalli Hajjah da tasamu bacci, ta sauƙe ajiyar zuciya tace "Ya hayyu ya ƙayyum kaga halin da Hajjahn mu take ciki Ya Allah ka bayyana mata ɗanta, Ya Allah ka kawo mata ƙarshen wannan jarrabawar da tai shekara da shekaru tana fama da ita". Dukkan su, suka amsa da "Ameen ". Suna zaune a inda take har azahar kafin suka fara tashi ɗaya bayan ɗaya suna zuwa suyi sallah su dawo, bayan sun idar suka fita zuwa dining domin cin abinci nan ma sai da Mami tayi da gaske kafin fadilah da Maya suka fita zuwa dining ɗin, suka bar Mami agun Hajjah tea kawai Dr. Ahmad ya kawo mata kamar yadda ta buƙata, suna cikin cin abincin, Dr. Kamal da shima da bai daɗe da shigowa gidan ba, ya fita sanye da riga da wando masu taushi da laushi daga alama bayan ya dawo sai da yayi wanka ya fito, yaja kujera kusa da mommy ya zauna , yace "mommy wallahi yau naga wata mai kama da mubeenah a asibiti". Mommy tace "kasan kowa yana da mai kamar sa guda bakwai". Yace " Mami suna kama sosai fah kawai dai ita hasken ta yafi na mubeenah kyau ne kuma ita yarinya ce bata kai mubeenah Shekaru ba". Mommy tace "bata da lafiya ne?". Yace " lafiyar ta ƙalau jinyar baban ta takeyi". Mommy tace "ayya Allah ya bashi lafiya". Yace "Ameen, yawwa ya jikin Hajjah?". Mami tace " da sauƙi har yanzu dai bata farka ba". Yace "Allah sarki Hajjah Allah Ubangiji dai ya bayyana mata ɗan ta nan kusa". Dukkan su suka amsa da "Ameen". Dai dai lokacin Dr. Ahmad ya fito daga ɓangaren Hajjah yana kallon Kamal yace "likita bokan turai har ka dawo kenan". Kamal yace" wallahi fah bro, ya labarin Amjad ne?". Dr. Ahmad yace" up to now he's not picking call". Kamal yace " Allah yasa dai lafiya". Ahmad yace "Ameen"..........

AYRAH.......

bayan sun idar da sallar la'asar tana zaune akan sallayar da mama takawo musu, tayi nisa cikin tunanin da take, Sa'adatu ta kalle ta, tace " ƙawata ya kamata fa kici abincin nan ko kaɗan ne, tunda cinki ko rashin cinki bashi zai bawa Abba lafiya ba". Ayrah ba tace komai ba ta ɗago ta kalle ta, Sa'adatu ta janyo food flask ɗin da mama ta kawo musu abinci aciki, ta ɗeba a plate ta miƙa mata, tace "dan Allah ki daure kici insha Allahu, Allah zai bawa Abba lafiya ". Ayrah ta amsa abincin tana kallon abincin amma ta gagara ci, Sa'adatu tace "Please ƙawata ki daure kici abincin nan mana". Ayrah ta fara cin abincin badan tana jin daɗin abincin ba kawai ta na turawa ne, kaɗan taci ta miƙawa Sa'adatu plate ɗin, Sa'adatu ta karɓa, ta miƙa pure water guda ɗaya, tasha , Ma'u ta kalli mama Abu tace " nifa nagaji gaskiya mama zan tafi gida". Mama Abu tace "ai Nima nagajin kinsan ba son zaman asibitin nakeyi ba ". Ma'u tace "to ki tashi mu tafi kawai". Mama Abu ta tashi suka tafiyar su, Ayrah ta ɗaga kanta ta kalli Abban ta da har an saka masa NG tube ɗin hawaye na bin ƙuncinta.............

___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*Mer'eesher*✍️

FEATURE WRITERS ASSOCIATION....

10..........

Sa'adatu ta kalle ta, tace "wai ƙawata Meyasa kuka baya Miki wahala ne?". Ta juya ta kalli Sa'adatu sai kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayen ta, a ranta tace " lallai Sa'adatu bata san abinda take ji ba, Sa'adatu tace "gaskiya baxan zo muna jinya kina sakani a gaba kina min kuka ba da wanne zanji?". Ayrah dai batace da ita komai ba, Sa'adatu ta miƙe tace "barinje gida na ɗebo mana kaya kafin ki gama kukan banzan naki ". Ayrah batace mata komai ba ta sunkuyar da kanta saboda wani nauyi da take ji zuciyar ta, tana mata, Sa'adatu ta kalle ta tace "bayan kaya babu abinda kike buƙata na ɗaukko Miki". A hankali tace " wayata a ɗakin Abban mu akan gado". Sa'adatu tace "to". Tare da ficewa daga room ɗin, tana fita Ayrah ta, tafka uban tagumi a ranta tana addu'ar Allah yasa ya kirata,

Sa'adatu bayan me napep ya ajjiye ta, a ƙofar gidan su, ta shiga taga mama tana ta haɗa musu kayan sakawar su a Ghana most go, ta kalli mama tace "mama ba dai yah Adam yaƙi yadda da ɗaga tafiyar nan ba". Mama tace "kwana biyu kawai yace mu ƙara". Sa'adatu tace " mama gaskiya baxan iya tafiya nabar Ayrah a halin da take ciki ba".Mama tace "zan masa magana ya barmu tukunna sai munga jikin Abban ayrahn yayi sauƙi sosai". Tace "yawwa mama Allah yasa ya yadda". Mama tace "amma fa sai dai ki rubuta jarrabawar taki a makarantar ku, dan shi saboda kije ki samu damar rubutawa ne kafin lokaci ya ƙure ya damu mu koma da wuri". Tace " shikkenan mama zan rubuta a makarantar tamu insha Allahu". Mama tace "Tom shikkenan".,

Tashi Sa'adatu tayi tace "mama barin yi wanka". Bayan tayi wanka ta fito, vassiline kawai ta shafa ta canza kayan ta zuwa doguwar rigar abayan da Ayrah ta bata, acikin wanda Amjad ya siya mata, batayi wani kwalliya ba, tayi rolling kanta da jersey vail tayi kyau abinta, tace "mama barinje gidan su Ayrah zan ɗakko mata wayar ta". Mama tace "shikkenan kiyi sauri" har zata fita sai ta dawo ta zauna tace "yawwa mama na manta ban faɗa miki ba, kinsan mama Abu da Ma'u tun ɗazu suka baro asibitin wai baza su iya zaman hospital ba". Mama tace "ikon Allah, Allah ya kyauta". Daga haka bata ƙara cewa komai ba, Sanin halin maman ya saka Sa'adatu tashi ta nufi kofar fita daga ɗakin,

Da sallamar ta, ta shiga gidan su, Ayrah mama Abu ce ta amsa mata sama-sama, ta ƙarisa ciki, ta samesu, sun baje kaza suna ci, ita da Ma'u ga goru nan, fanta a gefen su, Sa'adatu tace "Barka da hutawa mama". Mama Abu bata kulata ba, dan haka tace "zan ɗaukawa Ayrah wayar ta a ɗaki". Mama tace "gaki ga ɗaku nan ai". Miƙewa Sa'adatu tayi ta nufi ɗakin Abba tagama dubanta amma bata ga waya ba, ta dawo tana kallon Ma'u tace "Ma'u dan Allah kinga wayar Ayrah?". Ma'u tace "halan kin bani ajiya ne". Sa'adatu taja tsaki ta shiga ɗakin su Ayrah amma bata ga waya ba fa duk dubanta, ta fito ko kallon inda suke ba tayi ba, zata fice hatta kai bakin ƙofa, taji Muryar mama tana cewa" ki sanar da ƙawarki gobe dan gin baban Tanko zasu zo neman aurenta, kuma insha allahu ƙanina kawu Audi shi zai bada ita,
Chapter 10 · 0% Book details