Sashe 24
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Daddy suna zaune shi da mubeenah yaji ƙarar shigowan saƙo, dubawa yayi yaga Abbie ne ya turo masa photo ta Whatsapp, a mugun zabure Abba ya miƙe yana kallon Mubeenah bayan ya buɗe photon yace "hasashen ki ya zama gaskiya wannan photon Ibrahim ne tare da ni da kuma A saraki da autar mu". Yayi sauri yayi dailing numbern Abbie, Abbie yayi picking tare da sallama ya saka a speaker, Daddy yace photon nan na mune lokacin muna yara ni da A saraki da kuma ƙanin mu da ya ɓata wanda har yau hajjah take, jinya saboda rashin sa, ta tabbata wannan yarinyar jinin ɗan uwan mune". Sosai Ayrah ta fashe da kuka mai sauti bayan taji abinda Daddy yace...............
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
Book 1
Page 21..........
_______ sosai familyn saraki suka cika da farincikin ganin jinin ɗan uwansu, hatta Hajiya autar su Alhaji Abdullahi saraki wato Hajiya sai da aka kirata aka sanar mata, farinciki agun Hajjah kuwa ba'a cewa komai, a ranar ta fara shirin baro ƙasar da take zuwa Nigeria, washe gari gidan Alhaji Abdullahi saraki da gidan Alhaji Mustapha saraki wato mijin Mami, jirgin su yayi landing a Abuja, farinciki agidan Abbie ba'a cewa komai, sai nan suke yi da Ayrah musamman mubeenah ta yadda take janta ajiki ba'a magana, Ayrah da mubeenah suna zaune a falon Ammie suna ludo, a wayar mubeenah Dr Ahmad ya shigo , shida fadilah Ayrah ta ɗaga kai tana kallon sa, tace "ina yini". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ta kalli Mubeenah tace "shima a gidan ku, yake ko agidan Daddy saraki?". Mubeenah tace "yayana ne maman mu ɗaya amma Allah yayiwa mamar mu rasu, amma sai dai bamu san maraici ba, saboda matar daddayn mu Mami ta riƙe mu da amana sosai". Ayrah tace "ayya Allah sarki". Shi dai Dr Ahmad tun da ya zauna yake mamaki, can ya miƙe yace "ina zuwa". Daga haka ya fice, ya buɗe datan sa, ai kuwa sai ga saƙon Amjad ya shigo, yana tambayar su ko sun isa Abuja lafiya, Dr Ahmad ya ƙirasa voice call, bayan yayi picking sun gaisa, Yace " bro ya kun isa Abujan ne?". Dr Ahmad yace "mun iso lafiya wallahi alhamdulillah". Amjad yace "Masha Allah". Dr.Ahmad Yace " yanzu wani albishir zan maka amma You will pay idan albishir ɗin ya maka daɗi". Amjad yace "ok ina jinka". Ahmad yace "wannan dai cousin sistern nawa da muka zo gani, kasan wacece?". Amjad bai kawo komai a ransa ba, yace "ya za'ayi na santa? Kaji ka da wani banzar tambaya". Dr. Ahmad Yace " she's your girlfriend A'ishatul Humaira ". Amjad yace "wannan ba gaskiya bane". Dr. Ahmad yace "switch this call to vedio call zan shiga na nuna maka ita". Amjad yace "ok". Tare da yin switch ɗin call in zuwa Vedio call, Dr Ahmad ya shiga falon bakin sa ɗauke da sallama, lokacin Ayrah ta maida mubeenah gida a game ɗin da suke yi ta fara dariya tana yiwa mubeenah gwalo, dai-dai lokacin Dr Ahmad ya hasko ta, sosai zuciyar Amjad ta buga, saka makon kallon ta da yayi, Dr Ahmad ya samu guri ya zauna, yace "Yane Mallam send me, my money in my opay". Yana faɗan haka ya kashe kiran, a ɓangaren Amjad kuwa, fita yayi ya sanar da Jaddah abinda yake faruwa, Jaddah tace "Masha Allah ai dama muma gobe muke shirin tafiya ni da Nailah kawai sai mu tafi tare". Yace "Allah ya kai mu Jaddah". Yana faɗan haka ya fice, daga falon, Jaddah ta bishi da kallon tausayi a ranta tana matuƙar tausaya masa, saboda bata ga ta yadda auren sa da yarinyar da yake faɗa zai yiwu ba, bayan Maya tana rayuwar sa , abinda zata iya masa shine, ta taya sa da addu'ar Allah ya zaɓa masa wacce tafi zama alkhairi a rayuwar sa, .......
A ɓangaren Ayrah kuwa sosai taji adaɗin Kasan cewar ta da dangin mahaifin nata, duk da sometimes ta kan keɓe kanta gefe tayi kuka, tana jin ina shima mahaifin nata yana raye suga wannan ranar farincikin tare, wallahi tayi kewar mahaifin ta sosai kullum tana musu addu'a shi da ummin ta, ba dare ba rana, kwana ɗaya mutanen Kano sukayi suka tattara suka koma amma banda Hajiya autar su daddy da kuma Mubeenah, washe gari jirgin su Jaddah ya sauƙa a Nigeria, farinciki a gun Maya ba'a cewa komai, sosai tayi wannan tayi wancan, har lalle suka je aka musu ita da Ayrah, Black and red yayi kyau sosai abinka da fararen fata, Ayrah tana ɗaki tana danne-danne a wayar ta, sai yau wayar ma ta samu lokacin ta, wayar ta fara wringing da ido tabi numbern da ake kiran na ta, to ita waye me numbern ta, bayan duk 'yan familyn su tayi saving numbern su, kamar bazata yi picking ba, can dai tayi picking tare da sallama, bayan ya amsa, Yace "Madam marar gaisuwa fatan dai kun koma gida lafiya". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Yace "nasan baki gane me magana ba ko?". Tace "Erh wallahi ban gane ba". Yace " uncle Jabeer ne". Tace "ohhhh wanda muka haɗu da shi wancan ranar". Yace "Erh". Tace "ayya fatan kana lafiya". Yace " alhamdulillah". Tace "Masha Allah". Yace"dama kawai na kirane naji lafiyar ki, sai anjima". Tace"thank you". Yace "bye". Tare da kashe wayar, bayan ya kashe tabi wayar da kallo, Farhan da ke zaune akan bedside drower tana duba hand-out ɗin ta, tace "wanene wannan kuma sis?". Ayrah tace" wancan mutumin da muka haɗu dashi wancan ranar uncle Jabeer". Farhan tace "ayya Allah sarki". Mubeenah ce ta shigo bakin ta ɗauke da sallama tana kallon, Ayrah tace "sisy na kina nan ashe ina ta neman ki". Ayrah tace "wallahi kuwa aunty mubeenah". Mubeenah tace "to su Jaddah ne suka ƙariso tun ɗazu yanzu suna falon Ammie ki fito ku gaisa". Ai ko rufe baki, mubeenah ba tayi ba Farhan ta tashi ta fice da saurin ta, Ayrah ta miƙe ta ɗauki hijabin ta, ta saka suka fita tare da mubeenah, Maya da Amjad da Jaddah da kuma Ammie sai kuma Farhan da yanzu shigowar ta suna falon, suna zaune, Ayrah ta shigo bakin ta ɗauke da sallama ita da mubeenah, Jaddah ta ɗago kai tana kallon ta Ayrah ta ƙarisa ta zauna a ƙasan carpet tana miƙawa Jaddah gaisuwa, Jaddah tace"lafiya ƙalau alhamdulillah". Tana ta kallon Ayrah kamar me nazarin wani abu, Ayrah ta mai da kallon ta kan Amjad tace "uncle Amjad ina yini". Yace"lafiya Fulani". "Fulani ta maimaita abun a ranta, wasu memories suka fara dawo mata, "yaushe ƙarya zata fara shiga tsakanin mu Fulani?". Maganar da ya mata ranar da yazo Kano suka gaisa da ƙawarta Sa'adatu ya fara mata yawo, a hankali maganganu suka fara mata yawo a ƙwaƙwalwar ta..............
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
Book 1
Page 22...........
End of Book 1