← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 28

Sashe 17

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Maya bayan ya kashe wayar, ta ajjiye ta akan mirrow tanajin ƙarar shigowan massage tasan abie ne, ya tura mata kuɗin, a fili ta furta, ina ƙaunar ka sosai Abie na, the best father of the world, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, Allah ya bamu ikon maka biyayya tare da faranta maka a kowani hali muka tsinci kan mu". Mubeenah ce ta turo ƙofar ta shigo sanye da riga da scate na Atamfah ya mugun mata kyau sosai, kallon Maya ta rinƙayi kamar bazatai magana ba, sai kuma tace "dan Allah ina kayan da na baki, yanzu bazaki saka muyi ankon ba kike nufi ko me?". Maya tace "kema kin sani ba zan iya saka Atamfah ba, idan kina so muyi anko kawai kisaka Abaya". Mubeenah tace "wallahi bazan saka ba, amma ai kinsan saboda ke nayi ɗin kin nan guda biyu iri ɗaya". Maya tace"it's okay tunda bazaki saka Abaya ba". Mubeenah taja tsaki ta shigo ɗakin, ta ɗauki kayan a kan bed, ta buɗe wardrobe ta saka, ta ɗauki wayar ta, da hand bag ɗin ta, akan mirrow ta fice, sosai Maya taji babu daɗi akan abinda tayiwa Mubeenah amma ya kamata Mubeenah ta fahimce ta, ba laifin ta bane, kawai ita tafi gane tasaka Abaya bane, itama wayar ta da hand bag ɗin ta, ta ɗauka da kuma key ɗin motar ta, ta fice, ɓangaren Mami ta nufa taje har ta mata sallama bata ga, Mubeenah ba, saboda haka ta fito, ta nufi ɓangaren fadilah, knocking tayi fadilah ta buɗe mata, itama ta shirya cikin Atamfah irin na Mubeenah, tana kallon Maya tace "kuttttt Maya wai kina nufin baki saka kayan nan ba". Maya tace" kuma kun san bazan iya sakawa ba, to miye na damuwa da dole sai na saka". Mubeenah tace "Please ki daure ki saka dan Allah ". Maya tace "gaskiya bazan iya ba". Yayinda take shiga falon, Mubeenah ce ta fito, batare da ta kalli inda Maya take ba, tai wucewar ta, suka bi bayanta sai da fadeelah ta shiga tayiwa Mami sallama kafin ta fita, ta samu Maya a tsaye a compound ita kuma Mubeenah ta shige motar ta tana zaune, a driver seat, Fadeelah ta ƙarisa ta shiga front seat, kafin Maya ta shiga back seat, Maya bayan sun fara tafiya ta ciro wayar ta, a hand bag ɗin ta, ta shiga gallery ta ƙurawa photon Amjad ido, tana kallo tana jin wani sanyi a zuciyar ta, ........

*AYRAH*........

Misalin ƙarfe 2:30 na rana suna zaune a ɗakin su Liyana suna ta hira abinsu kamar sun daɗe da sanin juna, Jiddah ta shigo tana kallon Ayrah tace "Ayrah ki tashi kije kishirya kizo mu tafi unguwa". Khalil yayi sauri yace "momy Nima zan biku". Jiddah tace "bazaka kaje ba ka zauna kuyi wasa da 'yan uwanka". Liyana tace "dan Allah momy kiyi hakuri kije damu". Jiddah tace "babu inda zakuje". Ayrah tace "dan Allah aunty kiyi hakuri mu tafi da su". Jiddah tace "shikkenan ku shirya sai mu tafi". Ayrah tace "mun gode aunty". Ta kama hannun Khalil suka shiga bathroom sai da ta shirya Khalil, ta bar su Liyana su shirya ta wuce ɗakin ta, basu daɗe ba suka shirya suka, fice sosai Jiddah tayiwa Ayrah shopping hadda akwati ta siya mata, da abayoyi shower gels da turaruka da sauran su, su Liyana da leenah da Khalil ma an ɗan musu shopping ɗin, kafin suka dawo gida sosai Ayrah taita yiwa Jiddah godiya hadda kukan ta, ..........

*MAYA*...........

Tana zaune a hall ɗin sai bin Mutane take da kallo ko wacce da shigar ta irin ta su Mubeenah, masu cin snacks suna ci, masu photo sunayi, fadeelah ce ta ƙariso inda Maya take ta zauna, tace "Wai ke Meyasa bakya son zama cikin mutane ki duba curse mate ɗin mu suna ta farinciki, shekaru nawa rabon da mu haɗu, amma ke kin ware kanki, kin zo nan kin zauna". Maimakon ta bawa fadeelah amsa, sai kawai tace " dama get to gether za muzo shine, baku faɗa min ba". Fadeelah tace "naga wadda akwai maza ne, bakya son zuwa, wannan kuma na mata zallah ne". Maya ta ɗaga idanun ta, ta kalli Mubeenah sai rawa takeyi an saka musu waƙa, su da wasu curse mate ɗin su, fadeelah tace"ina zuwa " tana faɗan haka ta miƙe, ta shin ta ke da wuya Maya ma, ta tashi ta fita compound ɗin, ta zauna tana danna wayar ta, da ido take bin motar, bayan kusan minti 4 , ta tashi ta miƙe, ta buɗe front seat ta shiga, tana zaune tana ta danne-danne a wayar ta, Ya nufo motar, bai kula da mutum a motar ba, har sai da ya shiga yaji ƙamshin turaren ta, da mugun mamaki ya juyo yana kallon ta yace " ke.... From where?". Ta sunkuyar da kanta, tace "munzo get together ne, kuma wallahi I'm very tired and da mota ɗaya muka zo kuma su ba yanzu zasu tafi ba". Yace "ki hau taxi mana". Tace "Please yah Ammar I'm begging you ka kaini gida dan Allah". Ya kalle ta sai kuma Yace "ina da gurin zuwa". Tace "dan Allah ". Bai ƙara ce mata komai ba yaja motar ya fice.........

*AYRAH*

A iya yinin yau da tayi baƙara min jindaɗin zama da ita Jiddah tayi, taja yaran ta ajiki, kuma ita take duk wasu aikace-aikacen cikin gidan, tana kwance cikin dare, taji an janye duvet ɗin da ta lulluɓu da shi, sosai zuciyar ta, ta tsinke, ta tashi , jikin ta yana rawa, ta nufi gurin kunna haske, taji an ruƙo hannun ta, cikin firgita da tashin hankali, ta janye hannun ta, ta kunna hasken ɗakin, da mugun mamaki take, kallon sa , hawaye na bin ƙuncinta tace"uncle me yakawo ka ɗakina me kake buƙata da ni?". Yace"Ayrah haɗin kanki nake buƙata Ayrah dan Allah ki taimaka ki amince da ni, na miki alƙawarin zan Miki duk abinda kike buƙata a duniyar nan idan dai kuɗi zai iyayin sa". Ayrah har yanzu hawaye bai daina zirya a idonta ba, tana kallon sa da mugun mamaki da kuma tashin hankali............

___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________

FEATURE WRITERS ASSOCIATION....

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*MER'EESHER ✍️*

Book 1

Page 16......

***** "A'uzubillahi minash, shaɗanirrajim, dan Allah kayi hakuri uncle, ka fita min a ɗaki". Ta faɗa idon ta na zubda hawaye, ga nin yana ƙoƙarin yowa kanta, ya saka ta bige shi, ta fice da gudu, ɗakin su Liyana ta shiga ta rufe jikin ta yana ta rawa, bayan ta rufe ƙofar ta jingina da ƙofar, ta fashe da kuka, tuna su Liyana suna ɗakin kuma ya saka ta rufe bakin ta tana kuka, sosai ta zame ta zauna a gurin zuciyar ta na mata wani irin zafi a ranta tana fatan Allah ya fitar da ita daga cikin wannan mummunar ƙaddarar da take bibiyar ta, agurin bacci ɓarawo ya ɗauke ta, sai guraren sallar asuba, ta tashi, ta koma ɗakin jikin ta na rawa har lokacin bata fita daga cikin ta shin hankali da take ba, ko da ta shiga sai da ta, tabbatar baya ɗakin kafin ta rufe ɗakin ta ciki, tana shiga bathroom ta wuce ta ɗauro alwala, ta fara sallolin nafila tana roƙon Allah ya bata ikon cinye wannan jarrabawar ɗari bisa ɗari, Allah ya kawo mata mafita da ɗauki, bata tashi akan sallayar ba har sai da ta gabatar da sallar asuba, bayan ta idar ta fara karanto azkhar ɗin ta, bayan ta gama ta shiga bathroom tayi wanka, ta fito ɗaya daga cikin doguwar rigar da Jiddah ta siyo mata, ta saka, bayan ta gama shafe-shafe, da har zata fesa turare ta fasa, ta ɗakko dogon hijab ɗin ta blue ta saka, ta fice ta nufi kitchen jikin ta a sanyaye, saboda har yanzu memoring abinda ya faru jiya yana mata yawo a ƙwaƙwalwar ta,....

*MAYA*
Chapter 17 · 0% Book details