← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 28

Sashe 1

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read



🥀 *BAYAN DUHU*🥀

🌑 GABATARWA 🌑

Bismillāhir-Raḥmānir-Raḥīm

Godiya ta tabbata ga Allah (Subḥānahu Wa Ta'ālā), Ubangijin talikai, Mai rahama kuma Mai jin ƙai, Wanda Ya ba ni ikon fara wannan littafi tare da kammala shi cikin ikonsa da yardarsa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (Ṣallallāhu Alaihi Wasallam), da iyalansa, sahabbansa da duk waɗanda suka bi tafarkinsa har zuwa ranar sakamako.

Masoya karatu, ina yi muku barka da zuwa cikin wannan sabon labari mai suna BAYAN DUHU. Labari ne da ya ƙunshi darussa masu amfani, ƙalubalen rayuwa, haƙuri, soyayya, cin amana, juriya da kuma fata. A cikinsa za ku fahimci cewa duk tsananin duhun da rayuwa ta kawo, akwai ranar da haske zai bayyana da izinin Allah.

Ina roƙonku da ku karanta wannan littafi da zuciya ɗaya, sannan idan kun ga wani kuskure na nahawu ko rubutu, ku gyara ni cikin ladabi, domin babu mai kamala sai Allah Maɗaukakin Sarki.

A ƙarshe, ina godiya ga dukkan masoyana da masu karanta rubuce-rubucena bisa irin ƙauna, addu'a da goyon bayan da kuke ba ni. Allah Ya saka muku da alheri, Ya sanya wannan littafi ya zama sanadin alkhairi gare mu baki ɗaya.

Barkanmu da sake haÉ—uwa a cikin...

Book1️⃣

Page 0️⃣1️⃣

___________🥀BAYAN DUHU🥀______________

*A'isha Muhammad Kabir*

_Ma'eesher_✍️

Gida ne na masu matsaikacin ƙarfi wata kyakkyawar budurwa a tsakar gidan tana wanki, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci yarinyar ta haɗa jini da larabawa saboda irin kyau da hasken fatarta,

Wata mata ce ta fito daga É—aki, kallon ta tayi cikin masifa tace " wai ke Ayrah wace irin jakar yarinyar ce kwata-kwata bakya aiki da sauri tun É—azu baki gama wankin nan ba bayan kin san É—iban ruwa yana jiran ki". Ayrah tace "kiyi hakuri mama abu na kusa gamawa". Matar tace "Hai dallah wawiyar banza jaka minti 10 na baki kigama wankin nan ki fita ki É—ebo mana ruwa idan ba haka ba jikinki ya gaya miki".

Tana kaiwa nan matar ta juya abinta ta koma ɗakin ta tana ƙwafa, hawayen da Ayrah taƙe riƙewa ne suka fara fitowa, hannun ta tasaka ta share a ranta tanajin kewar ummin ta , saboda tasan halin mama abu, cikin minti goma sha biyar 15 ta gama wankin ta shanya,

Sannan ta nufi kitchen ta ɗauko bocket ta fice daga gidan tanajin cikin ta na mata kukan yunwa dan rabon ta da abinci tun jiya da dare da taje gidan su ƙawarta Sa'adatu ta bata tuwo taci, har yanzu da yake ƙarfe 12:20 bataci komai ba,

Tana fita ta nufi fanfon tuƙa-tuƙa wanda yake da ɗan nisa da gidan su, tana isa bakin fanfon zuciyarta tai mugun bugawa saboda wanda ta gano a bakin fanfon, jiki a sanyeye ta ƙarisa,

Tun kafin ta ƙarisa yaron sa ya kallesa yace "hattara dai oga gacan cilar ka tana zuwa". Bakin ta ɗauke da sallama ta ƙarisa bakin fanfon, wanda yayi magana ɗazu ya kalleta yace "Sa'a dai amaryar ogan mu".

Ɓata fuska tayi kamar zatai kuka sai kuma ta basar tasaka bocket in ta alayi ,
Ai kamar jira yake yi ya kalli yaron nasa yace "Dauda". Dauda yace "Sa'a dai oga Tanko". Tanko yace "matata bai kamata tabi layi ba a cire botikin uban kowa asaka mata nata". Ai kuwa haka Dauda ya saka mata botikin ta ya cika sannan ya cire mata,.

Yana ƙoƙarin ɗauka tace " barshi zan ɗauki abuna".bai mata musu ba ya bar mata, ta ɗauka ta nufi hanyar gida babu abinda cikin ta yake mata banda ƙugin yunwa". Bakin ta ɗauke da sallama ta shiga gidan nasu, wata budurwa ce wacce bazata wuce shekarun Ayrahn ba, kallon tayi rai ɓace tace "to soloɓiyo sai yanzu kika ga damar kawo mana ruwan tun ɗazu inaso nayi wanka kin shanya mutane sai jiranki suke".

Ayrah ta kalle ta tace "kiyi hakuri ma'u". Tsaki ma'u taja tace "dalla can mayya ki wuce ki kaimin wannan botikin bayi zanyi wanka sai ki ɗauki ɗayan botikin". Ayrah tace "ma'u mama abu fa ta hana wanka da botikin nan". Ma'u ta ƙule tace " shegiya ni kike faɗawa mama ta hana ke dai da kike jaka ke aka hana, ta ɗaura da cewa zakije ki kaimin ko sai na canza miki kamanni?". Ayrah batace da ita komai ba ta wuce ta kai mata ruwan bayi,

Tana fitowa ko kallon inda ma'u take batayi ba ta É—au ki wani bocket in ta fice daga gidan,

Batayi wata doguwar tafiya ba, tazo dai-dai ƙofar wani gida taji ana neman almajiri, ƙarisawa inda yarinyar take, tace "dan Allah idan abinci zaki bashi ki bani zanci wallahi yunwa nakeji". Yarinyar ta tsaya tana kallon ta da kwanon abincin a hannun ta , hawaye na bin ƙuncinta tace "mallama Ayrah!".

Mamaki ya cika Ayrah amma ta ɓoye tace "ki bani abinci naci". Yarinyar tace ki shigo ciki". Ta faɗi hakan yayinda take kama hannun Ayrah suka shiga ciki,

Wata mata ce a zaune a tsakar gidan tana gyara shinkafa kallon su tayi, tace "Maryam wannan ba Ayrah ba?". Maryam tace "itace wallahi aunty itace malamar mu a islamiyya da". Ta faɗa yayinda take miƙawa Ayrah abincin hannun ta, ta ɗebo mata ruwa ta bata,

Abinka da mejin yunwa haka ta zauna tana ta cin abincin hannu baka hannu ƙwarya, bayan ta gama ci tasha ruwa, ta Musu godiya ta fice dan bata so ta daɗe,

Bata gama É—iban ruwan nan ba sai kusan 1:30 ta ajjiye botikin, ta É—auki buta tayi alwala ta shiga É—akin su, ma'u ta samu tana kwance tana waya ko kallon inda Ayrah take batayi ba, har Ayrah ta shimfiÉ—a kwalin ta, ta gabatar da sallar ta,

Ta daɗe tana addu'a tana kaiwa Allah kukan ta, tare da fatan duk inda mahaifiyyarta take ta kasance cikin ƙoshin lafiya,

Tana idarwa ta jiyo muryar mama abu tana ƙwala mata ƙira,
Da sauri ta fita ta nufi inda sautin kiran mama abu yake fitowa,

Tana fitowa ta samu mama abu tsaye da tiren goro a hannun ta, tace "uban me kike tun ɗazu kinaji ina ƙiranki?". Tace "kiyi hakuri mama". Mama abu tace "to gashi maza ki tafi talle kuma karki dawo min gidan nan sai kin tabbatar da kin siyar da goron nan idan ba haka ba jikin ki ya faɗa miki".

Ayrah ta karɓi goron hannun mama abu ta nufi ƙofar fita daga gidan,.

Wunin ranar haka Ayrah taita zage gari amma batayi ko biyar ba, har 6pm bata koma gida ba saboda tana tsoron abinda zataje ta tarar,

Tana tsaye a bakin titi daga ƙarshe ta yanke shawarar komawa gida, tsallaka kwalta ta take yi amma zuciyar ta cike da tunani kala-kala kamar da ga sama wata lafiyayyar mota ta bigeta, ta faɗi ƙasa sumammiya,

Da sauri drivern ya fito, cikin tashin hankali shima wanda ake driving É—in ya fito , kyakkyawane fari tas tabar kallah masha Allah, hasken sa irin na larabawa,

Da sauri ya ƙariso kanta kallo ɗaya ya mata yaji zuciyarsa ta masa wani irin bugun da bai taɓa jin irin sa ba sai yau,

Drivern yace" ranka ya daÉ—e bari na É—akko ta muje asibiti".

Kallon drivern yayi yace "zan ɗakko ta". yana faɗan haka yasaka hannu ya ɗauki Ayrah sai cikin mota, a back seat ya ajjiye ta shi kuma ya koma front seat, tare da umartar drivern akan ya ƙara gudu,

Yanayi yana juyawa yana kallon fuskanta har suka ƙarisa hospital in, da wuri aka karɓeta aka shiga da ita,

Ba'a daÉ—e da shiga da ita ba wayar sa ta fara wringing, picking yayi tare da sallama,

Bayan an amsa masa sallamar, daga ɗaya bangaren yace "bro kana inane har yanzu baka ƙariso ba hankalin mu duk yabi ya tashi bayan ka sanar da mu 5 zaka ƙariso".

Yace "karka faÉ—a a mami amma mun bige wata yarinya ne yanzu haka muna asibiti ".

Yace"subhnallahi yanzu kuna wani asibitin?".
Yace" muna asibitin ku".
"Ok" kawai yace tare da kashe wayar,

Basu daÉ—e da magana ba, sai gashi ya shigo asibitin, da saurin sa,

Yayi kan su yana tambayar su "ya jikin yarinyar?".
Yace" basu fito da ita ba tukunna dai tana ciki".

Yace "bro ka taso muje office É—ina ka jira acan nima zan shiga na duba yanayin jikin yarinyar".

Ya faÉ—a yayinda yayi gaba shi kuma ya bishi abaya har izuwa office in, inda aka rubuta Dr. Ahmad M Saraki,.

Zama yayi akan kujera zuciyar sa cike da tunane-tunane , shi kuma Dr. Ahmad ya É—auki abinda zai É—auka ya fice,

Baifi minti 5 da fita ba sai gashi ya dawo ya kalle shi yace "alhamdulillah bro insha Allahu soon zata samu lafiya zaka iya zuwa ka ganta".

Batare da yace komai ba ya fita ya nufi É—akin da aka ajjiye ta, yana shiga ya samu tana bacci hannun ta É—auke da da drip,

Fuskarta ya tsaya yana ta kallo yana jin zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri,
Turo ƙofar akayi aka shigo Dr. Ahmad ne da wata nurse, juyawa yayi yana kallon su, Dr. Ahmad yace "kazo mu tafi gida ga nurse zata kula da ita".

Yace" no".
Dr. Ahmad yace "Please kazo mu tafi za ta kai gobe 9am kafin ta farfaÉ—o kuma idan bakazo gida ba me zance a mami bayan kace kar na sanar da ita".

Kallon ta yayi sai kuma ya juya ya nufi ƙofar fita, basu yi tafiya mai nisa sosai ba, suka shiga wani tamfatsetsen gida mai kyau, suna shiga sukayi parking, suka fito shida Dr Ahmad suka shiga ciki bakin sa ɗauke da sallama,

Wata kyakkyawar budurwa dake ta faman kaiwa da komowa ta juyo fuskanta ɗauke da farincikin da ya kasa ɓoyuwa a zuciyarta, ta miƙa musu gaisuwa dukkan su suka amsa,

Tace" sannu da zuwa yah Amjad".
Yace "yawwa". Ba yabo ba fallasa,
Ana cikin haka sai ga mami ta fito da sauri ya ƙarisa yayi hugging in ta,
Itama cikin farin ciki ta riƙeshi tace "welcome my son".
Chapter 1 · 0% Book details