← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 29

Sashe 7

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sanye take cikin wasu English wears white colour masu ɗan kama jiki sai kuma ta ɗora rap Abaya black colour akai tayi rolling fuskarta da veil ɗin rigar Masha Allah tayi kyau sosai abinta hannunta riƙe da mug na tea mai zafi tana sha, takun da taji abayanta yasa ta juya murmushi ta sakar masa saida ya sake kallonta dan ba ƙaramin kyau tayi masa ba tabbas badan bashida halin aurenta ba da ya mayar da ita mallakinsa yana matuƙar son kyakkyawar mace gashi kuma Ma'eesha Allah ya hore mata ga kuma kuɗi wanda shine yasa kyan nata ya sake fitowa fili cikin sanyin murya ta ce"yayana I'm gonna to miss you wlh" murmushi ya yi yana bata peck a goshi ya ce"same dear, da ace banida wasu ayyukan ai ni ne zan rakaki" turo baki ta yi tana langwaɓewa ta ce"toh yaya dan dai three days please mu tafi tare" cikin son kwantar mata da hankali ya ce"shalelen Father kenan, ai three days dayawa a wajena karki damu idan zaki Masarauta nida kaina zan rakaki" murmushi ta yi ta ce"yaya da gaske kake?" gyaɗa mata kai ya yi yana kwaikwayon muryarta ya ce"Eh da gaske nake babyn yaya" tuntsirewa ta yi da dariya ta ce"kai ko yaya hmmmm!" waro idanunsa ya yi ya ce"ni ko me?" girgiza kanta tayi tana rufe baki daidai nan suka ƙaraso parlon, General ne sanye cikin wasu kayan sojoji t-shirt da trouser sai jacket ya ɗora a sama sai Mami tana sanye cikin wani ubansu less blue colour mai ƙananun zane ɗinkin riga da zani ta ɗora mayafi pink akai idan ka kalli Mami ba zaka taɓa cewa ta haifi Ma'eesha ba tun daga yanayin fuskarta har zuwa jikinta Allah ya yi mata zubin halitta mai kyau hakama kuma ƴar tata, murmushi General ya yi idanunsa kan matar tasa sosai ta burgeshi dan yana matuƙar son ado da kwalliya shiyasa koda yaushe yake jin Mami kamar amarya a wajensa ko auren Mommy da ya yi saboda mahaifiyarsa ta matsa masa ne sai gashi itama ɗin bata samu haihuwar ba, fitowa Mommy ta yi cikin wata abaya ash colour tayi rolling veil kana kallon fuskarta zaka san ta fara manyanta dan Mami ta fita kyan jiki

"Father mu tafi ana jirana please"

Maganar Ma'eesha ce tadawo dashi daga tunanin daya tayi ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce"wato dai na fuskanci kin fison tafiyar nan ko?, mune kaɗai muke jin zamuyi kewarki ai Shikenan" ɓoye fuskarta tayi a jikinsa tana dariya ta ce"A'a Father nima wlh ina ji ai ba daɗewa zan yi ba"

"Kina da tabbacin ba zaki daÉ—e ba?"

Da sauri General ya kalli Mommy sai kuma ya ce"kamarya naga only three days zasu yi" duru-duru ta fara yi dan batasan sanda maganar ta suɓuce mata ba sai kuma ta ce kamar me koyan magana"uhmm...in daman nufina bata saniba ko a ƙara musu kwanaki" taɓe baki ya yi bai ce mata komai ba ya kama hannun Ma'eesha suka yi waje hakan yasa duk suka bi bayansu. Saida suka ga jirginsu ya tashi sannan suka koma gida sosai Ma'eesha ta yi kuka dan daman duk sanda zatayi wata tafiya sai tayi kuka kamar bazata dawo ba, wani killer smile Farooq ya yi sanda yaga jirgin nasu ya fara yawo a sararin samaniya cikin wata murya mai nuna zallar farin ciki ya ce"good bye lovely sister, I'm gonna to miss you shalelen Father" murmushi Mommy da take gefensa tayi dan taji abinda ya ce cikin ƙasa da murya ta ce"ka tabbata baza'a samu matsala ba?" kallonta ya yi sai kuma ya kama hannunta ya matse cikin nasa alamar Eh sannan ya saketa ya yi gaba, ajiyar zuciya Mommy ta sauke tana murmushi ko babu komai sun kusa samun abinda suka daɗe suna muradi.

*YOBE STATE*

*GASHUA MARKET*.

Tsugune take ƙofar wani shagon mai saida abinci tana wanke-wanke jikinta sai rawa yake kasancewar garin damuna kuma jiya da daddare anyi ruwa sosai batada wani zaɓi daya shige tayi aikatau dan samun abinda zata sanya a bakinta dan kwata-kwata bata iya jure yunwa ba fitowa matar ta yi tana kallonta ganin har kusa gamawa ta ce"yawwa yarinya kiyi sauri ki gama kizo ki ci abinci nasan kina jin yunwa" gyaɗa mata kai kawai Muhaira tayi dan magana ma wahala take mata koda yaushe cikin tunanin mafita take tabbas bazata cigaba da rayuwa cikin kasuwa ba dolene ta fita daga ciki tsawan waɗannan kwanakin batada aiki sai tunane-tunane duk ta hargitsa kwakwalwarta ko ya zatayi?????.

*MA'EESHA POV*

Tana fitowa daga wankan sannan ta sanya doguwar riga pink colour sannan ta gyara gashinta wayarta ta ɗauka sannan ta zauna dan kiransu Father, Da sauri ta faɗo jikinta tana dariya tsaki Ma'eesha tayi sannan ta tureta ta ce"wai dan Allah Suhaila yaushe zaki yi hankali jifa yanda kika wani faɗo min a jiki salon ki karyani" miƙewa zauna tayi tana kallonta ta ce"ke banza ce wlh kinsan me??"girgiza kai Ma'eesha ta yi Suhaila ta ce" gobe zamu koma gida right?" gyaɗa mata kai Ma'eesha ta yi sannan ta cigaba da faɗin" to kafin mu tafi zamu shiga kasuwa haka sir ya ce kinga zamuga gari sosai daman duk an riƙemu" ihu Ma'eesha ta saki tana rungumeta ta ce"wayyoo Allahna daɗi kasheni, zan yi wa su yaya Farooq tsaraba kenan, daman wlh tun jiya nakeson mu fita, kai Allah ya yiwa Sir Ahmad albarka naji daɗi sosai wlh" tashi Suhaila ta yi ta ce"lemme take shower then muci abinci" girgiza kai ta yi ta ce"banza Acici kawai" gwalo ta yi tana shigewa toilet ɗin ta ce"naji ɗin".

*MONDAY*
*4:00pm*

*GASHUA MARKET*.

Wani irin farin ciki ne ya mamaye Ma'eesha da ƙawayenta both maza da matan tana sanye cikin wata Abaya purple colour sosai suke murna saboda ganin kasuwar gashua ɗin tunda take a rayuwarta bata taɓa shiga kasuwa ba saidai supermarket dan kome zasu siya anan suke siya hakama sauran ƙawayen nata kasancewarsu ƴaƴan masu faɗa aji, banda dariya babu abinda suke yayinda wasu suka shiga tiktok sunata ɗaukan vedio wasu kuma na hoto ko'ina kallonsu ake domin sun burge kowa duk abinda sukaga ana siyarwa wanda basu san shi ba sai sun tsaya sun tambaya sannan sunyi hoto da mai siyarda abun, murmushi ta yi tana kallon matar ta ce"Nagode Adda Allah ya ƙara arziƙi" rungume Muhaira ta yi ta ce"karki damu yarinya kinyi kyau sosai, yanzu jeki ki yo mana cefane" da sauri ta karbi kuɗin sannan ta fita duk murna ta isheta barinma idan ta ƙara kallon Abayar dake jikinta dukda ƴar ɗinki ce amma zata iya cewa bata taɓa saka kaya mai tsadar wannan ba gashi kuma kalar purple ɗin ta karɓi farar fatarta duk inda tabi sai kallonta ake tayi wani irin kyau Masha Allah. Murmushi ta yi bayan ta ɗaga kiran tana kallonsa ta ce"yaya ka ganmu nan a kasuwar gashua zan tawo maka da tsaraba" murmushi ya yi ya ce"Allah ƙanwanta ki ce zan ci abun daɗi" gyada masa kai ta yi sannan ya ce"okay shalele I'll call you later" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta katse kiran suka cigaba da kallonsu.

*FAROOQ POV*

A hankali yake sintiri a bedroom É—in nasa kwata-kwata hankalinsa ya gaza kwanciya so yake kawai su kirashi su faÉ—a masa magana mai daÉ—i, ringing É—in daya ji yasa ya yi saurin kallon screen É—in wayar wani killer smile ya yi sannan ya É—aga wayar

"She's wearing Abaya purple colour"

Sauke wayar ya yi yana sakin wani numfashi.

*POV*.

Kallon mutumin daya tsaya gefenta ta yi, sanye yake cikin wasu English wears ɓaƙaƙe ya rufe fuskarsa da face mask, kallonta ya yi sai kuma ya kalli wayarsa sannan ya ce" two pack of tomato" okay ya ce sannan ya juya dan ɗebo tumatur ɗin, matsowa ya yi kusada ita bata yi auneba taji ya ɗora mata wani hankaci a hanci nan take tayi baya zata waɗi da sauri ya riƙeta cikin hanzari kuma ya sanyata bayan motar ƙirar Honda Accord sannan ya shiga gidan gaba da wani irin speed drivern yaja motar suka bar filin kasuwar. Saida suka yi nisa sosai da kasuwar sannan ya ce"stop the car!" a hankali drivern ya yi parking juyawa ya yi ya ɗagota ya kalli fuskarta sannan ya kalli pic ɗin da ke kan wayar tasa daidai nan kira ya shigo ɗagawa ya yi daga ɗaya ɓangaren ya ce"what is going?"

"I got her"

Ajiyar zuciya Farooq ya sauke sannan ya ce "lemme see her" juyoda fuskarta ya yi, bai san sanda wani murmushi ya ƙwace masa ba ya ce"good job!," kashe wayar ya yi sannan ya koma inda yake ya zauna ya kalli drivern ya ce"Airport".

*MAI ZAMANI POV*
Chapter 7 · 0% Book details