← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 29

Sashe 5

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanayin lokacin sanyi ne sbd haka kowa yana cikin É—aki shida Æ´aÆ´ansa, zaune take kan wata tsohuwar kujerar katako gabanta wani tulin wanke-wanke ne, yinsa take yayinda duk jikinta yake kakkarwa sanyin numfashi yana kai kawo wanke kayan take amma tuni hankalinta yabar wajen, dubban tunanunnuka ne ke yawo cikin kwanyar kanta, bakinsa É—auke da sallama ya shigo cikin gidan cikin rawar murya ta ce

"Sann..sannu da shigowa Baba"

Sai a sannan nasamu sukunin ganin fuskarta tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta wanda ya halicci wannan kyakkyawar budurwar tsayawa fasalta kyawu irin na Muhaira ɓata lokacine dan indai magana kake ta kyau to dazarar kayi ido biyu da ita magana ta ƙare tamkar ba mutum ba haka take da kyau saima ka saka idanunka cikin nata nan zaka gane Ubangiji ya yi baiwa. Kallo ya bita irin kallon tausayin nan duk ƴaƴan gidan sai ita kaɗai za'a saka aiki haka ma kuma cikin wannan sanyin ga yanayi na lalurarta, jiki a sanyaye ya ƙarasa gabanta cikin sanyin murya ya ce"Aishatu tashi kinji" batasan mene yiwa babba musu ba domin bata taɓa yi ba ta taso ne inda ko tanason abu ko bata so dole sai ta aikatashi, sosai ransa ya ɓaci hakan yasa ya fara kiran matan nasa

"Falmata!! Falmata!! Ya'acca!! Ya'acca!!"

Da sauri suka fito suna kallonsa da alama ma bacci suke ya ce"wai yaushe zaku fara imantawa wannan yarinyar ne?, me tayi muku haka da zafi?, kodan maraicinta ya kamata ace kuna tausaya mata sannan kuma ga yanayi na lalurarta wannan rashin imani ne kuke gwada mata kuma baku tunanin wata rana ayiwa naku haka" rai ɓace Falmata ta ce"haba mai gida idan bamu sata aiki ba kallonta zamu yi?, gaskiya ka wani daina nuna ka fifita yarinyar nan akan ƴaƴanka wannan ba daidai bane" baki buɗe yake kallonta sai kuma ya yi kwafa ya ce"A'isha tashi daga nan" dakyar ta iya yinƙurawa ta miƙe daga wajen jirin yana shirin ɗibanta da sauri Bani kura ya kamata ya ce"sannu kinji" tsaki Ya'acca tayi dan ita daman tun yarinyar na ƙarama ta tsaneta ashe zasu zauna tare da ita ga yarinya ce kyau kamar wata aljana. Bani kura bai sake bi ta kansu ba ya shige da ita ɗakin da take kwana.

Ɗan ƙaramin ɗaki ne babu komai cikinsa sai wata tsohuwar tabarma da wani bargon mai kamada tsumma sai kuma Ghana most go ɗin da kayanta ke ciki, zaunar da ita ya yi sannan ya ce"sannu bari na samo miki ko kunu ne sai kisha muje asibiti" gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ya juya ya fita, jingina tayi da garun ɗakin wasu irin zafafan hawaye suka shiga sakko mata ita ɗaya tasan irin zallar azabar da take ciki ga kuma yunwa da take ji dan rabonta da abinci tun jiya da rana tuwon daren da suka girka basu bata ba saboda Bani kura ya yi musu faɗa akanta haka ta kwana da yunwa yanzu kuma tana tashi da safe aka sanyata gyaran gidan gaba ɗaya. Kusan 10mins sannan ya shigo hannunsa riƙe da wani kofi sai leda zama ya yi gabanta ya miƙa mata kofin karɓa ta yi sannan ya buɗe mata ledar, ƙosai ne aciki da alama siyo mata shi ya yi, dakyar takai bakinta kan kofin kunun ta fara sha ko sugar babu ciki amma haka take sha daman inda sabo ta saba saida ta gama ci sannan ya ce ta shirya shima kuma ya fita dan shiryawar.

Numfasawa likitan ta yi tana sake ƙare mata kallo sai kuma ta kalleshi ta ce"Baba yarinyar nan tanada buƙatar kulawa ta musamman dan a halin da ake cikin ciwon zuciyarta yana gab da shiga matakin ƙarshe gefe guda kuma Asthma bata samun kulawar taga dace da mai irin ciwonta yanada kyau ace an kula da rayuwarta yanda ya kamata idan ba haka ba nan gaba kaɗan labarin zai canza" sosai hankalinsa ya tashi cikin rawar murya ya ce"yanzu likita me zamuyi?, yarinyar nan marainiyace nikuma banida ƙarfi bansan ya zanyi da ita ba" kallonta doctorn ta yi ganin yanda ta matse jikinta guri ɗaya ga yarinya har yarinya amma babu kyakkyawar rayuwa Allah mai iko aranta tayi maganar sai kuma a fili ta ce"Allah ya rufa asiri yanzu zan rubuta mata magunguna ka tabbata ka siya mata dan tanada buƙatarsu" gyaɗa kansa ya yi yana kallon Muhaira shima.

"Ke Muhaira!! Muhaira!!"

Dakyar take buɗe idanunta wanda suka sauya kala wani irin ruwa kwance akansu, tsaki kulu ta yi sannan ta ce"kizo inji Umma" kallonta Muhaira ta sakeyi sai kuma ta fashe da kuka tana cewa"Papii! Papinaaa!!, wajen Papi zani banson nan gidan A'aaaaaa!!" da sauri Kulu tayi waje daidai lokacin da Bani kura ya shigo gidan hannunsa riƙe da magungunan Muhaira tana ganin ta ce"Baba Muhaira! Muhaira jikinta ya tashi" da sauri yabi bayanta suka koma ɗakin lokacin suma matan gidan suka fito. Kwance ya sameta tana birgima tana kiran iyayen nata harma da wasu sunaye da sauri ya ƙarasa gabanta hankali tashe ya ce"Aishatu ya isa haka za'a kirasu kinji ki daina dan Allah" ko saurarensa bata yiba ta cigaba da kukanta tana zallewa, rungumeta ya yi ajikinsa yana tofa mata duk addu'ar da tazo bakinsa duk mutanen gidan sunyi tsuru tsuru suna kallonta dan daman idan ciwon ya tashi haka ta keyi, sosai Bani yasha baƙar wahala kafin ya samu aljanun subar kanta wani nannauyan bacci ya ɗauketa.

"Gaskiya mai gida a nemi mafita ya zamu dinga zama da mai lalurar aljanu acikin gida yarinya sai ciwoka kala kala gaskiya bazata saɓu ba" caraf Falmata ta karɓe tana faɗin"kema dai kin faɗa wlh wannan bazai taba yiwuwa ba haka kawai watarana ta shafawa ƴaƴanmu jaraba"

Ko kallonsu Bani kura bai yiba ya girgiza kansa ya yi waje, suma suka fito suna maida zance.

*ABUJA*.

*MALAM DUDU POV*

A matuƙar fusace Farooq ya miƙe tsaye yana yiwa malamin wani irin shegen kallo ya ce"bangane mai kake nufi ba?, Kai malam fito kayi mani bayani yadda zamu fahimta ka tsaya kana yiwa mutane wani zancen banza!" kallonsu Malamin ya yi sai kuma ya fashe da dariya lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai ya ce"kai yaro ni ba abokin wasanka bane na baku aiki kuma baku yisa yanda ya kamata ba sannan kuma baku taɓa bibiyar maganar ba shiyasa nima nayi muku shiru kuma a halin yanzu banida wani abu da zanyi akai kamar yanda na faɗa muku wannan yarinyar *BA ITA BA CE!"*

# *BA ITA BA CE!*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *Affection*
# *SQUAD 2024*

# *Nanameera ce!.*
[8/2, 9:17 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

*@Nanameera08* _wattpad_

*nanameera08* _arewabooks_.

*Nanameera ce!*

*Daga marubuciyar*
*NAANAH*
*TSAKANINMU*
*SHEIKH HEESHAM*
*FATTOMAH*
*nd now*
*BA ITA BA CE!*

# *SQUAD 2024*

```Page 04```

Kallonsa Mommy take da tsananin tashin hankali kwata-kwata ta kasa fahimtar abinda yake faɗa kwakwalwarta ta tsaya cak!, Miƙewa tayi dan fita daga gidan saidai kafin takai kofar zauren tayi baya luuu zata waɗi da sauri Farooq ya tare ta hankali tashe kuma yake furta "Mommy!! Mommy!! Mommy" tuni jikinta ya saki hakan yasa kawai ya yi waje da ita, kallonta ya yi hannunsa riƙe da goran ruwan sai sauke numfashi take a hankali shi kansa dauriya kawai yake amma tabbas abun ya tabashi sosai, riƙo hannunsa Mommy ta yi murya bata fita sosai ta ce"Farooq ka fahimci abinda malamin nan ke faɗa kuwa? ni ban fahimta sosai ba, nufi yake duk abinda mukayi ya tashi a banza kenan?, muna tareda silar rugujewar burikanmu, nashiga ukuna Farooq idan General ya fahimta wlh mun kaɗe har ganyenmu ni wlh..."

"Mommy dan Allah ya isa haka kina neman fasamin kai kema, please abar wannan maganar muje gida doctor ya dubaki maybe ma jininki ya hau baki sani ba, zamu yi maganar ko zuwa gobe ne"

Batada wani zaɓin hakan yasa dole tayi shiru badan tagama faɗar abinda ke ranta ba sanin kuma halin Farooq na fusata yasa tayi shirun, fita ya yi ya koma front sit ɗin ya tayar ya motar, tafiya kawai sukai yana furzar da wani irin numfashi sai wuci yake haka har suka ƙarasa gida.

*MAI ZAMANI POV*

Kamar bazai magana sai kuma ya ce"meya sameta?" kansa ƙasa ya ce"wlh Father wai jininta ne ya hau" miƙewa General ya yi ya ce"okay Allah ya bata lpy zuwa anjima kazo zamuyi magana akan tafiyarka Paris" ya juya ya fita. Bin bayansa Mami tayi har bedroom ɗinsa, zaune ta taddashi yana waya hakan yasa ta zauna kan bedside drawer tana kallonsa saidai ya kammala sannan ya juyo yana kallonta yana murmushi ya ce"Madam ya dai?" shiru tayi bata bashi amsa ba hakan yasa ya miƙe cikin takunsa na isa ya ƙaraso inda take hannunta ya kama sannan ya koma ya zauna ya zaunar da ita bisa cinyarta yana kallon kyakkyawar fuskanta ya ce"Gimbiyata yau gida aka tuna ne?, Sarautar ce ta tashi?" da sauri ta rufe fuskarta a ƙirjinsa tana dariya ta ce"kai kam bakada dama wlh" dariya shima ya yi sannan ya ɗago fuskar tata yana kallonta cikin ido ya ce"kema ai kin sani banda ma yanzu kina hanani" turo baki tayi kamar wata ƙaramar yarinya ta ce"to ai kai bakasan ka girma ba" jan kumatunta ya yi ya ce" to kenan dan mutum ya girma bazai enjoying lfy ɗinsa ba?" girgiza kai kawai tayi sanin halin mijin nata ta ce"ai shikenan".

*YOBE STATE*

*BANI KURA RESIDENCE*

Kallon Falmata ta yi da mugun mamaki ta ce"wai me kike nufi nifa bangane ba?" tsaki Falmata ta yi ta ce"ke daÉ—ina dake rashin fahimta wlh, yanda nace miki haka zamuyi idan dare ya yi yau malam aikin dare zai yi kawai sai mu koreta ni a tunanina hakan shine kaÉ—ai mafitarmu"

"Aikuwa bazaku taɓa samun nasara ba Allah yafi ƙarfin ku"
Chapter 5 · 0% Book details