← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 29

Sashe 23

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ya jikin nata?" numfasawa Zaki ya yi ya ce"da sauƙi Alhamdulillah" zama ya yi kan kujera yana kallonta ya ce"Muhaira" buɗe idanunta ta yi ta kalleshi amma bata ce komai ba, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa tsayawa Zaki ya yi yana kallonsu sai kuma ya ɗauke kai daidai nan Dr ya shigo ɗakin sake duba jikin nata ya yi sannan ya yi discharging nasu kallonsa tayi ganin yanda ya juya baya tura baki tayi gaba ya yi murmushi ya ce"hau na goyaki mana" ɗauke kanta tayi sai kuma ta hau bayan nasa tana riƙeshi sosai dariya ya yi mara sauti ya ce"tunani kike zan ya dake?" batace masa komai ba ya girgiza kansa sannan ya fice daga asibitin zaune suka sami Taj a mota yana jiransu sauketa ya yi ta shiga back seat sannan shima ya buɗe gaba ya shiga. Sunyi nisa sosai Taj ya ce"Dmash fa yana gidanka nd kuma yana jiran ka dawo ya karɓi Muhaira ne kuma ba shi kaɗai bane sunada yawa gabaɗaya ma dai abun nasu da akwai alamar rashin gaskiya saboda haka kar kaje gidan yana tunanin ya haɗa baki dani ne domin na ce masa zan kawo masa Muhaira without ur permission" kallonsa Zaki ya yi sai kuma ya yi murmushi ya ce"daman nasan dole haka zata iya kasancewa kada ka damu ka kasance a tare dashi komai ya kusa zuwa ƙarshe in sha Allah anjima zan yi magana da Sir" gyaɗa masa kai Taj ya yi sannan ya kalli Muhaira wacce tayi tsuru da idanu tana kallonsu murmushi ya yi ta mudubin ya ce"Baby lafiya?" turo baki tayi tana fashewa da kuka harararsa Zaki ya yi ya ce"wannan ma ai rashin mutunci ne kasan da anyi mata magana kuka take amma zaka kulata ni wlh nagaji da jin kukan nan" dariya ya yi ya ce"to na tuba please ki daina kuka kinji" cikin shashshekar kuka ta ce"ni gida zani" Taj ya ce"to kiyi shiru za'a mayar dake kinji" girgiza kai Zaki ya yi bai sake cewa komai ba har suka ƙarasa gidansa dake Al Hamra.

Haɗaɗden gidana amma bai kai wancen girma ba kallon gidan kawai Muhaira tayi ganin ba gidan da ta saba zama ba jan hannunta Zaki ya yi ya haura da ita upstairs wani parlon ya buɗe mata ta shiga sannan ya ce"oya kiyi sallah zan kawo miki abinci sai kisha drugs ɗinki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya juya ya fita ita kuma ta shige bedroom, zaune ya tararda Taj yana danna wayarsa yana ganin ya fito ya miƙe ya ce" ya kamata na tafi yanzu" numfasawa Zaki ya yi ya ce"inason na tambayeka wani abu daman" Taj ya ce"ina jinka" "a ina ka samo yarinyar nan ne?, sannan wane ya siyar da ita kaine ka sanshi ni bansan wane ne ba please ka nemo min information nasa" gyaɗa masa kai Taj ya yi sannan suka jera suka fita.

Kwance ya sameta amma ba bacci take ba tana ganinsa ta miƙe zaune har sannan kuma fuskarta a kumbure take zama ya yi a kan carpet ɗin parlon da hannu ya yi mata alama da tazo ta taso a hankali ta zauna gefensa kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita kan cinyarsa ya ɗora kansa bisa wuyanta cikin sanyin murya ya ce"ke dawa? wane ya sakaki kuka?" riƙe hannusa tayi sai kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka dafe kansa ya yi ya rungumeta ya ce"ya isa kidaina kukan okay" sosai tayi kuka a jikinsa sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya shafa bayanta ya yi ya ce"now tell me mene yasa kike kuka?" cikin shashshekar kuka ta ce"ni gida zani banason nan ka mayar dani gida" murmushi ya yi ya ce"shine kike rigima?" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kanta tana turo baki gaba tattausan hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta kallonsa tayi sai kuma tayi saurin rufe fuskarta da hannunta tana faɗawa jikinsa cikin shagwaɓa ta ce"Allah ni bansoo!" murmushi ya yi ya ce"to naji bakiso me kike so?" "Ni kawai ka mayar dani gidanmu Allah" shafa kanta ya yi ya ce"i promise you zaki gida sooner or later" "to ni yanzu yanzu nakeso naje ai" tafaɗa tana ɗago kanta daga jikinsa jan kumatunta ya yi ya ce"to yanzu so kike nazama fly na kaiki gida?" murmushi tayi tana jan cute beard ɗinsa ta ce"to nan a ina muke?" waro idanuwansa ya yi tayi saurin kautar da fusakarsa cikin shagwaɓa ta ce"ni kadaina kallona da wannan idanun naka abun tsoro" dariya sosai Zaki ya yi rabonda ya yi dariya mai yawan haka har ya manta Muhaira kuwa zuba masa idanu tayi kamar ta samu Tv bata taɓa ganin mutum mai kyau da cikar zati irinta Zaki ba yanada wani irin halitta mai matuƙar ɗaukan hankali yanayin jikinsa zaka irin zaton balarabe ne dan ko kaɗan baya kamada hausawa dukda ya iya hausan sosai. Ganin yanda take kallonsa kamar ta samu Tv yasa yakai hannunsa wajen idanunta da sauri ta ture hannunsa ta ce"A'aaaaa kabarni ni" murmushi ya yi ya ce"idanun nawa ne suke baki tsoro?, da idanuna da naki wannan ya kamata ace anji tsoro ke baki kalli naki idanun bane kamar wata mage?" wani kyakkyawan murmushi tayi tana riƙe da gemunsa ta ce"ai kai naka manyane kamar na dodo" "dodo kuma mene ne haka?" ta ce"abun tsoro mana wanda Dadata take bani lbr a tatsuniya" murmushi ya yi yana kama hannayenta ya ƙura musu idanu kamar wanda yake kallon wani abu kallon hannun nata tayi itama sai kuma ta janye su daga hannunsa ajiyar zuciya ya sauke ya ce"in tambayeki?" gyaɗa masa kai tayi ya ce"bani labarin inda kike sannan a ina Taj ya ɗaukoki ina iyayenki?" turo baki ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi ta ce"Papina ya tafi ya barni Dada tayi ta cemin zai dawo amma bai dawo ba sai kuma Dadata ta mutu tabarni duk sun tafi sun barni banida kowa sai Bani kura shine kawai ya ɗaukeni sannan..." katseta ya yi ya ce"eat ur food first sai ki bani lbrn" gyaɗa masa kai tayi sannan ya miƙa mata plate ɗin abincin kwaɓe fuska tayi bata karɓa ba girgiza kansa ya yi kawai sannan ya ɗauki spoon ɗin ya fara bata abincin a baki lumshe idanunta tayi saboda daɗin da abinci ya yi mata gyaɗa kanta tayi ta ce"unnnn daɗi" murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba dan shi a ƙa'idarsa idan yana cin abinci baya magana sbd haka ne itama ya yi mata shiru. Sosai ta ci abincin ta ƙoshi sannan ya bata drugs ɗinta dakyar tasha hardasu kuka tana gama sha kuma bacci ya ɗauketa a wajen wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya tashi ya fice daga parlon.

Kai tsaye ɗakinsa ya shiga yana zuwa ya faɗa bathroom ya yi wanka sannan ya fito shiryawa ya yi cikin wata jallabiya ash colour ya tufke kansa da ribbon ash colour sannan ya ɗauki turaren Creed Aventus ya fesa ƙarar da yaji wayarsa nayi ne yasa ya kalli inda take a hankali ya ƙarasa wajen ya ɗauka shiru ya yi yana kallon sunan dake kan screen ɗin wayar har sannan kuma bai ɗaga kiran ba yana ji har ya katse mamaki ne sosai kan fuskarsa duk da yasan zai iya kiransa amma ko kaɗan bai kawo yanzu ba ƙarar kiran ya sake ji a karo na biyu dafe kansa ya yi kamar wanda aka yiwa dole ya ɗaga shiru ya yi yana sauke wani numfashi daga ɗaya ɓangaren ma haka cikin sanyin murya ya ce"good afternoon sir" cikin kamilalliyar murya mai nuni da kamewa aka ce"Aliyu duk inda kake ka dawo gida" buɗe bakinsa ya yi zai magana yaji wayar ta katse kallon screen ɗin wayar ya yi sai kuma ya ajiyeta yana dafe kansa abubuwa nasan kwaɓe masa dole ne yayi azama ya yi abinda ya kawo shi ƙarar kiran wayar ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi kallon wayar ya yi sai kuma ya ɗaga cikin girmamawa aka ce"sir gamu nan kai muke jira" okay kawai ya ce sannan ya kashe kiran ya tashi ya fice kallon ƙofar apartment ɗinta ya yi sai kuma ya fice daga gidan.
Chapter 23 · 0% Book details