← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 29

Sashe 14

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ƙarar ruwan da yaji shine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi a hankali ya kalli gefensa ganin yanda wajen yake kwai alamar wanda ya faɗa yana numfashi, da sauri ya juya inda yabar Muhaira amma sai yaga wayam babu ita da sauri ya mike tsaye yana sake kallon ruwan, kenan yarinyar cikin ruwan ta faɗa??, Furzar da nunfashi ya yi yana dafe kansa sai kuma ya juya wajen wani table ya ajiye wayarsa sannan ya koma wajen without second thought kuma ya faɗa ruwan shima ji kake "tsundummmmm" saida ya fara iyo cikin ruwan sannan ya hangota can daga ƙarshen swimming pool ɗin kasancewar bashida wani zurfi yana zuwa ya jayonta ya rungume jikinsa sannan ya fito gaba ɗayan jikinsu sai ɗigar ruwa yake ajiye ya yi gefen wajen ganin ko numfashi batayi yasa ya matse cikinta da sauri ta fara tari ruwa na fitowa ta bakinta saida duk ruwan ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya idanunta sun rune sunyi jajur dasu tsaki ya yi sannan ya miƙe ya ɗauki wayarsa yana kallonta ya ce"tashi" shiru tayi masa tana kallonsa dan batajin zata iya tashi, ganin tana son ɓata masa lokaci yasa ya sunkuya ya ɗauketa kamar Baby suka fice daga wajen kai tsaye kuma motarsa ya nufa da ita.

Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa duk wata ƙofa ta jikinta sai rawar sanyi take hakan yasa ya kashe AC motar amma dukda haka bata daina ba, wani shahararren gudu ya shiga yi cikin ƴan mintuna suka ƙaraso gida. Suna shiga ya kamo hannunta ya fito da ita taka ƙafarta tayi wanda yasa ta fashe da wani irin kuka da sauri ya kalleta sai kuma ya ce"mene?" cikin kuka ta ce"wayyo ƙafata zai cire wayyo Allah nashiga uku Papi ka taimakeni" ganin yanda take kuka da gaske yasa ya sunkuya ya ɗauketa, suna zuwa ya kwantar da ita kan gadon yana kallon fuskarta ya ce"next time idan kika sake irin wannan shashancin saina zaneki" yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin, tura bakinta tayi sannan ta miƙe zaune ganin duk kayan jikinta a jiƙe suke gashi sun kama mata jiki, dakyar ta iya miƙewa ta shiga toilet tana hawaye saboda zafin da ƙafar ke mata.

"Zaki mene haka ka aikata?, inata jiranka ka kawomin yarinya amma naji shiru kasan halin daka sanya ni?, akanme zaki yi haka?, raina ya ɓaci sosai zuwa da safe lallai ka tabbata ka kawomin yarinyar nan or else..." Kallon screen ɗin wayar ya yi sai kuma ya ajiye yana taɓe baki ya gyara kwanciyarsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi. Wajejen 2am ta farka saboda tsananin ciwon da jikinta ke mata ga ƙafarta kamar ana sassara mata ita haka takeji ganin bazata iya cigaba da zama ba yasa ta miƙe zaune tana sakin wani sabon kuka babu wanda zai taimaketa dan ko tafiya bazata iya yi ba ganin ciwon na neman hallakata yasa ta sauka daga gadon ta shiga rarrafe kamar Baby haka har ta fito daga ɗakin kai tsaye kuma ɗakin Zaki ta shiga kwance ta sameshi yana baccinsa batayi wani tunani ba ta hau kan gadon cikin son samun ceto ta kwanta gefensa a hankali kuma ta shige jikinsa tana sakin wani irin numfashi. Above 5mins sai kuma wani wahalallen bacci ya ɗauketa tana sake rufe fuskarta cikin naked chest ɗinsa, duk abinda take Zaki na jinta dan tun sanda ta shigo ɗakin ya farka jin yanda jikinta ya ɗauki zafi yasa ya rabu da ita a hankali kuma zafin jikin nata ya dinga shiga nasa jikin lumshe idanunsa ya yi dan shima ba daɗin jikin nasa yake ji ba haka har bacci ya sake ɗaukeshi.

*FCT, ABUJA*

Sanye take cikin shigar atamfa Holland maroon colour ta ɗora veil fari akai dukda ba wani babba bane amma tayi kyau sosai, kallonta Najeeb ya yi ganin yanda ta haɗe rai ya ce"Ma'eesha" batareda ta kalleshi ba ta ce"na'am" "naga kamar baki saurarena" kallonsa tayi da manyan idanunta sai kuma ta tura baki ta ce"ai naga kunnene ki ji kuma ina jinka" numfasawa ya yi ya ce"shikenan na baki lokaci kije kiyi tunani da kanki ina fatan za ki yanke shawara mai kyau" kallonsa tayi har zata yi magana sai kuma tayi shiru ta juya tabar wajen kawai, girgiza kansa ya yi idan ba soyayya ba ai ya shige ajin yarinya ta dinga wulakanta shi. Kallonta Fateemah tayi ganin yanda take ta haɗe rai ta ce"wai daman Ma'eesha mene haka?, bakison mutumin nan fine amma haɗe ran na mene ne?" kwafa ta yi ta ce"wlh idan har bai yi a hankali ba sai na yi masa rashin mutunci nifa banason irin haka ya fara takuramin wlh" murmushi Zeey ta yi ta ce"nima dai abinda nagani kenan, ni wlh ban taɓa tunanin ma zai yarda ki dinga yi masa irin wannan wulaƙancin ba mutum mai hankali da aji" a hasale Ma'eesha ta ce"to ni na kawo shi ai shi ya kawo kansa inda za'a wulaƙanta shi wlh idan bai yi wasa ba saina yi masa abinda har ya koma da Allah bazai manta dani ba" girgiza kai Fateemah tayi ta ce"to Allah ya wuci zuciyarki shalele" harararta tayi ta ce"ni dai ku taso muje wajen sir Ahmad na bashi assignment ɗina" okay suka ce sannan suka tashi.

Zaune suke a main parlon na gidan banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi Mommy ce ta kalli General ta ce"yallaɓai daman inason zan tambayeka idan babu damuwa" ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi ya ce"uhnn inaji" numfasawa tayi sai kuma ta ce"idan babu damuwa inason zanje gida zuwa gobe" yana riƙeda glass cup ya ce"ohk Allah ya kaimu" murmushi tayi ta ce"daman idan babu damuwa inason zan tafi da Ma'eesha" kallonta ya yi for some minutes sai kuma ya girgiza kai ya ce"tana zuwa makaranta saboda haka bazatayi fashin skull ba saidai idan anyi hutu" Okay ta ce amma har cikin ranta bataji daɗi ba, tura baki Ma'eesha tayi tana jin haushin General daya ce ba zata jeba dan ita tanason zuwa wani waje kodan tayi yawo. Mikewa ya yi bayan ya goge bakinsa da tissue ya ce"zanje Villa" okay sukace ya kalli Ma'eesha wacce take kallonsa ya ce"Shalele zo ki rakani" da sauri ta miƙe tana murmushi ta ce"yawwa muje Father" girgiza kai Mami ta yi ta ce"ƙafar yawo shige ki ɗauko veil to". Buga ƙafarta tayi tana ƙunƙuni ta haye sama da gudu dan kada General ya tafi ya barta, murmushi ya yi kawai tun daga sama take cewa"Father baka tafi baaa" dariya suka yi duka har ta sakko tana haki kama hannunta ya yi ya ce"ki daina gudu kar wani abun ya sameki dear" gyaɗa masa kai tayi sannan sukai waje Mommy ta ce"au ko sallama ba zakiyi mana ba?" ɗaga musu hannu tayi tana dariya, miƙewa Mami ta yi ta ce"Allah ya shiryaki Ma'eesha" Mommy ta ce"Ameen".

*FAROOQ POV*

Murmushi Abeed ya yi ya ce"kai baba kanada sanyawa kanka damuwa wlh, wai me kake nema da har zaka bari ranka ya dinga ɓaci nifa idan ni ne kai wannan yarinyar tasa zan shiga na fita na aura sai nayi amfani da ita wajen kwato abinda yake hannunsa karka manta yana mutuwar sonta sai ka dinga tilastata tana karɓar kuɗaɗe a hannunsa haka har ka ja naka kasan" furzar da wani irin numfashi ya yi yana ajiye drink ɗin hannunsa ya ce"kai daɗina dake rashin tunani, idan da zan iya auren yarinyar ai da tuni nayi hakan bama sai kaji ba, ni yanzu kawai neman hanyar da zan kawar da yarinyar nake idan nayi hakan nayi rabin aikin" dariyar mugunta Abeed ya yi ya ce"to saika ɗaura ɗamara dan ni ba ɗan kowa ba bazan shiga ba haka kawai ta kwaɓe azo a kamani ubanwa zai fito dani, kaima kuma zan baka shawara kayi komai a sannu kasan dai ubanka mahaifi ba kowa bane idan ka jawo abinda soja zai ɗaureka kaga kayi ba wan ba ƙanin" miƙewa Farooq ya yi yana buga table ɗin gabansa ya ce"kai a wa ka faɗamin magana wlh har abada nafi ƙarfin a kulleni dan ko a yanzu inada abinda zai isheni rayuwata saboda haka maintain ur words!" ya ƙarashe maganar yana nuna shi da yatsa, tashi Abeed ya yi shima yana murmushi ya ce"Farooq kenan idan har da kanada abinda zai isheka kayi rayuwarka so why kake neman dukiyar wasu?, kayi rayuwarka da abinda ubangiji ya raba ya baka mana kadaina hangen dukiyar wasu ka zauna matsayinka na agola wanda aka kula da rayuwarsa kamar ɗan gida, saboda girman Allah wlh sai kayi mamakin yanda zakaci gaba a rayuwarka" tsaki Farooq ya yi sannan ya ɗauke wayarsa da car key ɗinsa yabar wajen girgiza kai Abeed ya yi sannan shima ya ɗauki mukullinsa ya yi waje.

*Asokoro Villa*
Chapter 14 · 0% Book details