← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 29

Sashe 29

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Furzar da wani irin zazzafan numfashi ya yi yana sake duba rollex ɗin hannunsa misalin ƙarfe 3am ne ɗan siririn tsaki yaja daidai lokacin motar tayi parking da sauri ya fito ya ƙaraso cikin ladabi ya ce "I'm sorry sir" taɓe baki ya yi bai ce masa komai ba ya yi gaba shi kuma yabi bayansa Saida ya sanya trolley ɗinsa a bot sannan ya dawo wajen driver seat ya tayar da motar da wani irin speed suka bar airport ɗin. A firgice ta farka tana Kalle-Kalle kallonsu Mami wanda suke bacci ganinsu tayi tamkar wasu dodanni hakan yasa ta runtse idonta da gudu kuma ta fice daga ɗakin kai tsaye stairs tayi tana zuwa ta buɗe ƙofar entrance ɗin gidan ta fita da gudu, buɗe gate ɗin da tayi shine ya farkar da gatemans ɗin wanda bacci ya ɗaukesu da sauri suka kalli ƙofar sukayi wajen Kofar da gudu saidai me sam ƙofar taƙi motsi gabaɗaya ta cije tana fitowa ta yi kan titi tana gudu kamar mahaukaciya wani irin wawan birki drivern yaja, ɗago kansa ya yi ya kalleshi kafin yayi Magana yaga mace a gabansu tsaki ya yi sannan ya fito daga motar kallonta ya yi da gudu ta ƙaraso wajensa ta riƙe hannusa tana nuna masa bayanta waro idanuwansa ya yi da mamaki ya ce "Muhaira?" shigewa jikinsa tayi tana sakin kuka rungumeta ya yi ya shige motar da sauri drivern yaja suka bar wajen buɗe gate ɗin ya yi daidai da farkawar General fitowa ya yi saman bene sbd hayaniyar mutanen da yaji hangosu ya yi sunata kokawa da ƙofa lokacin sojojin suka fito wani soja ne ya ja ƙofar da ƙarfi aikuwa ta buɗe da gudu sukayi waje suna nemanta sakkowa ya yi da sauri yana zuwa ya kalli sauran waɗanda basu fitan ba ya ce"what's going on?" cikin inda inda ya ce"sir.. sir...daman Ma'eesha ce ta... fita" "what?" da sauri General ya buɗe ƙofar ya yi waje shima yabi bayansu. Har akayi sallar asuba suna waje saidai babu Ma'eesha babu alamarta dawowa gidan suka yi yana shigowa parlon ya tarar dasu kowa yayi cirko-cirko a tsaye kallonsa Mami tayi ganin yanda idanunsa suka faɗa cikin rawar murya ta ce"yallaɓai tana....tana ina?" girgiza mata kai General ya yi hawaye na zirarowa kan fuskarsa duk dauriya irin tasa

"Tassssssssss"

Da sauri suka juya suka kallon Mami wacce ta faɗi ƙasa sumammiya girgiza kai General ya yi sannan ya yi hanyar upstairs saidai ko stairs biyu bai taka ba ya haɗo shima nan ƙasa a sume. Wani irin tashin hankali ne ya mamaye a halin da gudu Aleema tayi kan Mami tana fashewa da kuka ta ce"Mamiiiiiiiiiii!!"

*SHIN WANENE ZAKI?*
*INA MA'EESHA TA TAFI?*
*SHIN DA GASKE ZAKI YA RASU KO A'A?*
*WACE IRIYAR RAYUWA MUHAIRA XATAYI IDAN YA KASANCE ZAKI YA TAFI YA BARTA?*
*SHIN WANE WANDA YA YIWA MA'EESHA KURCIYA?*
*WANE NE WANDA YA KIRAYETA DA SUNAN MUHAIRA?*
*MENE NE HAÆŠIN MUHAIRA DA MA'EESHA HAR SUKE KAMA ÆŠAYA?*
*INA MAHAIFIYAR KHALIL TAKE?*
*SHIN MUHAIRA ƳAR WACE KUMA MENE NE DALILIN DAYA SANYA AKA YARDA ITA TUN TANA JARIRIYA?*
*SHIN MEYASA AKE CEWA BA ITA BA CE! IDAN BA ITA BA CE TO WACECE?*

*DUK WADANNAN TAMBAYOYIN DAMA WASU DA DAMA ZAKU SAMU AMSARSU SU NE A YAYIN DA KUKA BIYA ONLY 500# FOR NORMAL GROUP 1K FOR VIP VIA 9086030007 HAUWA LAWAN OPAY EVIDENCE OF PAYMENT VIA 08106608363 OR 07041901078 KI BIYA KI KARANTA CIKIN SAUƘI DA NISHAƊI SISTER*

*FOR MORE INFORMATION A YIMIN MAGANA VIA MY NUMBERS*

_TAKU HAR KULLUM NANAMEERA MU HAÆŠU A PAID GROUP_.
Chapter 29 · 0% Book details