Sashe 26
Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe 5pm Khalil ya iso gidan har parlon ya zo ya kama hannun Ma'eesha suka fita shida ita suna gidan gaba Aleema kuma na gidan baya har suka isa mall ɗin babu wanda ya ce komai a cikinsu kowanne da abinda ya dameshi. Siyayya sosai suka yo duk wani abu na nau'in kaya babu wanda Khalil bai siyawa Ma'eesha ba wani abun ita take nunawa wani kuma shi yake zaɓar mata hatta Aleema saida ya siya mata sai wajejen 6:30pm suka bar wajen kai tsaye kuma wani park ya kai su wajene wanda aka ƙawatashi da kayan wasan yara irinsu lilo, swimming pool da masu kayan wasan sannan akwai nau'i na abinci kala-kala a wajen zama sukayi kan kujeru suna Kalle-Kalle ya yi hakane kuma sbd ya ɗauke hankalin Ma'eesha dan Mami ta faɗa masa halin da take ciki dukansa ta yi hakan yasa ya juyo yana kallonta ya ce"mene ne?" turo baki ta yi sannan ta nuna masa can gefe inda akayi wani waje ana siyarda ice-cream kallonta ya yi sai ya ce"za ki sha?" da sauri ta ɗaga masa kai dungure mata kai ya yi ya ce"kinsan ai bakida lafiya ko sbd haka bazan siya miki ba" kuka ta sanya masa amma ya yi mata banza dan daman shi haka halinsa yake inda ya ce bazai abu ba to kome za'a yi bazai yi ɗin ba babu irin kukan da Ma'eesha batayi amma ya yi funfurus popcorn kawai ya siya musu suka bar wajen ana kiraye-kirayen sallar magrib ya yi parking fita Aleema ta yi ta shige cikin dan duk a gajiye take, murɗa handle ɗin ƙofar tayi taji a rufe hakan yasa ta juyo ta kalleshi da idanunta da suka yi jajur alama tayi masa daya buɗe motar ya girgiza mata kai jawota ya yi yana gyara zamanta a kan cinyarsa ya ɗago fuskarta hannu tasa ta tureshi tana fashewa da kuka yasan fushi take dashi murmushi ya yi yana haɗe jikinsa da nata ya rungumeta yana shafa kanta sosai tayi kuka a ƙirjinsa kafin ya sake ɗago fuskarta ya yi coping da tasa suna sauke numfashi a tare saurin janye fuskarta tayi saboda wani iri da taji a jikinta murmushi Khalil ya yi ya juyo da fuskarta ya kama kunnensa alamar ta yafe masa ɗauke kanta tayi hawaye na zirarowa kan kuncinta dafe kansa ya yi ya ce a hankali"I'm sorry eeshana" kallon bakinsa tayi sai kuma ta nuna masa ƙofa alamar ya buɗe mata da hannu shima yayi mata alama da ta yafe masa saurin gyaɗa masa kai tayi dan Allah Allah take tabar motar buɗe mata ya yi yana gani ta sauka da sauri ta shige parlon daidai nan Farooq ya fito da kallo yabi motar yana gani har securities suka gama kwashe kayan dake motar suna shiga dashi gidan sannan ya juya ya bar gidan taɓe baki Farooq ya yi yana kallon uban kayan da suke shigowa dashi ko ba'a faɗa masa ba yasan ba ƙananan kuɗi aka kashe ba furzar da wani zazzafan numfashi ya yi sannan ya buɗe motarsa ƙirar coralla ya shiga da wani irin speed ya bar gidan.
"Haba Aleema wannan kayan ai sunyi yawa"
Turo baki ta yi Fulani ta ce"babu wani yawa da sukayi daman haka akewa kowace ƴa idan za'a aurar da ita" murmushi Mami ta yi tana kallon mahaifiyartata sai kuma ta ce" to shikenan ai" dariya Aleema ta yi ta ce"Fulani kice ta ɗaga ki" kallonta matar tayi kyakkyawace sosai kuma sannan kamarsu ɗaya da Mami dan harma tafi Mami kyau kana ganinta kasan ta manyanta sosai amma kuma kuɗi da mulkin daya zauna musu shine abinda ya ɓoye tsufan nata Fulani kenan mahaifiya a wajen Mami kuma matar sarkin Katsina marigayi Alhaji Aliyu ɗan sarari ya yi tashen kuɗi a lokacinsa dan babu wani sarki wanda ya kai shi a arziƙi a lokacin yanzu kuma ɗansa Alhaji Ahmad Aliyu shine wanda yake karagar mulkin mace ce mai faran faran da jama'a musamman jikokinta suna matuƙar jin daɗin zama da ita kasancewar sunanta aka sawa Ma'eesha yasa take matuƙar sonta duk cikin matan sarki na wannan lokacin babu wacce ta kaita ƙarfin iko dan ita ce wacce mai martaba yafi so kasancewar da ita ya yi aure tun saurayi da budurwa kuma ita ƴar sarki ce wannan kenan.
Hararar Aleemah ta yi ta ce"ai sai kizo ki sanya ta ɗagani ja'ira kawai" gwalo Aleema ta yi ta ce"ke kam kin fiye rikicin tsufa wlh ko mema kika zo yi nan ohho!" Cikin kunfar baki Fulani ta ce"ubanki Mahamuda shi nazo yi nan ja'irar yarinya kawai" buɗe baki ta yi zata sake magana Mami ta ce"ke shiga hankalinki uwartawa kika mayar abar wasanki" da sauri Fulani ta ce"a'a kekam Asma'u banson ƙin Allah idan banyi wasa da jikokina ba dawa zanyi wasa kinsan dai su kaɗai gareni" girgiza kai Mami ta yi dan ta fuskanci rikicinta ne ya tashi hakan yasa ta miƙe ta ce"to Mama bari na kawo miki abinci" ta ce"ai da nayi zaton babu abinci a gidan ne nasa a kiramin janar din naji dalilin da zai barki da yunwa" tuntsirewa Aleema ta yi da dariya ta ce"to ke Fulani idan baya basu abinci ina ruwanki" banza Fulani tayi mata tana shafa kan Ma'eesha wacce bacci ya ɗauketa.
Daren ranar basu kwanta da wuri ba sbd hirar Fulani hatta Ma'eesha da ba jin abinda take cewa tayi ba saida ta zauna tana kallonta idan taga tayi wani abun tayi dariya saida Mami ta zo ta lallaɓa Fulani sannan ta kwanta, da sassafe kuma masu gyara jiki suka dira a gidan part guda Mami ta ware musu aka basu abinci sannan aka kai Ma'eesha wacce take ta kuka dan harga Allah baso take ba yinin ranar bata fito ba dan hanata suka yi sai wajen magrib sannan ta sanya kuka dole suka barta ta tafi tana zuwa ta kwanta jikin Fulani wacce take ta mita ta gyaran jikin wai an ɗauke mata ita Ita dai Mami batace mata komai ba sai Aleema ce take janta. Haka aka dinga yi mata gyaran jikin har ya rage sauran kwana uku a ɗaura aure kasancewar ba wani fita zasu yi ba tunda batada lafiya yasa aka ɗauko mai henna tazo har gida tayi musu ita da Aleema washegari da azahar tawagar Mami suka iso gidan ciki harda matar sarki Hajiya A'isha mace mai karamci da Mutane ba bahaushiya bace ta kasance balarabiya dan lokacin da sarki yaje Makkah gidansu abokinsa ya ganta ya ce yana sonta bai baro ƙasar ba saida aka ɗaura musu auren da ita. Tuni gidan General Ibrahim Tijjani mai Zamani ya cika maƙil da manyan mutane kowa sai hada-hadarsa yake a cikin gidan Ma'eesha kuwa tana part ɗin General dan ko kaɗan batason taron mutane ranar da akayi mata henna da rana aka ɗauko photographers aka dinga ɗaukanta hotuna tayi kyau cikin lufayar da aka ɗaura mata purple colour gashin nan yasha gyara ya zubo har gadon bayanta sai sheƙi yake yi ƙunshi mai matuƙar kyau aka yi mata sai murmushi take musamman sanda taga su Fateemah sun zo hakan ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba.
*RIYADH*
*AL HAMRA RESIDENCE*
Kallonta ya yi ganin yanda take faman kuka kamar ƙaramar yarinya a kwana biyun nan gaba ɗaya ta hanashi sukuni gashi yanzu ko kaɗan baya samun lokacin kansa abubuwa duk sun sha masa kai gajiya ya yi da jin kukan kawai ya kashe light ɗin daƙin duhu ya mamaye ko'ina cikin wata iriyar murya ya ya ce"ga dodo nan"da gudu Muhaira ta taso tana zuwa ta shige cikin blanket ɗin ta cukwuikuyeshi tana sakin kuka shafa kanta ya yi a hankali ya ce"ya isa to kiyi shiru karya kamaki" ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana sake shigewa jikinsa dan gaba ɗaya a tsorace take cikin kuka ta ce" ni ka kaina gida Papi banso nan ka tafi dani Allahhhhh!" numfasawa ya yi ya ce"bana faɗa miki xan kai ki ba gidan wa zamu ce idan munje garin naku?" turo baki tayi ta ce"ni banida gida kawai kasuwa Gashua zaka kaini wajen Mama mai abinci anan nake kwana" da mamaki ya kalleta cikin duhun ya ce"wace haka?" turo baki ta yi ta ce"ni duhuuu" murmushi ya yi sannan ya kunna dum light hakan yasa ɗakin ya yi wani irin blue ya kalleta ya ce"now tell me wace ita?" Numfasawa tayi sannan ta fara bashi lbrn rayuwarta tun daga farko har zuwa sanda Taj ya saceta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba dan bai yi zaton hakan zai iya kasancewa da mutum ba cikin kuka ta ce" dan Allah Papi karka kaini wajen Bani kura wlh banaso bazan iya aurensa ba dan Allah Papi kasuwa zaka kai ni" rungumeta ya yi ya ce"ya isa haka stop crying sleep kinji" yana ji tana shashshekar kuka har bacci ya ɗauketa shafa kanta ya yi sannan ya gyara mata kwanciyarta ya rufeta da duvet ya kashe AC ya fito parlon kai tsaye kitchen ya shiga ya haɗa coffee sannan ya fito ya shiga wani daƙi gaba ɗaya bangon ɗakin an rubuceshi wani wajen kuma an maƙala hutuna babu haske a ɗakin hakan yasa ba komai ake iya gani ba zama ya yi akan wata kujera da table a gabansa ya buɗe system ɗin ya shiga dannawa a hankali yana sipping coffee ɗinsa sai wajen 3am sannan ya tashi daga wajen ya rufe system ɗin ya fito kai tsaye kuma toilet ya shiga ya yi wanka ya ɗaura alwala sannan ya shirya cikin wata embroidery Jallabiya Black colour ya shimfiɗa prayer mat ya shiga sallolinsa na nafila har lokacin kiran asubahi ya yi saida ya tasheta sannan ya fita dan gabatar da sallar a masjid bayan ya idar kuma ya zauna karatu bai shigo gidan ba sai wajen 6am kai tsaye kuma kan kujera Three seater ya kwanta ya lumshe idanunsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi.
Ringing É—in wayarsa ne ya farkar dashi yana É—agawa ko sallama bai yiba ya ce"ohk I'm coming" ya ajiye wayar ya shiga bedroom kai tsaye bathroom ya shiga ya yi wanka sannan ya fito ya shirya a gurguje kallonta ya ya ganin yanda take bacci hankali kwance kasancewar ranar weekend yasa bai tashe ba ya yi waje.