← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 29

Sashe 3

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani zazzafan numfashi ya sauke bayan ya saki curtain ɗin, a hankali cikin tafiyarsa mai nuni da isa ya ƙaraso gefen kujerar dake gaban gadon ya zauna sanye yake da wata Polo T-shirt white colour sai kuma wani Cargon Three-quater black colour a jikinsa ba wani fari bane can haka zalika kuma ba baƙi bane yana dai da haskensa dai-dai misali, ɗan ƙaramin tsaki yaja sannan ya buɗe system ɗin gabansa ya shiga dubawa. Duba da irin yanda yake kallon system ɗin zaka fahimci tabbas wani abu mai matuƙar muhimmanci yake gabatarwa, turo ƙofar ɗakin tayi bakinta ɗauke da sallama a ciki ya amsata sannan ta ƙaraso gabansa zama tayi gefensa tana sanye cikin wani material black colour mai adon flower pink ɗinkin doguwar riga A-shape mug ɗin gabanta ta ajiye masa gefen table ɗin gabansa ta cigaba da kallon abinda yake, above tens minutes sannan ya kammala ya rufe system ɗin sai a sannan ya ɗago yana kallonta fara ce tass kuma asalin kyakkyawa dan ko ba'a faɗa maka ba kasan ita ɗin ba ta kasance cikin ƙabilar Hausawa ba ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana wasa da fingers ɗinta masu ɗauke da zanen flower wacce tayi matuƙar amsar farar fatarta taɓe baki ya yi sannan ya ɗauki mug ɗin data ajiye a hankali kuma yakai tea ɗin bakinsa wani runtse ido ya yi saboda wani irin zaƙi da yaji har cikin kansa da sauri ya ajiye mug ɗin yana mata wani hargitsatsen kallo ya ce "Ma'eesha I'm play with you?" kallonsa ta yi fuska a kwaɓe ta ce" A'a yaya I'm sorry wlh banson sugar ya yi yawa ba I'm so sorry" kallonta ya yi from head to toe sannan ya yi tsaki ya tashi bai tsaya cigaba da jin abinda take faɗi ba ya ɗauki wayarsa ƙirar iphone 14pro max ya yi waje. Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙirjinta sanin halin yayan nata sai kuma ta miƙe itama tabi bayansa.

A nutse take taka stairs ɗin benen har ta sakko gaba ɗaya, ya rabbi wani irin haɗaɗɗen parlon ne irin mai tafiya da imanin mutum ɗin nan komai na cikinsa golden colour ne tun daga kan kujeru, curtains, carpet, center table even bulb da suke parlon golden colour suke bayarwa banda sanyin A.C babu abinda ka keji a parlon sai kuma wani irin daddaɗan ƙamshin da yake fita daga kowace kusurwa ta parlon ko ba'a faɗa maka ba kasan wannan parlon bai yi kamada na ƙananan mutane ba ko kuma basu ji da ƙaramin arziƙi parlon ne irin wanda koda a cikin Villa yake sai ance ya haɗu iya haɗuwa, parlon ne na irin manyan nan wanda suka jiƙu da manyan kuɗaɗe, a hankali ta ƙaraso cikin parlon inda ta hangin iyayen nata. Zaune yake kan kujera Three seater yana sanye da wata dakakkiyar shadda Madam gezner blue black ɗinkin jamfa da babbar riga idanunsa maƙale da wani farin tabarau yayinda yake kallon jaridar dake hannunsa da alama kuma karantawa yake duba da yanda ya bada full attention ɗinsa a wajen magidancin mutum ne dan aƙalla zai kai irin 60yrs ɗin nan amma idan har kayi duba da yanayi na siffarsa zaka iya cewa bai fi 46yrs saboda kwarjini da kuma hutu wanda ya zauna masa. Major General Ibrahim Tijjani mai Zamani kenan wanda ke riƙeda muƙamin shugabannin sojoji na ƙasa kuma sanannen ɗan kasuwa mai tashen arziƙi mamallakin Companyn mai Zamani corture indai magana kake ta kuɗi to tabbas M.G Ibrahim ƙarshene sannan kuma uwa uba ya kasance mutum mai taimakon na ƙasa dashi wannan shine dalilin daya sanya yake da mabiya daga kowacce fuska. Da sauri ta zauna gefensa tana shagwaɓe fuska ta ce" Father narhhhh!!" murmushi ɗauke a fuskarsa yake kallon tilon ƴar tasa kallo mai nuna zallar so da ƙaunar da yake mata shafa kanta ya yi cikin kamilalliyar muryarsa ya ce" Shalelen Father what's wrong uhn" turo baki gaba tayi ta ce" Father ko ba yaya Farooq bane" da sauri Farooq wanda yake zaune kujerar dake opposite tasu ya ɗago yana kallonta amma bai ce komai ba, murmushi Father ya yi sanin halin rigimarta ya ce"keda yayan naki ne kuma yanzu?, To kiyi haƙuri bazai sake ba ya tuba" taɓe baki ta yi sannan ta ce"Father kace masa ya kaini saloon ɗin" dafe kansa ya yi yana zare glasses ɗin idanunsa ya ce" ohho!! Shalelen Father rigima ko?, Ki tambayeshi da kansa idan yaga zai rakaki fine idan kuma yanada wasu uzurin sai ki tafi da guards zasu jiraki" girgiza kai tayi ta ce"nooo! nasan ma zai rakani" kallon Farooq ta yi wanda yake kallonsu tun ɗazu ta ce"yaya zaka rakani ko?" da sauri ya gyaɗa mata kai ko babu komai ya samu damar da zai gasa mata aya a hannu, murmushi ɗauke a fuskarta ta kalli Father ta ce"yawwa Father kaji ko ya ce zai rakani" numfasawa Father ya yi ya jinjina mata kai sannan ya miƙe yana riƙe da hannunta ya ce"na tayaki murna amma karku daɗe zan fita byee" gyaɗa masa kai ta yi tana murmushinta mai kyau ta ce"ok Allah ya tsare hanya Father narh" kissing goshinta ya yi sannan ya yi waje.

# *BA ITA BA CE*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *love*.
# *SQUAD 2024*

# *Nanameera ce!*.
[8/1, 7:28 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

*nanameera08* _arewabooks_.

*@Nanameera08* _wattpad_.

*Nanameera*.

# *SQUAD 2024*

```Page 03```

Kallon Farooq ta yi ganin ya miƙe tsaye sai kuma ta ce" yaya bari na sauya kaya" taɓe baki ya yi bai ce mata komai ba ta juya tabar parlon, kwafa ya yi sannan ya yi waje. Haɗaɗɗen bedroom ne kana ganinsa kasan an kashe kuɗaɗe wajen haɗashi komai a bedroom ɗin purple colour ne coz ita ce favee colour ta Ma'eesha, kallon gefen bed ɗin ta yi sa kuma ta saki murmushi a hankali ta ƙarasa wajen ɗaukan Teddy bear ɗin ta yi wanda ita ce ta kasance purple colour ce sannan tayi waje.

*Haj.Salma pov*

Zaune take kan royal cusion ɗin dake zagaye da parlon idanunta bisa TV tana kallon show ɗin da ake haskawa a MBC Max turo ƙofar tayi hakan yasa ta ɗago dara-daran idanuwanta tana kallonta sai a sannan na ƙare mata kallo fara ce tass kuma asalin kyakkyawa kallon Ma'eesha nayi sannan na kalli Haj.Salma ko ba'a faɗa maka ba kasan Ita ɗin mahaifiyarta ce domin babu inda suka sha banban ta kammani zama tayi gefenta tana ɗora kanta a cinyarta ta ce"Mami zamu tafi"shafa kanta Mami tayi sannan ta ce"to Shikenan sai kun dawo Allah ya tsare hanya" Ameen Ma'eesha ta ce sannan ta miƙe dan fita daga parlon

"Ma'eesha!"

"Na'am Mami"

Kallon fuskarta ta yi sai kuma ta ce"where is your mask?" langwaɓar da kai tayi sai kuma ta ce"Mami yana cikin jakana" harararta Mami ta yi ta ce"oh daman amfaninsa kenan?, Bring it out my friend!" turo baki gaba ta yi sannan ta buɗe ƴar ƙaramar jakar hannunta ta zaro mask ɗin

"saka shi"

Kallon Mami tayi taga ta haɗe fuska babu alamar wasa sai kawai ta maƙala face mask ɗin sannan ta fice daga parlon tana buga ƙofar, girgiza kai Mami ta yi sannan ta ce"Allah ya shirya ki Ma'eesha". Zaune ta sameshi a motar yana danna wayarsa murmushi ta yi ta ce"sorry yaya I kept yhu waiting" ɗan siririn tsaki ya yi sannan ya ajiye wayar ya juya yana kallonta, sanye take da wata turkish Abaya black colour tayi rolling veil ɗin a kanta sosai tayi kyau tamkar balarabiya. Zazzafan numfashi ya furzar kafin ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa cikin cool voice ɗinsa ya ce"uhnn kinsan ai ina jiranki kika barni" langwaɓar da kanta tayi tana kallonsa idanunta rau-rau ta ce"I'm sorry yayana" girgiza kansa ya yi sannan ya saki hannunta ya kunna motar, akwai ƴar tafiya daga parking lot ɗin gidan zuwa gate dan kwalta ce aka shimfiɗa tamkar titi, tsaki tayi tana kallon sojojin da suke bakin street ɗin gidansu har zuwa cikin gidan, ita kam har ga Allah batasan irin wannan tsaron da ake musu. Kallonsa tayi ganin inda ya yi parking motar sai kuma ta ce"yaya naga ka tsaya anan?" banza ya yi mata ya ciro wayarsa ya shiga dannawa abinsa haɗe rai Ma'eesha ta yi ta kuma cewa"yaya Farooq kaga da wajen saloon ɗin can kuma kai kayi parking anan muƙarasa please kaga Father ya ce..."
Chapter 3 · 0% Book details