← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 29

Sashe 28

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali ya kalli mudubin dake maƙale a bangon wani killer smile ya yi sannan ya juya ya fita yana murɗa handle ɗin ƙofar wayarsa ta fara ƙara ɗan siririn tsaki yaja kafin ya kalli screen ɗin ganin sunan Taj yasa ya ɗaga ya ce"ya akayi Taj?" daga ɗaya ɓangaren Taj ya ce"sir da alama yau kana cikin farin ciki dan naji a muryarka" murmushi Dmash ya yi ya ce"tunda kabani farin ciki ai dole nayi" Taj ya ce"Sir ina gidan yanzu please kazo it's something important nd ka tawo da Muhaira dan kowane lokaci Zaki na iya kawo maka farmaki ina wajen da aka saba gudanar da taro kowa ya hallara kai kaɗai ake jira" okay Dmash ya ce sannan ya kashe wayar tura ƙofar ya yi ya shiga dakin zaune ya sameta inda ya barta gaba ɗaya idanunta sun kumbura saboda kuka dan murmushi ya yi sannan ya kamo hannunta bin bayansa Muhaira tayi tana Kalle-Kalle dan ita gaba ɗaya a tsorace take dashi tunda yace zai kasheta burinta bai shige taga Papinta yazo ya rabata da wannan wajen ba.

Babban ɗakin taro ne mai matuƙar kyau da haɗuwa kana kallon wajen kasan an kashe iyayen kuɗi wajen haɗashi wasu manyan mutane ne zaune a parlon kowannesu yana sanye da suit ko ba'a faɗa maka ba kasan ba talakawa bane dan kana ganinsu kaga kuɗi, tashi Taj ya yi yana murmushi ya ce"welcome Sir" jinjina kai ya yi sannan ya nemi guri ya zauna da kallo Muhaira ta bi Taj amma sai taga ko kallonta bai yi ba hakan yasa ta sunkuyar da kanta hawaye na zubo mata, tattauna suka shiga kan abinda ya shafe su Taj ya ce", yanzu ma na tawo muku da wasu ƙarin matan ai" dafa kafaɗarsa Petor ya yi ya ce"weldone Taj" murmushi kawai ya yi sannan ya miƙe ya ce"I'm coming" ya juya ya fice daga parlon kallonsu Tyha ya yi ya ce"come out" okay sukace sannan suka fito daga motar suka bi bayansa miƙewa tsaye sukai duka ɗan daso ya ce"wowwwww wannan tayi min kyau sosai" ya faɗa yana kallon Zeey, sunkuyar da kansu suka yi Taj ya ce"Nima nasani sir shiyasa na samo muku latest waɗanda nasan zaku ji daɗinsu fiye da ƙima" wata dariya suka yi sannan Dmash ya ce"Taj aikinka yana kyau akwai wata kwangila da nakeson na baka" murmushi ya yi ya ce"okay sir Ina ji" Dmash ya ce"ina son ka kashe Zaki idan kayi haka nikuma nayi maka alƙawarin baka ragamar daularmu wacce yanzu take hannun Zaki" miƙewa Muhaira tayi cikin kuka ta ce"a'a wlh bazai karɓa ba hamma Taj nasan ai bazaka kashe Papi ba ko?" ta faɗa tana riƙe hannun Taj wata kyakkyawar tsawa Taj ya yi mata wacce ta sanya tayi baya tana fashewa da kuka kallonsa Dmash ya yi ya ce"why zaka mata tsawa sai ka ce mata Eh" girgiza kai Taj ya yi yana miƙewa tsaye ya ce"i can't Sir coz bana ƙaunar yarinyar nan na tsaneta kamar yanda na tsani Zaki" tashi Dmash ya yi yana kallonsa ya ce"wannan ba hujja bace karka sake irin haka" murmushi Taj ya yi ya ce"idan kuma nasake fa?" da mamaki duk suke kallonsa Petor ya ce"Taj kaji abinda ka faɗa kuwa" kallonsu ya yi sai kuma ya dafe kansa ya ce"oh I'm sorry sir I thought da Zaki nake magana" okay sukace daidai lokacin suka fara jiyo ƙarar harbi da mamaki duk suke kallon ƙofa Dmash ya ce"what happened?" girgiza kai Taj ya yi alamar bai sani ba turo ƙofar da aka yi ne ya sanya suka kallo ƙofar da sauri sanye yake cikin wasu uniform na sojoji wanda sukayi matuƙar yi masa kyau baki buɗe duk suke kallonsa da sauri su Tyha suka sara masa irin yanda akewa babba idan anganshi da sauri Dmash ya kalli su Petor wanda yaga sunyi the Same irin abinda su Tyha sukai ciki harda Taj takowa ya yi cikin parlon yana taku na isa da taƙama hannayensa zube cikin aljihun kayan jikinsa baki na rawa Dmash ya ce"hii...hy..you" murmushi Zaki ya yi ya ce"kayi mamakine?, ai banyin tunanin zakayi mamaki ba Sir Fahad Dmash nayi zaton ai kanada dakakkiyar zuciya" girgiza kai Dmash ya yi ya ce"ya akayi ban ankara da wuri ba?, meyasa na yarda dakai Zaki?" ɗaga kafaɗa Zaki ya yi ya ce"call my real name" kallon tag ɗin jikin rigarsa ya yi sai kuma ya ce"General Aliyu Ahmad Aliyu" "Yes it's my name ka ɗauka duk tsawon lokacin dana bata tare dakai sbd ina son harƙalla dakai ne?, koda wasa baka taɓa burgeni ba gabaɗaya na tsaneka ina rayuwa dakai ne kawai sbd hakan ya zame mini dole ka gagari mutane dayawa an turo sojoji babu adadi amma ƙarshe saidai su rasa rayuwarsu a banza sbd haka nayi alƙawarin na daina aiken kowa da kaina zanyi maganin abun. A duk sanda muka haɗu dakai ina jin kamar na fasa kwanyar kanka a wannan lokacin saidai wata zuciyar ta hanani ban shigo rayuwarka ba saida nagama sanin komai naka a tunaninka kai ne ka jawoni cikin rayuwarka amma kayi kuskure dan ni ne wanda na jawoka cikin tawa rayuwar kuma yanzu zan miƙa ka ga hukuma" wata dariya Dmash ya yi sannan ya ce"haba kai ma kayi irin wannan dabarar ballantana ni" yana faɗin hakan ya ɗora bindiga kan Muhaira yana shaƙeta ya ce"ko ku rabu dani ko kuma na harbeta" murmushi Zaki ya yi yana tsaye inda yake ya ce"taya zaka yi harbi bayan babu komai a cikin bindigar?" kallon gun din Dmash ya yi shidai yasan ya zuba bullet a ciki amma ya kasa yarda da abinda Zakin ke faɗa masa cikin zafin nama Zaki ya ƙarasa gabansa ya finciketa yana buga masa kan gun aka riƙe kansa ya yi yay baya zai faɗi Taj ya tareshi yana murmushi ya ce"haba sir naga zaka fadi har kayi give up?" girgiza kai Dmash ya yi daidai lokacin yaransa suka shigo parlon without second thought kuma suka fara buɗe wuta hannun Taj Zaki ya kama ya danƙa masa Muhaira ya ce"go" girgiza kai Taj ya yi ya ce"mu bar ka anan sir?" gyaɗa masa kai ya yi Taj ya ce"no sir I can't" "Taj!! ba shawara nake baka ba" sara masa ya yi sannan yaja hannun Muhaira suka fita daga parlon. Duk yawancinsu saida Zaki ya harbesu duk ba baya harbin inda mutum zai mutu dan a raye suke buƙatarsu yana yi Petor na tayashi saida suka rage sai su biyu sannan suka tsaya taɓa shi Petor ya yi ya joyu ya ce"Sir ka tuna?" girgiza kai Zaki ya yi ya ce"sanda ka kashe Smallo he's my brother sbd shi na shiga hukumar sojoji kawai dan na ɗaukar masa fansa" buɗe baki Zaki ya yi zai magana ji kake tassssss ƙarar shigar bindigar cikin ƙirjinsa da gudu Taj suka ƙaraso da wasu tarin sojojin garin Saudiyya Petor na ganin haka ya dasa gun din akansa ya kashe kansa zubewa Muhaira tayi awajen tana zunduma ihu ta shiga jijjiga Zaki wanda yake kwance baya ko numfashi sai jini ne yake zuba a ƙirjinsa rungumeshi tayi tana kuka kamar ranta zai fita take kiran"Papi!! Papina ka tashi ka tashi dan Allah kaima tafiya zaka yi ka barni?? kaima su Dada zaka bi?? Papi wake up ka tashiiiii don't leave me alone please Papinaaaa!" ko alamar motsi Zaki bai yiba har sannan kuma banda jini babu abinda ke gudu a jikinsa gaba ɗaya ta bata jikinta da jininsa da sauri Taj ya zo ya janyeta yana girgiza mata kai cikin kuka ta ce"hamma Taj ka cewa Papi ya tashi ya tashi mu gudu" shiru Taj ya yi mata dan bashida amsar bata koda ace shi ba likita bane zai iya faɗa cewa kai tsaye Zaki ya tafi domin duba da inda aka yi masa harbin balle kuma shi da yake likita wasu zafafan hawayene suka shiga sakkowa kan fuskarsa tabbas ya yi rashin aboki domin Zaki abokinsa ne tun na yarinta. Kallonsa Muhaira tayi daidai lokacin da wasu likitoci suke ɗauke Zaki daga wajen da idanu Taj ya yi masa magana ya girgiza masa kai alamar he's gone juyowa ya yi zai yiwa Muhaira magana yaga ta sulale ƙasa nan ta faɗi ƙasa sumammiya.

*Nmandi azikewe Airport*
Chapter 28 · 0% Book details