← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 29

Sashe 10

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsayawa ya yi na wasu seconds sannan ya taka har gabansu kallonsu ya yi duka sannan ya ƙarasa wajen Taj wanda ya cukwuikuyeta ya riƙe gam yana zuwa ya sanya tattausan hannunsa ya karɓeta hannun Taj wani wahalallen numfashi Taj ya sauke yana dafe ƙirjinsa zullo ta shiga yi a hannun Zaki hakan yasa ya yi wani murmushi sannan ya ɗauketa cak a kafaɗa ya shige ciki, bin bayansa Taj ya yi har sannan bai gama dawowa daidai ba ya shiga parlon bai ga Zaki a parlon ba hakan yasa ya nemi waje ɗaya ya zauna yana sakin wani Irin numfashi. Ganin da gaske aljanun kanta suke kuma koda wasa sunƙi magana yasa ya danneta akan gadon yana kallon fuskarta wacce tayi wani irin jaa girgiza kansa ya yi sannan ya ɗora hannunsa kan goshinta ya shiga murzawa da sauri ta saki wata irin ƙara cikin sautin kuka kuma ta ce"mu ka rabu damuuu ina ruwanka ka sakemu" taɓe baki ya yi cikin cool voice ya ce"bazan rabu daku ɗin ba me kuke a wajenta?" "batada kowa batada gata ta rasa duk wani farin cikinta tun ranar da tazo duniya babu wanda ya damu da ita rayuwarta cike take da ƙalubale dolene mu kula da ita mune kaɗai gatan ta ka rabu damu muyi aikin gabanmu kar kace zaka shiga tamm" yanda ta wani taune lips ɗinta wanda duk suka gama jiƙewa ya yawo sai ta bashi tausayi, ƙara yunƙurawa ta yi zata miƙe ya sanya hannunsa ya tokareta a hankali take sakin wani numfashi shiru ya yi na wasu mintuna sai kuma ya ce"uhnnn ku bar jikinta" tsaki ta yi ta ce"kai ne zamu ce ka rabu da ita amma mu babu wanda ya isa ya rabamu da ita" haɗe ransa ya yi ya ce"ohk rashin kunya zaku yimin?" girgiza kai tayi tana taɓe baki gyara kwanciyarsa ya yi ya sakar mata dukkan nauyinsa sannan ya kamo fuskarta a tafin hannunsa, cikin wata kamilalliyar murya ya shiga rera karatun Alkur'ani inda yake karanta suratul jinn kuka Muhaira ta sanya kuma duk abinda ake koda wasa bata buɗe idanunta ba cikin wata iriyar murya mai nuna fita hankali ta ce"kayi haƙuri wayyoooo zamu tafi kabari dan Allah zaka kashemuuuu!" ko saurarenta bai yi ba ya cigaba da karatunsa saida yakai inda ya yi niyyar sannan ya ɗago yana kallon fuskarta cikin sanyin murya ya ce"now leave her" cikin ƙaraji ta ce"wlh mun tafi amma zamu dawo kasa wannan a ranka" taɓe baki ya yi yana dungure mata kai ya ce"karku fasa dawowa nima bazan fasa ƙonaku ba" turo masa baki gaba tayi sannan ta ce"mun tafi muu" harararta ya yi ya ce"Allah ya raka taki gona" wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta sake rufe idanunta a hankali shima yake sauke numfashi dan ya daɗe rabonda ya yi magana mai tsawon wannan tashi ya yi daga jikinta wanda ba daban aljanu ba da tuni ya illata ta bai sake saurarenta ba ya juya ya shige toilet dan watsa ruwa harga Allah ƙamshin turaren yarinyar bai masa ba duk da yasan ba wani ne ya sanya mata ba sai Taj.

Fitowa ya yi daga wanka yana sanye cikin wata bathrobe ƙirjinsa a buɗe wani lafiyayyen gashi ne kwance a kansa tudun nononsa Kamar na mace saboda cika nipples ɗin kuma jajaye dasu, six pack ɗinsa ya fito raɗau ko ba'a faɗa maka ba kasance ba ƙaramin gym yake ba dan ko ɗan wristling albarka, bedroom slippers kawai ya saka ya juya ya fita gashin kansa na ɗigar ruwa kamar na Mace, cikin isa yake taka stairs ɗin benen wanda hakan ya sanya Taj juyowa kallonsa ya yi sai kuma ya ɗauke kai a hankali Zaki ya ƙarasa sakkowa sannan ya zauna kujerar dake facing tasa taɓe baki ya yi ganin yanda ya ajiye uban Cake a gabansa yana faman ci girgiza kai ya yi sai kuma ya ce"kwaɗayayye kawai" dariya Taj ya yi yana kai wani slice na chocolate cake bakinsa ya ce"naji ɗin" saida ya cinye tass sannan ya ɗauki water bottle ya sha ruwan ya ajiye yana gyatsa ya ce"Alhamdulillah" sai a sannan ya kalli Zaki ya ce"wlh yarinyar nan aljanu take" "wace yarinya??" harga Allah Zaki ya tambaya dan kwata-kwata ya manta da wata yarinya, harararsa Taj ya yi ya ce"banson rainin hankali ya kuka ƙare da aljanun" sai a sannan ya tuna ya taɓe baki yana faɗin"inada abinda yafi wannan yanzu ya kunyi magana da manager?" gyaɗa masa kai ya yi ya ce"Eh munyi an kammala komai, sannan akwai wasu yara guda biyu da Abrar ya yimin maganarsu zuwa anjima zanje naga idan zasu yi daman akwai wani wanda ya ce min yana son guda biyu idan naga sunyi sai kawai na miƙa masa" jinjina kai Zaki ya yi sannan ya ce"then we should talk later I'm so excited" miƙewa ya yi yana murmushi ya ce" a wuta lpy" sannan ya yi waje, da kallo Zaki ya bisa sannan ya tashi ya haye sama da ɗan sauri.

Kai tsaye Taj ɓangaren su Tyha ya nufa yana zuwa ya samesu suna cin abinci da hannu ya yi mata alama da tazo ta tashi tana ɗaukan veil ɗinta sannan tabi bayansa kai tsaye kuma motarsa kirar Bugatti suka shiga ya bar gidan.

Bayin Allah nagaji 😤😂.

# *BA ITA BA CE*
# *ZAKI*
# *MUHAIRA*
# *TAJ*
# *TYHA*
# *RIYADH*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!*
[8/5, 8:58 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖*

*Ameenatou I Ibrahim*
*Nanameera*.

*nanameera08@arewabooks*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

```Page 07```

Sheshsheƙar kukanta yaji sanda ya shiga cikin bedroom ɗin, zaune take ta haɗe jikinta waje guda ta tura kanta cikin cinyoyinta gashin kanta duk ya wargaje taɓe baki ya yi sannan ya ƙarasa gaban bed ɗin alamun shigowar mutum da taji ya sanya ta ɗago dara-daran idanuwanta wanda suka jiƙe da hawaye ta kalleshi, shima ita yake kallo kwarjinin nasa idanun ya sanya ta sunkuyar da nata sai kuma ta cigaba da rera kukanta Zaki bai sake saurarenta ba ya taɓe baki sannan ya juya ya fice daga ɗakin zaunawa ya yi nan parlon shi kaɗai yake yin tsaki da dukkan alamu Taj ya haɗashi da wahala, mikewa ya yi ya buɗe wani haɗaɗɗiyar Freezer ya ɗauko Apple guda biyu da dabinon ajuwa ya dawo ya zauna lumshe idanunsa ya yi saboda wani zaƙin zuma dana dabinon da suka dakeshi yana matuƙar son abu mai zaƙi a rayuwarsa that's why koda yaushe baya rasa cake, dabino da chocolate a fridge saida ya ci kusan guda goma sannan ya rufe robar water bottle ya ɗauka ya ɓalle murfin ya farasha sanyin ruwan ne ya sanya ya yi saurin ajiyewa dan lokaci ɗaya ƙirjinsa ya riƙe bandama rashin jin magana irinta Zaki da bazai sha ruwan sanyi ba, idanun da yaji yana yawo akansa yasa ya juya two eyes sukayi dashi ta ɗauke kanta tana turo baki ɗauke kansa ya yi shima ya cigaba da cin Cake ɗin gabansa wani takaici ne ya turnuƙe Muhaira kasancewar har sannan aljanun basu gama sakinta ba. Saida ya gama cin abubuwan daya ɗebo sannan ya miƙe ko kallonta bai yiba ya shige bedroom ɗin ya rufe ƙofar da kallo kawai Muhaira ta bisa haka kawai taji batasan ganinsa ko meyasa ohho??, tafiya tayi ta zauna ƙasan carpet ɗin parlon mai wani irin laushi kamar mage hannayenta ta ɗora kan carpet ɗin tana taɓawa dan ita bata taɓa jin abu mai laushin wannan ba abu kamar buredi. Gajiya tayi da zaman wajen hakan yasa ta kwanta nan ƙasa not too long kuma bacci ya ɗauketa dan a matuƙar gajiye take.

A hankali ya buɗe idanunsa, da sauri ya tashi zaune yana kallon agogon dake gefensa babu kaya jikinsa daga shi sai wando Three-quater milk colour da alama tunda ya yi wanka bai saka kayan ba, ɗan siririn tsaki yaja sannan ya miƙe ya shige toilet ruwa kawai ya watsa ya fito yana ɗiga dryer ya ɗauka ya tsane kansa sannan ya sanya wani ribbon baƙi ya ɗauresa har kan gadon bayansa ya sauka dan gashinsa ko wata macen albarka wata V-neck t-shirt ya sanya coffee colour sai wandonta wanda ya kasance gajere shima coffee yarin diamond ya sanya a kunnensa ɗaya sannan ya fito, ƙamshin turaren Aventus Eau de perfume spray ne ya daki hancinta tana zaune gefen kujera sai baza idanu take idanunta sun faɗa sosai ko ba'a faɗa maka ba kasan yunwa takeji tsayawa ya yi a parlon yana gyara zaman farin Bluetooth ɗin kunnensa da kallo Muhaira ta bishi tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin mutum mai kyawun Zaki ba ga iya kwalliya kamar ɗawisu

"Keeee!"
Chapter 10 · 0% Book details