Sashe 1
Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[7/30, 10:00 PM] NanameeraðŸ˜âœŒðŸ»: https://chat.whatsapp.com/LVwoOVW31kC9r0d7QRPZhP
*BA ITA BA CE..💖💖💖*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
*Follow my account both arewabooks nd Wattpad.*
*nanameera08*_arewabooks_.
*@Nanameera08* _wattpad_.
*Nanameera*
# *SQUAD 2024*.
```PAGE 01```
*بسم لله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…*
Wata iriyar tsawa mai firgitar da zuƙata aka yi wacce tayi daidai da sanda jaririyar data haifa ta tsala wani irin ihuu mai cika kunnuwa, ruwane ake yinsa bana wasa ba ruwan da duk wani mai hankali zai dinga jin tsoron zubarsa an daɗe sosai ba iya makamancin irin wannan ruwan ba cikin garin Damaturu, duhu ne mamaye da bukkar da suke ciki domin fitilar kwan gab take da mutuwa dan ko haskenta ba'a gani sai ɗan kyalli wanda shine zai tabbatar maka da cewa an kunna fitilar. Shirun da jaririyar ta yi ya yi daidai da ɗaukewar ruwan tamkar ba'a taɓa yinsa ba a hankali matashiyar matar take sauke wani wahalallen numfashi wanda take jansa dakyar, tsuroo magidancin mutumin ya zuba idanunsa yana kallon abinda matar tasa ta haifa sosai kuma ya yi mamakin yin shirun jaririyar. Above 20mins suna cikin wannan halin har sannan kuma babu wanda ya furta wata kalma a cikinsu, dakyar matar ta yunƙura dan ganin halin da abinda ta haifa yake ciki daidai lokacin da zuciyarta tayi wata irin kyakkyawar buguwa dalilin ganin ɗiyar tata da tayi yashe a gefenta ko ba'a faɗa mata tasan itama tabi sauran ƴan uwanta, runtse jajayen idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka shiga zirarowa kan kuncinta tabbas taji babu daɗi kamar yanda ta saba jin babu daɗi ce eh.' a duk sanda ta haifa ɗa ko ƴa kuma ya mutu amma ya zatayi? tata ƙaddarar kenan jiki asanyaye ta janye gawar jaririyar bayan ta yanke cibiyar sannan ta ɗorata akan ƙirjinta bayan tsayin watanni data ɗauko tana ɗawainiya da cikin tasha wahala kamar yanda ta saba sha kowane lokaci sai gashi yanzu ma Allah ya karɓi abarsa. Miƙewa magidancin ya yi ya ɗauki wata ƙwarya wacce ke can gefe guda ya yi waje... Wani irin sanyin ake mai tsara ƙofofin jiki yayinda har sannan yayyafin bai gama zuba ba yanayin da ya yi wani irin daɗi banda ƙamshin ƙasa babu abinda ke tashi sai kuma kukan kwaɗi wanda ya samo asali dalilin taruwar ruwa a wajejen, daga can wani gefe inda ruwa ya taru yanayin wajen kamar pond ya ƙarasa yana tafiya a hankali. Tsugunawa ya yi sannan ya kafa kan tulun yana tarar ruwan da yake zuba a hankali yake sauke ajiyar zuciya wacce take nuni da halin da zuciyarsa take ciki saidai tsananin tsoron Allahnsa da kuma yarda da ƙaddara ya hanashi fallasa asirin zuciyarsa. Tamkar wanda aka tsikara haka ya juya gefensa daga can gefe guda ya hango wani farin abu mai ɗan faɗi kai tsaye bazai iya cewa ga abinda yake ciki ba. Ɗauke idanunsa ya yi daga wajen yana ambaton sunan Allah ya miƙe tsaye bayan ya gama ɗiban ruwan ya ɗora bisa kafaɗarsa. Gaba ya yi batareda ya sake kallon inda yaga wannan farin kyallen ba, da sauri yaja ya tsaya saboda wata irin bugawa da zuciyarsa ta yi a hankali kuma ya juyo yana kallon bakin pond ɗin tamkar wanda mayen ƙarfe ke jansa haka ya samu kansa da komawa wajen sosai sanyin asubar yake shigarsa wanda ya haifar masa da wani irin masassara mai kamada zazzaɓi, sake tsugunawa ya yi a karo na biyu amma wannan karon ya tsuguna ne gaban wannan farin yadin sosai ƙirjinsa ke dukan uku uku yayinda wata matsananciyar fargaba ta ziyarceshi a nutse bakinsa ɗauke da sunan Allah ya ɗora hannunsa kan yadin amma ga mamakinsa sai yaji wani irin laushi wanda bai taɓa jinsa a jikin wani nau'i na tufafi ba tamkar auduga saidai kuma yanada wani irin gashi a jikinsa kamar na jikin mage hannunsa na wata iriyar kakkarwa ya buɗe yadin wanda kai tsaye za'a iya kiransa da bargo ya subhanallahi!! da sauri ya yi baya sakamakon abinda ya yi arba dashi cikin wannan bargon cikin ransa yake furta duk wani sunan Allah da yazo bakinsa kuma iyaka iyawarsa kusan 2mins yana wannan halin kafin kuma ya yi ta maza saboda wata jarumta da yaji ta zo masa a hankali ya saka hannayensa duk biyun ya ɗauki bargon sannan ya miƙe tsaye kasancewarsa mutum mai cikar zati ya sanya ya ɗauki tulun da ɗaya hannunsa sannan ya cigaba da tafiya dan komawa inda ya fito.
Yanda ya bar matar haka yazo ya tarar da ita har sannan kuma jaririyar tana kwancen bisa ƙirjinta tayi nisa cikin duniyar tunani dan kwata-kwata batasan ya shigo cikin bukkar ba lura da hakan ya sanya bai kulata ba ya ƙarasa can gefen tabarmar kabar ya shimfiɗar da halittar dake cikin bargon domin idan har ya ce yasan mene a ciki ya yi ƙarya ganin yanda bargon yake a jiƙe ya sanya ya yi saurin yaye shi daga cikinsa ya ilahy wani irin daddaɗan ƙamshi ne ya ratsa cikin hancinsa wanda lokaci ɗaya ya cika cikin ƴar ƙaramar bukkar tasu jinjina kansa ya yi cikeda al'ajab ya miƙe yana ƙarasawa wajen matar tasa dukda duhun dake bukkar hakan bai hanashi ganin kyallin hawayen dake fuskarta ba numfasawa ya yi sannan ya sanya hannayensa ya karɓi jaririyar hannunta sannan ya miƙe ya fice daga bukkar sai a sannan ta saki wani raunataccen kuka mai tafiya da imanin duk wani mai saurare kuka ne mai fitowa tun daga ƙawon zuciyarta kuka ne mai nuni da tsananin baƙin cikin da take ciki kanta ta matse tsakanin cinyoyinta ta cigaba da rera kukanta.
Misalin ƙarfe 5:10am ya dawo cikin bukkar lokacin haske ya ɗan fara shigowa cikin bukkar da sauri ya ƙarasa wajen da ya yi ajjiya dan a wannan lokacin ji ya yi yana buƙatar mene ne shigowarsa ya yi daidai da ɗagowar matar a hankali kuma take binsa da idanunta wanda suka sauya launi daga fari zuwa jaa hannayensa ya sanya ya ɗaga halittar daidai nan kuma ta ƙaraso gabansa da wani irin sauri kallonsa take sai kuma ta kalli abinda ke hannunsa jaririyace mace kuma sannan kana ganinta kasan ɗanyen jego ce domin ba zata taɓa shige kwana ɗaya da haihuwa ba, da sauri ta karɓe yarinyar tana zuba mata idanu fara ce irin tass ɗin irin farin da ba'a fiye samun ƴaƴan hausawa dashi ba duk da kasancewarta jaririya hakan bai ɓoye asalin kyawun fuskarta ba idanunta a rufe suke yayinda gashin idanun ya kasance ya sakko har ya zo wajen kan gefen idanunta hannayenta a dunƙule suke kamar na kowace jaririya wacce take sabuwar haihuwa danshin da taji a jikinta da kuma lura da tayi kamar bata numfashi ya sanya ta yi saurin rungumeta kasancewar babu ko wando jikinta da sauri kuma ta kalli mijin nata a karo farkon bayan haihuwar tata ta ce
"Ki kira sarkin ruwa yaya Gani"
Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana tafiya da ɗan sassarfa ya fice daga bukkar, sake ƙanƙameta ta yi tana sauke ajiyar zuciya a hankali kuma wasu sabbin hawayen suka ziyarci kuncinta saidai wannan karan na zallar farin ciki ne duk da har sannan batasan daga inda mijin nata ya samo jaririya kuma ta tabbatar da cewa ba wacce ta haifa ba ce ba.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taji yarinya ta tsala ihu batasan lokacin da hawaye suke fara fitowa daga cikin idanunta ba sosai tayi murna dunƙule hannayenta ta yi wanda ke nuni da zallar farin cikin da take ciki miƙa masa yarinya Sarkin ruwa ya yi sannan cikin sakin murya ya ce"ina maka fatan Alkhairi Ya Gani Allah ya yara maka ita" tattausan murmushi ya yi sannan ya furta cikin kami'lalliyar muryarsa "Ameen ya rabbil alameen" fita Sarkin ruwa ya yi ita kuma ta ƙaraso da sauri tana duban kyakkyawar jaririya ta ce"Ya Gani ki bani shi" sai a sannan nagane ba bahaushiya ba ce domin asalin muryata ta Fulani ta bayyana cikin kalaminta koda yake daman da zarar kayi ido biyu da ita fuskarta taza shaida baka hakan kasancewarta kyakkyawar bafulatana sanye take da wasu kayan Fulani irin blue colour ɗin nan sai murjani wanda ta rataya a wuyanta, murmushi ya yi kawai sannan ya miƙa mata ita da sauri ta rungumeta a ƙirjinta tamkar wani ya ce zai kwace ta cikin kurɓattaciyar hausarta ta ce" wacece shi?, ko ɗiyata ne ya tashi?" gyara zamansa ya yi kan tabarmar kabar sannan ya kalleta a nutse kuma ya furta "*BA ITA BA CE ba!!*" sake kallon fuskarta ta yi ganin yanda take barcinta yasa ta kalleshi da ƴar damuwa a fuskarta ta ce" to waye shi?, kuma ina ka same shi?" Numfasawa ya yi sannan ya kama hannunta cikin sanyin murya ya labarta mata duk abinda ya faru, ya ce"saboda haka na yanke shawarar zamu kula da ita daga nan har ƙarshen rayuwarmu zamu riƙeta matsayin ɗiyarmu wacce ta mutu, tabbas na tabbata akwai wani ɓoyayyen al'amari a tareda wannan yarinyar wanda lokaci ne kawai zai tabbatar mana da hakan" yanayin yanda yake magana zaka gane cewa ba yare ɗaya suke dashi ba domin shi yana magana ne irin yanda mutanen garin ke magana musamman ma Kanuri wanda hakan ya tabbatar da cewa shi ɗin ya kasance Kanuri ne. Cikin sanyin murya itama ta ce" karki damu Ya Gani zan kula da ita kamar ɗiyata dana rasa nima naji ina sonshi sosai kuma ma yana kama dani kin gani" murmushi ya yi ganin da gaske nuna masa take ya gani jaririyar na kama da ita ya girgiza kansa sannan ya miƙe ya fice daga bukkar yayinda ita kuma ta ɗago fuskar yarinyar tana kallonta kallon da yake nuna irin ƙaunar da take mata ita kaɗai kuma take sakin wani yalwataccen murmushi haka har bacci ɓarawo ya saceta.
*BA ITA BA CE...💖💖*
*#Human trafficking*
*#heart touching*
*#destiny*
*#Loyalty*
*#pity*
# *SQUAD 2024*.
*Comments nd like*.
[7/31, 3:29 PM] NanameeraðŸ˜âœŒðŸ»: *BA ITA BA CE!...💖💖*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
*Follow my account both arewabooks nd Wattpad*
*nanameera 08* _arewabooks_
*@Nanameera08* _wattpad_.
*Nanameera*
# *SQUAD 2024*.
```Page 02```
*Rugar Jama'are*