Sashe 19
Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Numfasawa ne ya kusa ɗaukewa saboda jin abu da tayi agabanta cikin tsananin tashin hankali ta buɗe baki zaka kwalla ƙara, da sauri ya toshe mata baki yana yi mata alama da tayi shiru, kusan five minutes kafin ya ɗago ya kalleta da idanuwansa da suka sauya kala cikin wata iriyar murya ya ce" Ma'eesha! da sauri ta kalleshi dukda ba ganin fusakarsa take yi ba ya ce"naji I'm sorry amma bazan sake ba bazan sake yi miki abinda nayi yanzu ba dan Allah forgive me my lil sis" da sauri ta faɗa jikinsa tana kuka mara sauti, murmushi Farooq ya yi sannan ya dafa kanta ya ce"Nagode sosai ƴar albarka dare ya yi shige ki kwanta" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta juya ta haye sama ta barshi nan tsaye yana saƙa da warwara.
*RIYADH*
*Al Yesmin international school*
Fitowa tayi daga cikin makaranta tana kallon yanda ake ta zuwa ɗaukan yara gaba ɗaya a gajiye take ga wani irin ciwo da ƙirjinta ke mata tura baki tayi ganin har sannan ita babu wanda ya zo ɗaukanta waje ta nema ta zauna ta miƙe ƙafarta saboda wani irin ciwo da take mata tun daga nesa yake kallonta ganin yanda duk ta kwaɓe fuska kaɗan ya rage bata fashe da kuka ba, fitowa ya yi daga motar yana sanye cikin Jallabiya Black colour idanunsa maƙale cikin sun glasses kasancewar akwai rana a garin kwata-kwata Muhaira bata lura dashi ba har ya ƙaraso gabanta girgiza kansa ya yi sannan ya ja kunnenta da sauri ta ɗago tana kallonsa sai kuma ta fashe da kuka bai ce mata komai ba ya kama hannunta suka bar wajen saida ya sanyata a motar sannan ya kalleta ganin yanda take kuka kamar wacce aka yiwa wani abu ya ce"za ki yimin shiru ko sai ranki ya ɓaci?, sbd ke kike da bakin kuka duk abinda aka yi miki sai ki fashe da kuka?" tura masa baki ta yi tana shashshekar kuka. Siririn tsaki yaja sannan ya ja motar suka bar wajen, a bakin ƙaton gate ɗin gidan ya yi parking ba tareda ya kalleta ba ya ce"sauka" kallonsa ta yi sai kuma ta buɗe motar ta fita shi kuma ya bar wajen kallonta suke har ta shigo gidan suna zaune kan wata kujera suna hira shigewa ta zo yi Tyha ta ce"keee zo nan" juyowa Muhaira ta yi ta kalleta sai kuma ta tura ƙofar ta shige batareda ta amsa kiran da tayi mata ba baki buɗe Tyha ta bita da kallo sai kuma ta yi kwafa ta ce"wai wannan wace ce?" ɗaga kafaɗa Amrish ta yi ta ce"nima nasani maybe dai itama siyanta akai ko kuma aka satota" Zeey ce ta ce"kenan ita ba a cikinmu take ba naga tana kwana part ɗin Zaki?" Tyha ta ce"tunda kikaga haka ko Zaki ɗin ne ya riƙeta maybe dan ya ganta da kyau ne kuma daga gani yarinyace sosai" murmushi Amrish ta yi ta ce"aikuwa amma duk da haka yarinyar batada kunya" numfasawa Tyha ta yi ta ce"aikuwa zan yi maganinta saidai idan ba zata fito ba" tsaki Zeey ta yi ta ce"ke daɗina dake rashin tunani to da gani kike tana fitowar?, yau ɗin ma bakiga school taje ba" wani kallo Tyha ta yi mata ta ce"dalla Malama karki sake cemin mara tunani zan miki rashin mutunci wlh" ganin abin nasu na neman zama faɗa yasa Amrish ta ce"dan Allah ku saurarawa mutane wannan ai ba daidai bane ku dinga abu kamar wasu yara" buɗe baki tayi zata yi magana sukaga Zaki ya shigo gidan da motarsa sunkuyar da kansu sukai har ya fito daga motar hannunsa riƙe da ledoji. Wani guard ya miƙawa ledojin sannan ya yi gaba, yana zuwa suka sunkuya cikeda girmamawa suka ce"sannu da zuwa yallaɓai" bai basu amsa ba ya yi gaba, har ya riƙe handle ɗin ƙofar sai kuma ya juyo yana tafiya hannunsa zube cikin aljihu ya ce" ina sauran?" Tyha ce ta ce"sunje school" "then ku mene ya hanaku zuwa?" kasa bashi amsa suka yi ya ce"idan ba zakuyi karatu ba kunfi son ɗaya rayuwar fine zanyi maganinku" yana faɗin haka ya juya ya shige parlon.
Dafe ƙirji Amrish ta yi ta ce"mun shiga uku wlh tun wuri musan abunyi nidai zan koma school gobe" Zeey ta ce"nima haka wlh dan nasan idan ya waiwayemu abun bazai yi da kyau ba" kallonsu Tyha ta yi sannan ta ce"sai abinda Taj ya ce min" tsaki Amrish tayi ta ce"banza kawai" tashi suka yi suka barta a wajen saida taga sunyi nisa sannan itama tabi bayansu. Da sauri ya ƙarasa inda take kwance ɗin idanunta har sun fara ƙaƙƙafewa ɗagota ya yi jikinsa yana kallon fuskarta ya jijjigata ya ce"keeee! keee!" ganin tana neman rasa rayuwarta gashi babu inhaler a gidan yasa ya zauna yana gyara zamanta akan cinyarta a hankali yayi coping face ɗinsu ya ɗora bakinsa daidai nata cikin nutsuwa ya zura bakinsa cikin nata sannan ya saki wani zazzafan numfashi da sauri ta riƙeshi tana sauke wani irin numfashi saida ya yi mata haka wajen sau uku sannan numfashin nata ya dawo zare bakinsa ya yi daga nata yana kallonta har sannan wasu hawayene suka shiga sakko mata na zallar azabar fitar numfashi, sosai ta bashi tausayi dan yasan azabar cutar numfashi dan har yanzu idan Asthmarsa ta tashi sai ya yi kamar ya rasa ransa. Saukar numfashinta ya ji a ƙirjinsa hakan yasa ya kalli fuskarta gani ya yi tayi bacci ya shafa kanta sannan ya miƙe da ita ya shiga bedroom ɗinta yana kwantar da ita ya juya tayi saurin riƙe masa hannu cikin wata iriyar murya ta ce"karka barmu ka zauna a nan tsoro muna ji" kallon fuskarta ya yi yaga ta kwaɓe fuska hakan yasa ya zauna gefen gadon ya zuba mata idanu yana kallonta wata iriyar ƙara ta saki sai kuma ta miƙe zaune tana sauka daga kan gadon da sauri cikin zafin nama ya riƙota ya haɗata da ƙirjinsa ya rufeta ruf yana jin yanda take ƙoƙarin guduwa ya sake rufeta yana haɗe face ɗinsu waje guda cikin wata iriyar murya mai amo tashiga furta" mu ka kyalemu tafiya zamuyi da ita ka rabu damu ka daina riƙemu" shiru ya yi yana sakin ajiyar zuciya ya ce"au kune?" sake yunƙurawa tayi ya yi saurin rungumeta yana sakin murmushi ya ce"meyasa zaku tafi da ita to?" ta ce"saboda ita ɗin amanarmu ce babanta ya barma amanarta kafin ya mutu sbd haka dole sai ta bimu ka rabu damu" haɗe ransa ya yi yana dungure mata kai ya ce"ƙarya kuke" "mu ba ƙarya muke ba munsan Allah ai" murmushi ya yi ya ce"au da gaske?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"shikenan muyi abu guda, naji ku tafi amma ku barmin amanarta ni zan riƙe muku nayi alƙawarin bazan bari wani abu ya cutar da ita ba" tura baki tayi gaba ta ce"kayi alƙawari?" gyaɗa kansa ya yi ta sake cewa"to amma bazaka bari kowa ya taɓa ta ba, duk randa wani abu ya sameta to ka karya alƙawarinmu kuma zamu zo mu tafi da ita" numfasawa ya yi ya ce"na yarda" murmushi ta yi tana miƙo masa hannunta ta ce"to kayi mana alƙawari" girgiza kansa ya yi sannan ya ɗora hannunsa akan nata, waya sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma jikinta ya saki kallon fuskarta ya yi sai kuma ya kalli hannunta wanda yake cikin nasa ya ɗauki ƴan mintuna a wajen kafin ya kwantar da ita ya rufa mata duvet ya fice daga ɗakin.
Kai tsaye kuma ɗakinsa ya shiga yana zuwa ya ajiye wayarsa sannan ya shige bathroom ya sakarwa kansa shower saida ruwan ya dakeshi sosai sannan ya dafe kansa wanda ya kejin ya yi masa nauyi tunani ne kala-kala cikin ransa lokaci ɗaya kuma ya tuna da maganar Dmash furzar da wani irin numfashi ya yi sai kuma ya yi tsaki kawai ya yi wankansa, fitowa ya yi cikin wata bathrobe fara dryer kawai ya saka a kansa saboda jiƙewar da ya yi sannan ya kwanta yana rufe jikinsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi. Sai wajen 6:20pm sannan ta farka daga baccin da sauri ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala sannan ta fito wata jallabiya ta sanya mai ƙaramin hannu ta gyara gashinta sama-sama dan ita a rayuwarta ta tsani a taɓa mata kanta ko da itace kuwa parlon ta fito saboda wata irin yunwa da take ji da sauri tayi hanyar kitchen, dube-dube ta shiga yi dan ganin ko zata samu abinci tura baki tayi ganin babu komai a kitchen ɗin kuma tsoron kunna gas take gudun kar abinda ya faru da ita ɗazu ya sake faruwa, fitowa tayi tana jan ƙafa da sauri ta ƙarasa wajen ledojin da tagani tana zuwa ta shiga buɗewa takeaway ne guda uku a ciki na farkon ta buɗe taga jallof rice ce wadda taji wadatattun kayan haɗi ƙamshinta ne bai yi mata ba hakan yasa ta buɗe ɗaya takeaway ɗin fried rice tagani a ciki tayi murmushin jin daɗi sannan ta ɗauko ɗayan ta buɗe taga gasasshiyar kaza da sauri ta ɗauko sannan ta dawo ƙasan carpet ɗin ta baje ta hau cin abincinta hankali kwance tass ta cinye shinkafar kazar kawai ta rage amma itama taci tafi rabi sannan ta ɗauka ta mayar ledar ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa tasha sannan ta koma ɗaya parlon tayi zamanta tana kallo.
Fitowa ya yi cikin wata t-shirt da 3quater kai tsaye wajen ledojin ya nufa saboda wata irin yunwa da yake ji buɗe ledar ya yi yaga empty takeaway a ciki da mamaki ya kalli take away ɗin sannan ya buɗe ɗayan jallof rice ya gani itama kuma da alama taci dan ba haka ya ajiye ba yana buɗe ɗayan yaga babu kazar sai ƴar kaɗan a fusace kamar zai yi kuka ya yi ɗaya parlon yana wuci da sauri ta ɗago kanta jin yanda ya buga ƙofar yana kallonta ransa a haɗe kamar hadari ya ce"
# *Unconditional love*
# *Destiny*
# *SQUAD 2024*
# *BA ITA BA CE!*
# *Ameenatou I Ibrahim*
# *Nanameera ce!âœï¸*.
[8/10, 11:19 AM] NanameeraðŸ˜âœŒðŸ»: *BA ITA BA CE!..💖💖*
*Nanameera ce âœï¸*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 13```
# *DESTINY*