← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shafa kanta Mommy ta yi ta ce"ki daina wannan kukan ke wai wace irin shashasha ce nafada miki shida zaman aure da ita saidai a lahira amma anan dai duniya ya yi kaɗan bai isa ba sbd haka ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa" cikin kuka ta ce"haba Mommy kullum haka kike cewa amma gashi har yau sauran kwana 6 ɗaurin auren banga ana niyyar fasawa ba ni wlh bazan iya sharing miji da wata ba watar ma kuma kurma wacce koda naci mutuncinta ba jina zatayi ba dan Allah Mommy ki taimaka minnnn!" ɗago fuskarta Mommy tayi ta ce"kawo kunnenki na faɗa miki wani abu" miƙa mata kunnen tayi ta raɗa mata da sauri ta kalli Mommy tana murmushi ta ce"dan Allah Mommy da gaske kike?" gyaɗa mata kai Mommy tayi ta rungumeta tana dariya ta ce"kaiiiii amma naji daɗi sosai Mommy" da sauri Khalil ya saki handle ɗin ƙofar gaba ɗayansa ya jike da gumi kana kallon fuskarsa kasan hankalinsa a tashe yake

"Khalil lafiya?"

Da sauri suka kalli ƙofar sai kuma suka miƙe tsaye dafe ƙirjinta ta yi ta ce"mun shiga uku Mommy badai sunji ba?" shiru Mommy tayi tana kallon bakin ƙofar murɗa handle ɗin akayi suka shigo suna kallonsu duka His Excellency ne ya ce"

_Free pages sun kusa ƙarewa ƴar uwa only 4 pages remain isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan adamu Opay digital service evidence via 08106608363 or 07041901078 ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali akwai special group posting sau biyu a rana with is 1k only karku manta zaku iya fara payment yanzu ƙofa a buɗe take🥳🥳_

_Bamu fara komai ba cikin littafin BA ITA BA CE akwai abubuwan da karantawa kaÉ—ai zai iya fahimtar dakai karku bari a baku labari_

# *BA ITA BA CE*
# *Destiny*
# *Unconditional love*
# *Power*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce ✍️!*.
[8/12, 9:18 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!...💖💖*

*Nanameera ce ✍️*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

```Page 17&18```

"Lafiya na ganku tsaye?" wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke sannan Mommy ta yi murmushi ta ce"daman fita zanyi sai naji an turo ƙofar" kallonta Khalil ya yi sai kuma ya kalli Ramlah wacce take ta binsu da ido ya ce"ki shirya zamuje asibiti" gyaɗa masa kai tayi sannan ya juya ya fita his Excellency ma yabi bayansa dafe ƙirji Mommy ta yi ta ce"Allah nagode maka" numfasawa Ramlah ta yi ta ce"bari naje Mommy" okay ta ce mata sannan ta buɗe ƙofar ta fita ita kuma ta nemi waje nan ta zauna tana tunane-tunane. Kwance ta tarar dashi kan bed ya rufe idanunsa ƙarasawa tayi ta zauna gefen gadon a hankali ta ce"doctor gani" shiru Khalil ya yi mata kuma ba bacci yake ba saida ta maimaita sau uku sannan ya tashi zaune yana kallonta da idanuwansa wanda sukayi ja da Mamaki ta ce"bakada lpy ne?" girgiza mata kai kawai ya yi sannan ya tashi ya shige toilet taɓe baki ta yi sai kuma ta tashi ta fita dan daman bata gama abinda take ba, fitowa ya yi cikin wani yadi maroon colour mai shara-shara ɗinkin jamfa da wando ya ɗora hula zanna akansa fuskarsa maƙale cikin glasses kamar koda yaushe gaba ya yi tana ganin haka tabi bayansa zaune ta sameshi a motar yana danna wayarsa gidan gaba ta buɗe ta shiga sannan ya ajiye wayar yaja motar suka bar gidan. Murmushi Aleemah ta yi ta ce"wlh kuwa Mami nifa na ƙagu ayi auren nan nasan ma gobe ko jibi su Fulani zasu zo" Mami da take tajewa Ma'eesha kanta ta yi murmushi ta ce"ke kam Allah ya shiryaki Aleema in banda abinki ai auren nufine na Allah kuma naga Zahrah ba wani shekaru ne da ita ba, abun da kamar wuya Fulani tazo kinsan dai halinta" taɓe baki Aleemah ta yi ta ce"wlh Mami ita take jawowa kanta bakiga yanda take wulaƙanta samari ba duk kuɗin mutum idan ya ce yana sonta sai ta nemi ta ci masa mutunci kowa ya kasa gane kanta kuma taƙi ta faɗi wanda take so" girgiza kai Mami ta yi ta ce"Allah sarki to Allah ya shiryata maybe Gani take basu yi mata ba ko kuma akwai wanda takeso amma idan ba haka ba ai Zahrah tanada hankali kuma tasan me take" murmushi Aleemah ta yi ta ce"ai ni wlh kullum addu'a nake mata insha Allah sai ta rasa wanda zata aura tunda ita ruwan ido ta tsaya" girgiza mata kai Mami ta yi ta ce"ba'a faɗar haka ki dinga yi mata addu'a tagari" turo baki gaba ta yi batace komai ba har Mami ta kammala abinda take tashi tayi ta kalli Ma'eesha wacce tayi tsuru ta ce" taso muje kici abinci zamuje unguwa" maƙale kafaɗa ta yi alamar bazata jeba tunda ta tashi daman babu wanda ta kula hatta General daya shigo dubata bata kulasa ba, kamo hannunta Mami ta yi suka fice daga wajen sanin inda ta ita ne bazata tashin ba. Kallon Aleemah ya yi wacce take sanye cikin wata doguwar riga ta atampa me ɗan kama jiki kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai dan ita daman bata wani ƙaunarsa duk sanda tazo gidan batason abinda zai haɗata dashi har tayi gaba taji ya ce"Aleemah" tsayawa tayi amma bata juyo ba takowa ya yi cikin tafiyarsa ta isa ya tsaya a gabanta haɗe hannayenta tayi a ƙirji ta zuba masa idanu ɗan cute smile ya yi ya ce"ya kike?" "Lpy" cewar Aleemah numfasawa ya yi ya ce"daman inason magana dake idan babu damuwa please" ta ce"ina jinka" Farooq ya ce" mu ɗan zauna mana please" ɗaga kafaɗa tayi sannan ta zauna kan ɗaya daga kujerun da akayi ado dasu a garden ɗin zama ya yi shima yana facing ɗin ta ya ce" na daɗe inason na samu damar faɗa miki abinda ke cikin raina amma sai nake ganin kamar bazaki aminta dani ba, wlh Aleema ina matukar sonki tun ba yau ba dan Allah kar kiyi rejecting soyayya ta please leema" tunda ya fara magana Aleema take kallonsa with so much surprised koda wasa bata taɓa tunanin haka daga gareshi ba duba da yanda yake maganar zaka fahimci har cikin zuciyarsa haka yake nufi miƙewa ta yi ta ce"I'm so sorry amma ni ban taɓa soyayya ba and kuma banajin zan iya farata yanzu coz karatu shine abinda nake focusing yanzu dan Allah ka fahimceni" tana gama faɗin haka ta juya tabar wajen da kallo kawai Farooq ya bita sannan ya girgiza kansa wani killer smile ya yi ya ce"karki damu yarinya da sannu zaki zo hannuna" ya tashi ya yi waje dan daman fita zai yi

"Me kika tsaya yi?"

numfasawa ta yi ta ce"wlh Mami na ɗan tsaya magana da Farooq ne" "Farooq kuma mene ya haɗaki da magana dashi?" murmushi ta yi ta ce"Mami karki damu" taɓe baki Mami ta yi ta ce"kije ku ci abinci zuwa anjima Khalil zai zo ku fita nima yanzu fita zanyi" okay Aleema ta ce sannan ta shige ciki, Da sallama ta shiga zaune ta tarar da Mommy tana danna wayarta da alama magana mai muhimmanci take tana ganin Mami ta tashi tana murmushi ta ce"sannu da zuwa" zama Mami ta yi ta ce"yawwa " "ya jikin Ma'eesha?" murmushi Mami ta yi ta ce"da sauƙi Alhamdulillah yau ne dai ta tashi da abun dan taƙi kula kowa" girgiza kai Mommy ta yi ta ce"Allah sarki ubangiji ya yaye mata cikin sauƙi" "Ameen" cewar Mami, Mommy ce ta ce"yawwa daman munyi magana da talatu ta ce za'a samu kayan" "Nima daman abinda ya kawoni kenan zuwa anjima idan kin shirya zamuje siyan ragowar wanda akayi order kuma sun zo to za'a je jere in sha Allah" murmushi Mommy ta yi ta ce"Allah sarki Ma'eesha da yanzu tana ta surutu kala-kala ta ce wannan ta ce wancen, to Allah ya kaimu anjiman daman babu abinda nake" okay Mami ta ce Sannan ta tashi ta fita. Murmushi Mommy ta yi ta ce"dani kike zancen Asma'u".
Chapter 25 · 0% Book details