← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 29

Sashe 21

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shiru General ya yi yana saurarenta har ta kammala maganar sannan ya ce"then me kikeso nayi akai?" murmushi Mommy tayi ta ce"A'a kawai daman naga ya kamata ace na sanar maka ne shiyasa" bai ce mata komai ba ya cigaba da sipping coffee ɗinsa, sakkowa tayi daga saman tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya murmushi Mommy tayi ta ce"Shalele an tashi" shiru Ma'eesha tayi mata tana zuwa ta zauna gefen General ta ɗora kanta a cinyarsa shafa kanta ya yi sannan ya ce"Shalelena meya faru?" shiru tayi masa hakan yasa ya leƙa fuskarta ƙuri tayi masa da idanu ya sake cewa"ƴar gidan Father tell me kedawa?" ganin tayi banza yasa Mami ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce"ke bakijin ana yi miki magana ne kikayi shiru Ma'eesha ki kiyayeni fa!" ko kallonta Ma'eesha bata yi ba hakan yasa General ya sake kallonta idanunta a buɗe suke balle ace bacci take ɗago kanta ya yi ya ce"ƴar Baba meyasa kika yi shiru" a hankali ta ɗora hannayenta bisa fuskarsa ta shiga shafawa sai kuma tayi murmushi da tsananin mamaki duk suke kallonta General ya ce"faɗa min mene ke yi miki ciwo?" bakinsa tabi da kallo sai kuma ta girgiza masa kai miƙewa tsaye ya yi yana riƙe da hannunta ya ce"Ma'eesha bazaki magana ba?, ni abokin wasanki ne? Ma'eesha I'm ur mate da nake miki magana nd u remain silence?" da kallo kawai Ma'eesha ta bishi sai kuma ta faɗa jikinsa tana sakin wani kuka mai sauti" da sauri General ya kalleta sai kuma ya durƙusa yana kallon kyakkyawar fuskanta ya ce"Ma'eesha baki jin abinda nake faɗa miki ne ko kunnenki na yi miki ciwo ne?" bakinsa ta ƙalla sai kuma ta girgiza masa kanta da hannu ta nuna masa bakinta sai kuma ta nuna masa kunnenta da sauri Mami tace"Ma'eesha baki jin abinda muke faɗa, tell us Ma'eesha" ta faɗa tana jijjigata fashe tayi da kuka tana rungume Mami, cikin tashin hankali Mami ta ɗago fuskarta ta ce"Ma'eesha kinji abinda na faɗa?" kallon bakinta tayi sai kuma ta girgiza mata kai tana goge mata hawayen dake zuba a fuskarta. Cikin kuka Mami ta ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Ma'eesha wane yayi miki haka?, Wa ya kurumtaki?, me kika yiwa wani? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun mun shiga uku" da sauri Mommy ta rufe mata baki tana kuka itama ta girgiza mata kai ta ce"ki daina cewa an shiga uku zaki ƙara wata masifar kawai muyi mata addu'a koma wane ya yi mata wannan abun Allah ya saka mata kuma ya bi mata haƙƙinta" fashewa Mami ta yi da kuka tana dafe kanta ta ce" me tayiwa wani?, yarinyar da bata shiga harkar kowa babu ruwanta da mutane wane mara imanin ne ya cuci rayuwarmu" ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka mai gunji. Miƙewa General ya yi wanda idanunta suka kaɗa sukayi wani irin jaaa waje ya yi ko gabansa baya gani sake tashi Mami tayi ta koma inda Ma'eesha take zaune tana kuka ta kama hannunta ta ce"Ma'eesha kinyi faɗa da wani ne ko akwai wanda ya ce zai yi miki wani abu?" girgiza mata kai Ma'eesha ta yi takama hannun Mami tana ɗorawa akan bakinta ta girgiza mata kai rungumeta Mami tayi tana sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kaɗai ce ƴar data mallaka kuma take burin taga tayi aure kodan su samu ƙarin zuri'a tunda su basuda yawa sai gashi an samu wani mara imanin ya kurmantata dan babu shakka wannan abun ture akai mata ko jifa. Shigowa Farooq ya yi da mamaki yake kallonsu duka dan shi tunda sassafe ya fita ƙarasawa ya yi ganin yanda suke kuka kamar waɗanda aka yi mutuwa ya kalli Mommy ya ce"Mommy what happened?" kasa bashi amsa Mommy tayi saboda kuka da yaci ƙarfinta hakan ya sa ya ce"Mami dan Allah ku sanar dani abinda yake faruwa" kallonsa Mami tayi da idanunta wanda suka yi wani irin jaa ta ce cikin kuka"Farooq sun kurmantata sun cucemu Ma'eesha bata jin abinda muke cewa kuma bata magana" cikin tsananin tashin hankali ya ce"what!!!?" ƙarasowa gaban Ma'eesha ya yi ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa cikin wata iriyar murya mai nuna zallar tashin hankali ya ce"Shalelen Father ki cemin ba haka bane abinda Mami tafaɗa ki yimin magana dan Allah Ma'eesha kice wani abu ko naji sanyi a raina nasan halinki da wasa dan Allah Ma'eesha stop joking tell me the truth kar zuciyata ta buga kiyimin magana naji muryarki kinji shalelen ƙanwata" da idanu kawai Ma'eesha ke binsa da kallo dan yawan maganar da ya yi mata yasa ta gaza fahimtar koda magana ɗaya abu ɗaya kawai tasani shine yana magana ne akan abinda ya sameta hakan yasa ta nuna masa bakinta da kunnenta sannan ta girgiza masa kai. Durƙushewa Farooq ya yi kamar ƙaramin yaro ya shiga rera kuka wanda ya daɗe bai yi irinsa cikin rayuwarsa ba kuka ne wanda yake fitowa tundaga zuciyarsa yana matuƙar son Ma'eesha bashida burin daya shige ganin farin cikinta koda yakeson ya rabata da iyayenta yana yine sbd hakan ya kasance ƙudirinsa amma bazai taɓa mance Alkhairin Ma'eesha a gareshi ba bazai manta irin so da ƙaunar da take nuna masa ba tabbas duk wanda ya yi mata wannan aika-aikar to ɓa ƙaramin maƙiyinta bane. General ne ya shigo cikin sauri gabaɗaya ya fice hayyacinsa wasu doctors ne guda biyar suka shigo sai Farooq da His Excellency Muhammad Tanka da sauri Khalil ya ƙarasawa wajenta ya kama hannayenta cikin sanyin murya mai nuna rauni ya ce"

_Ƙaddara a bace wacce bawa baya iya tsallaketa kowa da kalar tasa ƙaddarar kuma kowa da akwai silar tasa ƙaddarar ba'a iya guje mata domin ita ta kasance rubutacciyar aba ce tamkar zanen dutse haka take duk yanda zakayi bazaka iya gogeta ba no matter who are you or what you have nobody can change his/her destiny either good or bad ya rabbi ka bamu ikon cinye duk wata jarrabawar da zaka yi mana😭🤲🤲_.

# *Love*
# *Destiny*
# *Manifestation*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce ✍️*.https://chat.whatsapp.com/BghAYLLnNSvK6y3XpGoE9I

*BA ITA BA CE!..💖💖*

*Nanameera ce ✍️*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

```Page 14```

"Eeshana da gaske baki jin abinda nake faɗa? eeshana ki ce ba gaskiya bane abinda ake faɗa min talk to me please" ya faɗa yana jijjigata, fashewa tayi da kuka ta rungumeshi tana girgiza masa kai Dr Sabo ne ya ƙaraso wajen yana kallonsu ya ce"aje da ita asibiti maybe agano abinda ke damun nata" okay kawai Khalil ya ce sannan ya miƙe tsaye yana riƙe da hannunta sukayi waje ajiyar zuciya Mami ta shiga saukewa tana binsu da kallo har suka fice sannan ta tashi da sauri ta haye sama da kallo Mommy ta bita sannan ta tashi itama ta shige nata apartment ɗin, cikin tashin hankali take cewa"wlh Fulani bazan iya jurewa ba zuciyata bazata iya ɗauka ba tashin hankalin ya yimin yawa Ma'eesha fa dan Allah" daga ɗaya ɓangaren ta ce"haba Asma'u mene haka?, ki yarda da ƙaddara mana babu wanda ya isa ya sauyata koma wane ya yiwa Ma'eesha mugunta ai Allah yana ganinsa kuma zai yi maganinsa saboda haka karki sake cewa zaki damu kanki ku tayata da addu'a Allah ya bayyana asirin koma wane idan kuma Allah ne ya ɗora mata to shi zai yaye mata zuwa gobe ko su Jakadiyane zasu zo sai su tawo da Aleema" gyaɗa mata kai Mami tayi saboda kuka da yaci ƙarfinta girgiza kanta tayi tana ajiye wayar ta ce"Allah dan girmanka da buwayarka Allah dan zatinka ka bayyana koma wane ya aikatawa Ma'eesha haka Allah ka bata lafiya ka yaye mata ka kuma bamu ikon cinye jarrabawar" ta ƙarashe maganar tana kuka kamar ranta zai fita gabaɗaya duniyar tayi mata zafi rabonda ta shiga tashin hankali irin wannan tun ranar da Mai martaba ya rasu girgiza kanta ta yi tana jinjina mugunta irinta ɗan Adam ko me Ma'eesha ta aikata?????.
Chapter 21 · 0% Book details