← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 29

Sashe 13

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin haɗaɗɗen parlon ne mai Matuƙar girma komai na cikinsa silver ne sai sheƙi yake parlon ne mai kamada faɗa kana ganinsa kasan wasu ishasshun mutanene ke rayuwa a ciki zaune suke sunyi da'ira akan wani katafaren dinning table mai kyau abincine baje a gabansu sai wanda kaga damar ci, manyan masu kuɗi ne amma ba larabawa ba kana ganinsu kasan zamane ya kaisu ƙasar, dan larabawan basuda yawa sosai a cikinsu, wani babban mutum ne ya kalli Zaki wanda ke zaune kujerar dake facing tasa yana sanye cikin wasu suit black colour ya ɗora Glass akan fuskarsa ya yi wani sihirtaccen kyau cikin isa ya ce"Lion" ɗagowa Zaki ya yi ya ce"Yes sir" ajiye cokalin hannunsa ya yi ya ce"mata nawa ne yanzu a hannunka?" cikin sanyin murya ya ce"only 5 remains" murmushi ya yi ya ce"zuwa dare ka bawa Taj ya kawosu" ajiyar zuciya Zaki ya sauke sannan ya ce"amma Sir da an nemi wasu cox waɗannan sun ɗan daɗe a ajiye" gyaɗa kansa ya yi ya ce"Eh kuma hakane amma ai naji Taj yana maganar wata yarinya da ka siya right" da sauri Zaki ya kalleshi kafin ya ce"hakane" murmushi ya yi ya ce"kawai ka bawa Taj ita ya kawomin da daddare hope virgin ce?" gyaɗa masa kai kawai Zaki ya yi yana sauke wani numfashi ya miƙe without looking at anybody ya yi waje, da kallo suka bisa sannan wani daga cikinsu ya ce"wannan yaron ɗan zafin kaine yanada wahalar sha'ani" murmushi ya yi ya ce"haba Bala ai Zaki ba daga nan ba shiyasa nakeson mu'amala dashi above 5yrs muna tare dashi anan amma koda wasa bai taɓa yimin abinda ba daidai ba. Yasan aikinsa sosai shiyasa duk cikin yarana both na nan dana 9ja nafi sonsa kuma bakowa yakewa aiki ba" murmushi wanda aka kira da Balan ya yi ya ce"ai naga alama gashi yasan takan mata idan ya kawo maka mace kamar karka rabu da ita shiyasa nake son aikinsa" murmushi ogan ya yi ya miƙe ya ce"bari naje na shirya yau inada sabon jini" tuntsirewa sukayi da dariya ɗayan ya ce" kaifa Dmash bakada kyau kuma baka wasa da kaya" sunkuyowa ya yi ya ce"wazai yi wasa da abinci ai babu" yana faɗin haka ya haye sama suka bisa da dariya.

Shigowa ya yi parlon hannunsa zube cikin aljihu yana tafiya yana furzar da wani irin zazzafan numfashi, zaune ya samesu ita da Taj yana bata labaru kanta a ƙasa dan bata san shi ba kuma batada saurin sabo, miƙewa ya yi yana kallon Zaki ya ce"sai yanzu?" gyaɗa masa kai kawai ya yi sannan ya haye sama, miƙewa Muhaira tayi Taj ya ce"A'a beauty ina za ki kuma?" turo baki gaba tayi tana wasada fingers ɗinta masu tsayi ta ce"to ba wajensa zan je ba" murmushi ya yi ya ce"shi wa?" da sauri ta kallesa da idanun ya kashe mata ido ya ce"kinsan shi ne?" kwaɓe fuska ta yi ta ce"Papina ne ai to" dariya ya yi ya ce" su Zaki Papi are you Fulani?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"enyeee kuma kin iya fulden?" gyaɗa masa kai nan ma ta yi ya ce"to yimin naji" buɗe baki ta yi zatayi magana suka ji ƙarar taku da sauri duka suka juya suna kallonsa. Sanye yake cikin wata armless maroon colour ya sanya Three-quater Maroon colour shima ya sanya Gucci brand fara akansa gashinsa ya sauka akan bayansa hannunsa riƙe da mug ɗin coffee.

Taɓe baki ya yi bai kulasu ba ya zauna kan wata kujera ya zauna komawa suka yi suka zauna suma duk sunyi shiru kamar waɗanda akawa dole, a hankali yake sipping coffee ɗin hannunsa har ya shanye sannan ya ajiye mug ɗin a table ɗin gefensa ya juyo yana kallonsu, murmushi ya yi yana kallon Taj ya ce"munafiki" dariya Taj ya yi ya ce"naji ɗin, wai Sir Dmash ya ce nazo na tafi da yarinyar nan" haɗe rai Zaki ya yi bai ce masa komai ba ya kalli Muhaira wacce take kallon Taj ya ce"kee come here" miƙewa tana tafiya a hankali ta ƙaraso gabansa ta tsuguna kallon fuskarta ya yi for some minutes sai kuma ya ce"jeki bedroom ɗina ki ɗaukan wayana" miƙewa tayi ta haye sama, sai a sannan ya kalli Taj ya ce"zan kai masa ita da kaina kawai kayi tafiyarka" kallonsa Taj ya yi da mamaki ya ce"da kanka kuma amma why?" haɗe rai ya yi ya tashi ya miƙe tsaye daidai lokacin Muhaira ta sakko hannunta riƙe da wayar tasa, kallonta ya yi sanye take da wata riga long sleeve amma bata ƙarasa saukar mata ba ta tufke gashin kanta ya sauka har wajen ƙugunta, miƙa masa wayar ta yi ya karɓa sannan ya yi waje yana jan hannunta.

Kai tsaye part ɗin ƴan matan gidan yana nufa har sannan kuma yana riƙe da hannunta ita kuwa sai binsa take kamar wata doluwa suna zuwa ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama wacce ba lallai bane su jita, zaune take a parlon tana karatun littafinta da sauri ta miƙe cikin rawar murya ta ce"bar...barkaaa da fitowa yallaɓai" kallonta ya yi from head to toe sai kuma ya ɗauke kansa ya ce"uhnnn ina suke sauran?" cikeda ladabi ta ce"suna bedroom bacci suke" bai ce komai ba ya juya ya bar wajen Muhaira ta bita da kallo. Cikin wata mota Fererri ash colour ya sanyanta sannan ya zagaya wajen driver da sauri guards ɗinsa suka tawo ya ɗaga musu hannu sannan shiga motar ya yi mata key bakinsa ɗauke da addu'a.

A hankali ya sanyo ƙafarsa waje bayan ya kashe motar kusan 2mins yaga bata fito ba hakan yasa ya koma side ɗinta yana yi mata wani kallo ya ce"jira kike saina fito dake ne?" zumɓura baki ta yi ta ce"to ni nasan yanda ake buɗewa ne da zaka yimin faɗa" kwafa Zaki ya yi sannan ya buɗe motar yana harararta ya ce"baƙauyiya kawai" fitowa ta yi sannan itama ta galla masa harara cikeda tsiwa ta ce"naji ɗin kai kuma mai yiwa mutum iss..." maganar ta maƙale saboda wani mugun kallo da taga ya watsa mata ta haɗe rai itama tana ɗauke kanta tsaki ya yi sannan ya ce"Mumu kawai witch" wasu hawayene suka shiga sakko mata na baƙin ciki ita kwata-kwata batasan mutumin nan saboda ko kaɗan bashida kirki a hankali ta shiga murza idanunta tana shashshekar kuka dafe kansa ya yi ganin yarinyar na son tara masa mutane ya ce a fusace"idan baki yimin shiru ba saina kwaɗa miki mari wlh" banza ta yi masa ta nemi waje ta zaune kasancewar duk ƙasan garin kamar glass yake ko'ina tsaf, kallon agogon rollex ɗin hannunsa ya yi sai kuma ya kalleta ya ce" shikenan tashi kiyi shiru kinji" turo baki ta yi tana murza idonta ta ce"to ka maidani gidanmu ni, banason nan ni banasoo!!" ta faɗa tana sake fashewa da kuka.

Ganin da gaske Muhaira bazata tashi ba yasa ya yi gaba cikin wata iriyar murya mai ban tsoro ya ce"gasu nan ku kamata" da gudu tabi bayansa tana riƙe masa hannu kyakkyawan murmushi ya yi ita kuwa ta riƙe shi gam gudun kada ya tafi ya barta. *Olaya Aqua park* shine sunan dake saman haɗaɗɗen ginin cikin tafiyarsa ta isa ya shiga ciki tana riƙe da hannunsa.

*ZAKI HAKA ZAMU YI DAKAI😢😭😂*

# *LOVE*
# *DESTINY*
# *POWER*
# *TRAFFICKING*
# *SQUAD 2024*
# *NANAMEERA CE!✍️*
[8/7, 1:58 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖*

*Ameenatou I Ibrahim*
*Nanameera*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

```Page 09```

*Olaya Aqua park*
Kallon wajen kawai Muhaira take kamar idanunta zasu faɗo iyaka haɗuwa wajen ya haɗu park ne mai ɗauke da swimming pool amma rufaffe akwai wadataccen haske a wajen dan bazaka taɓa cewa ba rana ba ce ba jan hannunta Zaki ya yi suka shiga wata ƙofa sai a sannan tagane ashe da ba taga komai ba inda suke tsaye yafi inda suka shiga da farko haɗuwa tsayawa ya yi gaban swimming pool ɗin wanda yake bada feshin ruwa mai matuƙar sanyi murmushi tayi tana cire hannunta daga nasa ta ƙarasa wajen tana shirin zura ƙafafunta taji an riƙeta. Kwaɓe fuska tayi tana kallonsa taga ya haɗe rai sai ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta ce"dan Allah Papi nashiga?" girgiza mata kai ya yi ta langwaɓar da kanta cikin sigar roƙo ta ce"wlh bazan yi wasa ba" taɓe bakinsa ya yi sannan ya ja hannunta zuwa wasu kujeru wanda suka zagaye wajen zama ya yi ya zaunar da ita gefensa bai ce mata komai ba, sosai ranta ya ɓaci dan ita a rayuwarta tana matuƙar son wasan ruwa dukda illar da hakan ke mata wata waiter ce tazo ta ajiye musu ice-cream a table ɗin gabansu sannan tabar wajen, kallon ice-cream ɗin Muhaira ta yi amma bata ɗauka ba wayar hannusa ya mayar aljihu sannan ya ɗauki ice-cream ɗin guda ɗaya ya fara sha sosai yake lumshe idanu saboda daɗin ice-cream ɗin hakan yasa Muhaira ta sanya hannunta zata ɗauki ɗayan, buge mata hannu ya yi yana harararta har sannan kuma bai ce mata komai ba. Turo baki ta yi cikin shagwaɓa ta ce"toh ni bazan sha ba?" banza Zaki ya yi mata ya cigaba da abinda yake aikuwa ta fashe da kuka yana jinta har ya shanye na hannunsa sannan ya ɗauki ɗayan ma ya fara sha ganin da gaske shanyewa zai yi bai bata ba yasa ta ƙara volume ɗin kukanta wani killer smile ya yi sannan ya kalleta ganin yanda duk ta ɓata fuskarta da hawaye ya ce" then you like it?" saurin gyaɗa masa kai ta yi ya dungure mata kai ya ce"kwaɗayayiya kawai" hannunta ta sanya tana dafe goshinta ta ce"ohhccccc zafi wayyo" harararta ya yi sannan ya miƙa mata ragowar na hannunsa karɓa tayi tana cigaba da kukanta har ta shanye sosai ice-cream ɗin ya yi mata daɗi dan yau ne shanta dashi na biyu miƙewa ya yi yaje wajen swimming pool ɗin ya zauna a nutse ya zura sangalin fararen ƙafafunsa cikin ruwan a hankali yake furzar da wani zazzafan numfashi gabaɗaya tunaninsa ya kwance abubuwa nason fin ƙarfinsa rauninsa nema yake ya fito fili wanda hakan ne yake gudu.
Chapter 13 · 0% Book details