← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sake riƙe hannun General tayi ganin wasu mahaukan jami'an tsaro dukda ta saba ganin na gidansu amma waɗannan sunfi nasu yawa, har suka shiga main parlon na gidan Ma'eesha bata saki General ba sai kwaɓe fuska takeyi saida shugaban ƙasa Muhammad Sani Tanka ya fito sannan suka zauna bayan sun gaisa ya kalli Ma'eesha ya ce"ƴar Baba kin girma ko?" kasancewar General abokinsa ne tun suna yara yasa sunsan juna sosai murmushi ya yi ya ce"daman jiya Khaleel ya dawo kije yana second parlon ɗin nan" to kawai ta ce sannan ta miƙe tana tafiya a hankali har ta buɗe ƙofar parlon. Haɗaɗɗen parlon ne wanda aka kashe iyayen kuɗi wajen haɗashi ƙamshin turaren Parfums De marley Layton ne ya daki hancinta ta lumshe idanunta kafin tayi sallama, zaune yake ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya black beauty ne yanada cute round face da siririn hanci sai beard ɗinsa mai kyau kana kallon fatarsa kasan kuɗi ya zauna. Ƙasa ƙasa ya amsa sallamar tata kafin ta zauna kujerar dake gefensa waro idanunsa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce"eesha" murmushi ta yi ta ce"ya Khaleel ina yini?" girgiza kansa ya yi ya dawo gefenta ya ce"ashe dai ban manta ki ba, ykk yasu Mami?" tana wasada fingers ɗinta ta ce"suna nan klao, ashe ka dawo" ya ce"Eh nadawo jiya shekaru sun tafi eesha kin girma abinki" rufe fuskarta tayi da hannu tana murmushi ta ce a shagwaɓe"kai yaya ai kaima ka ƙara girma sosai ji beka fa kafi ya Farooq" haɗe ransa ya yi ya ce"har yanzu wannan guy ɗin na gidanku?" sunkuyar da kanta tana gyada masa kai dan tasan ko kaɗan basa shiri da Farooq, ɗaga kafaɗarsa ya yi ya ce"amma mene yake har yanzu a gidan i think ya isa ace ya yi aure ya bar gidan" ɗaga kafaɗarta ta yi alamar bata sani ba ya ce"then yana shiga harkarki" ji tayi gabanta ya yanke ya faɗi ta yi shiru bata bashi amsa ba, hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta kallonsa tayi taga fuskarsa babu alamar wasa hakan yasa ta fashe da kuka tana faɗawa jikinsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya Khaleel ya sauke yana riƙe da ita above 3mins kafin ya ɗagota yana kallonta ya ce"baki amsa min tambayata ba eesha" tura baki tayi gaba ta ce" to ai naga a gidanmu yake kuma..." kallon da taga ya yi mata ne yasa tayi shiru bata ƙara sa abinda zata faɗa ba shiru ya yi na wasu seconds tuni idanunsa suka sauya kala wani ruwa ya kwanta a kansu lura da hakan yasa tayi sauri miƙewa tsaye cikin sigar rarrashi ta tsuguna a gabansa tana haɗe hannayenta biyu ta ce"dan Allah yaya Khaleel kayi haƙuri bazan sake ba wlh dan Allah" ta faɗa tana shashshekar kuka miƙewa tsaye ya yi bai ce komai ba ya kama hannunta hakan yasa ta miƙe itama tabi bayansa har suka shiga wani ƙaton parlon.

Parlon ne babba nan ma ya sake buɗe wata ƙofar inda suka shiga wani haɗaɗɗen waje kamar stadium ko'ina anyi zane duk bangon ɗakin an yi kaca-kaca dashi hannunta ya ja har gaban wani bango wanda duk akayi zane iri-iri a jikinsa wani ansa Ma'eesha, wani eesha, wani kuma Khalil wani kuma Tanka wasu kuma heart aka zana a ciki an saka *Khaeesh* batasan sanda ta rungumeshi ba tana kuka kamar ranta zai fita hannayensa ya sanya ya zagayeta ajikinsa yana jin yanda duk ta jiƙa masa ƙirji da hawaye saida tayi kuka mai isarta sannan ta ɗago ta kalleshi cikin kuka ta ce"ya Khaleel meyasa kaci amanata?, ya Khaleel meyasa kayi aure ka barni?, ka manta sanda kake cewa ni zaka aura Father zai bar maka ni shine kaje kayi aurenka a wata ƙasar ya Khaleel baka sona ni kaɗai nake sonka kuma nima yanzu nadaina sonka bana son..." da sauri Khaleel ya haɗe bakinsa da nata yana bawa lips ɗinta wata amintacciyar tsotsa yayinda hawaye suka shiga gangarowa kan kuncinsa shima sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka jikin Ma'eesha ban rawa babu abinda yake a hankali ya zare bakinsa daga nata yana kallon kyakkyawar fuskanta wacce tayi face-face da hawaye ya ce"

# *Khaleel*
# *eesha*
# *Zaki*
# *Muhaira*
# *love*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!✍️*
[8/8, 11:33 AM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖*

*NANAMEERA*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

```Page 10```.

# *The war*

"I'm sorry eesha amma ya kamata ace kin tsaya kin fahimci abinda zan faɗa miki wlh isn't my fault banida zaɓi na auri Ramlah ne saboda babu yanda zanyi ni ne nake kula da ita nd kuma yanayin lalurarta dole idan ta ce tanason abu ayi mata shi idan ba haka ba za'a ga ba daidai ba wannan shine dalilin kawai" girgiza kai tayi tana raba jikinta da nasa ta ce"A'a yaya Khalil kaima kana sonta yasa ka aureta idan ba haka ba bazaka mance alƙawarinmu cikin sauƙi ba, karka damu nima yanzu inada wanda nakeso kuma nake shirin aure saboda haka..." hannayensa ya sanya yana rufe mata baki cikin zafin rai ya ce"wlh baki isaba eesha ke tawace ni kaɗai kuma babu wanda ya isa ya aureki ina raye kuma na barshi nasan kin gane abinda nake nufi"ture hannunsa ta yi tana harararsa ta ce"da kenan amma yanzu na shige wannan level ɗin kuma har abada zan cigaba da kallonka matsayin marayaudari wanda yaci amanata" ta ƙarashe maganar tana rufe bakinta saboda wani kuka daya zo mata da gudu ta fice daga ɗakin. Jingina ya yi da wall ɗin ɗakin yana dafe kansa gabaɗaya ya ji duniyar tayi masa zafi furzar da wani irin zazzafan numfashi ya yi sannan ya juya ya fita. Zaune ya tadda ta kan royal cusion ɗin parlon sai kuka take kamar ranta zai fita, hannayensa zube cikin wandonsa ya ƙaraso gabanta sannan ya tsuguna ɗago fuskarta ya yi cikin sanyin murya ya ce"eeshana" kallonsa tayi da idanunta da suka sauya kala zuwa jaa bata ce komai ta cigaba da kukanta cikin son ya rarrasheta ya ce"now tell me kina sona?" da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta janye hannunsa daga kan fuskarta ta miƙe tana kallonsa ta ce"a baya dai na soka yaya Khalil naji kamar bazan iya rayuwa idan babu kai ba nayi mararin kasancewa matarka kamar yanda ka kwaɗaitamin" numfasawa ta yi sannan ta cigaba da faɗin"amma yanzu na haƙura dakai na barka kayi rayuwa mai daɗi da matar daka aura nima ina fatan nasamu wanda zai soni sona har ƙarshen rayuwa"ta ƙarashe maganar tana goge hawayen kan fuskarta, miƙewa tsaye ya yi yana kallonta zuciyarsa fal tausayinta ya ce"Ma'eesha nasan nayi kuskure amma dan Allah karki ɗauki haka matsayin makamin da zaki cutar da rayuwata har yau har gobe ina sonki kuma inada burin aurenki ƙaddara ce ta rabamu amma nayi miki alƙawarin wannan karan bazan bari ta rabamu ba"

"Aikuwa kayi kaɗan kuma kayi ƙarya domin ƙaddara ta rigada ta gifta tsakaninku babu kai babu ita har abada matuƙar ina numfashi wlh Khalil bazan bari ka zauna da ita ba ko a baya ina faɗa maka balle kuma yanzu da ka rigada kayi aure" hankali tashe yake kallon Mommy bashi kaɗai ba hadda Ma'eesha wacce tazama kamar statue a wajen kenan har i Wannan lokacin Mommy bata daina tsanarta ba?, har yanzu tana nan akan bakanta na son ganin bayanta?, a baya ta saba da cin zarafin Mommy a gareta tun bata san tsanarta Mommy tayi ba har tayi girman da ta fahimci komai amma tsananin so da ƙaunar da takewa Khalil ya sanya bata iya fushi koda yaushe tana hanyar zuwa inda suke. Bakinsa na rawa ya ƙarasa wajen Mommy yana kallonta ya ce"haba Mommy i think ai mun shige wannan level ɗin mene haka please?, mene ne aibunta da kika tsaneta har haka?, ya kamata ace ko dan saboda ni ki daina yi mata irin waɗannan abubuwan yanzu fa ba da bace Ma'eesha ta girma tasan kanta zata fahimci duk abinda kike mata dan Allah Mommy stop it" juyowa ya yi da niyyar yiwa Ma'eesha magana saida ko inuwarta babu tun sanda ya bar gabanta ta fice daga parlon, dafe kansa ya yi sannan yabi bayanta.

Tsaye ya sameta jikin corridor tana goge hawayen fuskarsa gudun kada General ya gani, rungumeta ya yi ta baya hakan yasa ta sake fashewa da wani sabon kukan na takaici jan hannunta ya yi bai ce mata komai ba ya buɗe wata ƙofa suka shiga kai tsaye kuma waje suka fito motarsa ya buɗe ya zurata ciki sannan shima ya shiga ya yi mata key suka bar gidan, kwafa Mommy tayi tana sakin curtains ɗin ta ce"dani kake zancen wlh" ta shige bedroom ta ɗauki wayarta ringing ɗaya matar ta ɗauka Mommy ta ce"kina ina Hajiya?" daga ɗaya ɓangaren ta ce"kin ganni nan ina gida lafiya?" girgiza kai Mommy ta yi ta ce"gobe ki zo zaki rakani unguwa" okay kawai ta ce sannan ta kashe wayar ta shiga safa da marwa cikin ɗakin sai kuma ta fita.
Chapter 15 · 0% Book details