← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 29

Sashe 4

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Heyyyyyyyy! yimin shiru aku kawai bazan ƙarasa ba anan zan tsaya sauka kije ayi miki idan kin gama kizo mu tafi or else..." kallonsa tayi tuni hawaye ya fara sintiri akan kuncinta cikin kuka ta ce"dan Allah yaya kayi haƙuri kaga idan naje ƙafana ciwo zai yimin dan Allah ka ƙarasa dani" ba zaka taɓa cewa da Farooq take magana ba dan ko inda take bai kalla ba danna wayarsa kawai yake, sanin halinsa na kaifi ɗaya ya sanya Ma'eesha ta sauka daga motar tana tafe tana kuka har ta tsallaka ɗaya side ɗin, tafiyar wajen 5mins ce ta kawota bakin shagon a hankali ta tsaye ta goge idanunta sannan ta shiga ciki. Above 1hour kafin a gama gyara mata kan, kasancewar ba kuɗi take biya ba already an biya ya sanya ta fito dan su tafi gida saidai me??? tana zuwa inda tabar Farooq ɗazu taga babu shi babu alamarsa kuma babu motar ga wani irin ciwon ƙafa da take yi zama tayi gefen titin ta rushe da kuka tamkar jaririya tana yi tana jan numfashinta saboda asthmarta dake shirin tashi, ta ɗauki aƙalla awanni biyu zaune a wajen kafin ya dawo da sauri ya ƙaraso gabanta yana kallon yanda ta dunƙule waje ɗaya ya dafata, da sauri ta ɗago kanta ta kallesa sai kuma ta sake rushewa da wani kukan, kyakkyawan murmushi ya yi sannan ya kama hannunta cikin sigar rarrashi ya ce"ya isa tawo ƴar Babyn Father daina kuka kinji" ganin taƙi miƙewa yasa ya sanya hannayensa duk biyun ya ɗauketa kamar Baby ya sanyata a motar. Zama ya yi sannan ya ɗorata akan ƙirjinsa ya rungumeta tamkar wacce ake turata haka ta sake fashe da wani kukan, shafa kanta ya shiga yi cikin cool voice ya ce"I'm sorry naje unguwa ne amma bazan ƙara ba kidaina kuka kefa jaruma ce" ɗago fuskarta ya yi to see her reaction yaga sake haɗe ranta tana murza idanunta. Murmushi ya yi ya ce"shikenan muje na siya maki chocolate sai mu koma gida" da sauri ta ɗago ta kalleshi ya ɗaga mata gira ya ce"then you love it?" tura baki tayi sai kuma ta girgiza masa kai tana sake komawa kan ƙirjinsa, dariya ya yi ya ce"gulma ko?" murmushi tayi tana ɓoye kanta ta ce cikin wata murya irinta shagwaɓaɓɓun ƴaƴa "yaya ƙafana zai cire wayyo zafi yake minnnn!" a ɗan rikice ya kalli ƙafar tata sai kuma ya ce"I'm sorry bari muje gida sai a samiki magani sannu kinji" gyaɗa masa kai tayi tana matse hawaye shikuma ya yi motar key suka bar wajen.

*MALAM DUDU POV*

Cikin wata iriyar murya mai tsananin amo yake cewa"daman ai mun sanar dake lokacin zai ƙarato to yanzu gashi nan yazooo Hhhhhh!, Keee Hajiya yanzu lokacin daya dace ya auri wannan yarinya komai na ƙarƙashin kulawar mu karku wani damu ku bil'adama Hhhhhhhh!" cikin rawar murya matar gabansa ta ce"tooo yanzu zan yi masa maganar idan naje gidan amma ya za'a yi shi Alhajin ya yarda da auren nasu ba tareda ya yi tunanin wani abu ba??" haɗe rai bokan ya yi sai kuma ya ce" mantamu kika yi dolensa ya yarda da haɗin auren kuma shine wanda zai fi kowa farin ciki akan hakan Hhhhhhhh!, Ni Dudu nayi miki wannan alƙawarin" shiru tayi sai kuma ta ce"to me zan baka?" Wani mirmushin mugunta ya yi sai kuma ya ce"aikema kin sani" murmushin itama tayi sannan ta tashi ta shige bedroom ɗin dake kusada zauren, mikewa ya yi shima yabi bayanta, sai bayan 50mins sannan ta fito daga ɗakin tana gyara ɗaurin zaninta sannan tayi waje.

*MAI ZAMANI POV*

Kallon doctor yake har ya kammala dubata sannan ya ce"doctor what's going up?" numfasawa ya yi sannan ya ce"sir ba wani abu bane kawai tayi stressing kanta ne nd kuma kasan yanayin lalurarta but nayi mata injection zata samu sauƙi in sha Allah" numfasawa ya yi ya ce"okay you can go we should talk later" okay doctor ya ce sannan ya ɗauki first eid box ɗin nasa ya yi waje daidai nan ta shigo tana kallonsu duka ta ce"yallaɓai ya jikin nata?" batareda ya juya ba ya ce" Alhamdulillah call Farooq" taɓe baki tayi sannan ta juya ta fita, zaune ta sameshi yana shan coffee ɗin nasa na ƙa'ida kallonsa tayi ganin kamar wani abun yake tunani ta ce"Farooq me kake tunani haka" furzar da wani zazzafan numfashi ya yi ya ce"Mommy wlh I'm tired!, nagaji!! I can't endure it anymore haba!" zama tayi gefensa da mamaki a fuskarta ta ce"then what happened?" a ɗan fusace ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana kwafa ya ce"Mommy Are you questioned me?, bama kisan meke damuna ba?, haba Mommy!!" Kama hannunsa ta yi cikin nata cikin son kwantar masa da hankali ta ce" Farooq kanada saurin ɗaukan zafi uhn, ƙoƙari fa nake ganin abubuwa sun tafi yanda mukeso meyasa kake damuwa?" zare hannunsa ya yi daga cikin nata ya miƙe tsaye yana zagaye parlon tamkar wanda ya yi wa Sarki ƙarya miƙewa itama ta yi ta ce"dan Allah ka kwantar da hankalinka kasan farin cikinka shine nawa, amma dole na iya takuna saboda kafini sanin halin General bashida kirki idan yaso" harɗe hannayensa ya yi a ƙirjinsa still looking at her ya ce"then mene ne abunyi Mommy?, Shekaru fa tafiya suke, mistakely idan General ya mutu yanzu zan fa tashi banida komai kema kuma haka amma kin ɗauki abun not serious" murmushin takaici tayi tana kallon ɗan nata ta ce" yanzu me kake so?" ajiyar zuciya ya yi sannan ya kama hannunta ya ce"good!, Mommy kije wajen General da buƙatar mu, tun kafin yarinyar nan wani a waje ganta labari ya sauya she's 17yrs fa yanzu kuma University take zuwa anytime zata iya cewa tana son wani kuma kinsan general bazai mata auren dole ba!" murmushi ta yi ta ce"Farooq ka kwantar da hankalinka indai wannan ne angama aurenka da Ma'eesha ka ɗauka anyisa, Ma'eesha takace kaima kuma kasan da wannan" sai a sannan ya saki fuskarsa ya yi murmushi ya ce"Mommy banson aurena da Ma'eesha ya wuce 2months kiyi iya bakin ƙoƙarinki please" shiru ta yi kamar me nazari sai kuma ta ce"in sha Allah za'a yi amma kafin nan akwai buƙatar na koma wajen Malam dan muji ta bakinsa" miƙewa ya yi ya ce"hakanma yanada kyau ko zuwa dare saina kaiki dan nima inason naji kanun labaran" dariya ta yi ta ce"mai zafi ma kuwa, yanzu dai kaje General na kiranka" okay ya ce sannan ya fita tana biye dashi.

Da sallama bakinsa ya turo ƙofar ɗakin, zaune ya tadda Mami tana bawa Ma'eesha abinci sai General dake tsaye gefenta sauke idanunsa ƙasa ya yi sannan ya ƙaraso parlon Mommy na biye dashi, cikeda ladabi ya ce"Father gani" saida wasu ƴan daƙiƙu suka shige sannan ya kallesa fuskarsa babu alamun rahama ya ce"Farooq mene dalilin barin yarinyar nan tafi tafiya da ƙafarta bayan kasan meke damunta?, sannan idan kasan bazaka iya fita da ita ka kulamin da ita ba mene naka amsawa?, zan iya barin duk wani abu da nake na kaita inda zata sannan na dawo da ita domin duk duniya babu wacce nakeso sama da yarinyar nan, baka saba yimin haka ba tausayi da jiƙai ne tsakaninka da ita saboda haka ka tabbata ka cigaba da tafiya a haka idan ba haka ba zaka fuskanci zallar ɓacin raina get out of my side!" kansa a ƙasa ya miƙe yana kallonsa ya ce"sorry Father Allah ya wuci zuciyarka" sannan ya fice daga parlon, rai ɓace Mommy ta miƙe tana kallon General batace komai ba itama ta juya ta fita. Kallonsa Mami tayi ta ce"yallaɓai wannan abun bai dace ba koba komai kasan Farooq ba daga nan ba wajen kulawa da Ma'eesha yana iya bakin ƙoƙarinsa meyasa zaka yi masa haka?, ai sai ka saka yi dinga tunanin kodan bakai ka haifeshi ba yasa kayi masa haka" wani kallo General ya watsa mata sannan ya ce"ai daman ba nine na haifeshi ba bare ya yi tunani akan haka, lemme tell you something wlh indai akan Ma'eesha ne zan iya faɗa da kowa koda kuwa ace kece da kika haifeta hope you get me right?" ya fice daga parlon a fusace, tagumi Mommy ta zuba tama rasa me zatayi tabbas ba ƙaramin so General Kewa Ma'eesha ba kasancewar ita kaɗai ya haifa itama ɗin bayan shekaru masu ɗinbun yawa, bayan ya cire rai da sabon ƴaƴa kuma tun daga kanta bai ƙara ba wannan ne dalilin daya sanya yake mata wani irin so bashida burin daya shige yaga tana farin ciki haka duk lokacin da ciwonta ya tashi yafi kowa shiga tashin hankali domin kasancewarta AS kuma tana ɗauke da Asthma hakan yasa lokaci zuwa lokaci ciwon yakan tayar mata.

*FAROOQ POV*

"Kin gani ko Mommy, General ya fara gasamin magana akan ƴarsa kuma duk laifinki ne above one year Ina cewa ayi auren nan amma kin ƙi yarda dani, yanzu me kike tunani nan gaba kaɗan zai iya korata cikin gidan nan indai akan wannan shegiyar ƴar tasa ce sbd haka ni gaskiya bazan iya cigaba da lamuntar wulaƙanci ba gwara kawai ayi auren yanzu sai yanda nayi da Ma'eesha kafin nadawo kansa kuma!" ya ƙare maganar yana wani wuci kamar zaki, ita kanta Mommy ranta a ɓace yake dan General ya bata mamaki amma idan tayi duba da irin halinsa da kuma kasancewarsa soja sai gane zai yi abinda yafi haka ma dole ne su nemi mafita tun kafin ya juyo kansu, shiru sukai na wani lokaci sai kuma ta ce"shikenan Farooq ka shirya zuwa anjima zamu wajen Malam nan da 1months Ma'eesha zata dawo ƙarƙashinka sai yanda kaso zaka yi da ita" kallonta kawai ya yi sannan ya juya ya shige toilet dan idan ba shower ya sakarwa kansa ba bazai taɓa jin daɗin duniyar ba, kwafa Mommy ta yi sannan ta juya ta fita.

*YOBE STATE*
*Sabon fegi*

*6:30am*

*MUHAIRA POV*
Chapter 4 · 0% Book details