Sashe 16
Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tura ƙofar tayi ta shiga wani haɗaɗɗen bedroom ɗin ya yi kyau sosai zaune ta hangeta tana danna wayarta hankali kwance tsaki Mommy ta yi sannan ta ƙara sa gabanta tana fincike wayar ɗago kanta tayi tana turo baki sai a sannan na kalleta fara ce tasa amma ba wata kyakkyawa ba kana ganinta kasan idanunta a buɗe suke tasan duniya zama Mommy tayi gefenta ta ce"shashasha kina nan kina danna waya bakisan halin da ake ciki ba" turo baki tayi ta ce"to dan Allah Mommy me zanyi ai bansan meya faru ba kuma kinzo kina min faɗa" girgiza kai Mommy tayi ta ce"to idanma zaki daina wannan shashancin ki daina idan kuma ba haka ba nan da ƴan kwanaki kiji ance mijinki ya ƙara aure" da sauri ta miƙe zaune tana kallon Mommy da manyan idanunta ta ce"Mommy kamarya mijina?, mene ya samu mijin nawa aure kamarya?" ajiyar zuciya Mommy ta sauke ta ce"kamar yanda kika ji na faɗa miki dan Khalil na gab da ƙara aure" miƙewa tayi tsaye tuni attachment ɗin kanta ya wargaje ciki tashin hankali take cewa"dan Allah Mommy ki daina yimin irin wannan wasan haba, ina Khalil ɗin yake?" kama hannunta Mommy ta yi ta zaunar sannan ta ce"bari kiji na faɗa miki kinsan yarinyar da yake so da can baya har na sanya yabar ƙasar saboda kada ya aureta to yanzu daya dawo tazo gidan nan ɗazu da babanta kuma Khalil ya nuna har yanzu yana sonta kuma yanda ya nuna ma nan gaba kaɗan zai aureta" ɗora hannunta tayi a ka cikin tashin hankali take cewa"nashiga uku Mommy wayyo Allahna dan Allah ki hanashi wlh bazan iya zama da kishiya ba" tsaki Mommy tayi ta ce"ke amma anyi shashashar yarinya Macen kikewa kuka?, kishiyar da ba'a yi miki ba?, to ni bazan lamunci kiyi kishi da wata ba bare kuma Ma'eesha dana tsaneta tun tana ƙarama kibar komai a hannuna daga wajenki kawai inason ki tubure ki nuna ke ciwonki ya tashi karki kuskura ki bari ya gane ba ciwon gaske bane ya tashi nikuma duk sauran zanyi" jikinta na rawa ta miƙe tsaye zata yi waje Mommy ta ce"gidan ubanwa zaki?" "Mommy zanje na kwanta ne kafin ya dawo" murmushi Mommy tayi sannan itama ta miƙe ta fice.
*Riyadh*
*Al Olaya residence*
Yana gama breakfast ɗin ya fito cikin cikin wata jallabiya ash colour gashinsa ya sakeshi ya kwanta kan bayansa kallonta ya yi ganin yanda take hawaye har sannan, girgiza kai Zaki ya yi sannan ya ƙaraso gabanta yana kallonta ya ce"tashi tsaye" girgiza masa kai ta yi tana yarfe hannu ya ce"bazaki tashi ba?" kamar zatayi kuka ta ce"ni to bazan iya tashin ba ƙafana yana zafi sosai" dan ƙaramin tsaki ya yi sannan ya sanya hannunsa ya ɗauketa ya fice daga parlon. Kallonsa Muhaira tayi sai kuma ta kalli doctorn kawai ta fashe da kuka haɗe ransa ya yi ya ce"zakiyi min shiru ko saina bige bakin?" ko saurarensa bata yiba ta cigaba da kukanta tana ganin likitan ya gama haɗa allurar ta miƙe da gudu tana rungume Zaki tana sakin wani irin kuka gaba ɗaya sun rigada sun gama gano abinda ya sanyata kukan hakan yasa Zaki ya ce"kidaina wannan abun ki fito ko ranki ya ɓaci" sake zagaye hannayenta tayi a jikinsa ta ce"dan Allah kar ayimin allura wlh naji sauƙi babu zafi yanzu" cikin son shawo kan rigimarta ya ce"babu zafi?" gyaɗa masa kai tayi ya ce"to zo naga" da sauri ta dawo gabanshi ya sanya hannunsa ya jawota jikinsa ya rungume ya ce"to faɗamin mene yake damunki da?" cikin sanyin murya ta ce"ƙafata ce tana ciwo sai kuma kaina, gashi ƙirjina yana min zafi sosai kuma..."maganar ta tsaya sakamakon allurar da taji an tsaka mata da sauri ta sake shigewa jikinsa tana sakar masa cizo murmushi kawai ya yi sannan ya ajiye sringe ɗin yana shafa bayanta ya ce"shhhh ki daina kukan ya isa haka" kamar yana sake tura ta haka ta cigaba da yi masa kuka ya ce"Shikenan kiyi shiru zan siya maki chocolate da ice-cream" cikin shashshekar kuka ta ce"ni a'a banso ka maidani gurin Baba banason nan Papi" shafa kanta ya yi bai ce komai ba yana ji har ta fara sauke numfashi a jikinsa alamar bacci ya ɗauketa. Cikin nutsuwa likitan yake masa bayani ya ce"Sir yarinyar nan tana ɗauke da cutar Asthma sannan kuma reason ɗin dake sawa ta dinga ciwon ƙafa jininta AS ne babbar matsalar kuma ita ce tanada ciwon zuciya wanda yake gab da kaiwa matakin ƙarshe" da sauri Zaki ya kalleshi sai kuma ya kalli Muhaira wacce take rungume ƙirjinsa Allah mai iko wannan ƴar ƙaramar yarinyar da ciwon zuciya abun akwai tausayi sai a sannan maganganun aljanun jikinta suka dawo kansa kenan idan da gaske suke ita ɗin batada kowa kenan?, amma kuma ai a wajen ɗan uwanta ya siyeta something fishy!.
Maganar likitan ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi ya ce"Sir akwai buƙatar a dinga kulawa da ita da abinda zata ci da wanda zata sha sannan kuma kada a dinga yawan ɓata mata rai dan hakan zai iya haifar da matsala" duk wannan maganar da ya faɗeta ne da harshen labarci, gyaɗa kai Zaki ya yi sannan sukayi sallama ya fito daga asibitin kai tsaye kuma gida ya nufa da ita.
*FCT, ABUJA*
Hannunsa riƙe cikin na Ma'eesha ya ce"idan Allah ya kaimu gobe zan zo dan Allah eesha ki cire komai daga ranki karki bari wani abun ya samu lafiyarki" gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ta sauka daga motar ta shige gida, saida ya daina hangota sannan ya juya ya bar gidan zuciyarsa har sannan cike take da ɓacin rai koda wasa bai taɓa zaton abun zai zama haka ba da bazai taɓa barin Ma'eesha ba a wancen lokacin. Kallonta Farooq ya yi har ta ƙaraso gabansa tana shirin shige shi ya ce"Ma'eesha!" yanda ya faɗi sunan nata ne tagane something not good hakan yasa ta dawo ta tsaya amma bata ce komai ba, miƙewa tsaye ya yi yana kallonta ya ce"uban wane ya kawoki gida?" shiru Ma'eesha tayi masa dan idan ranta yana ɓace to bata iya magana, sosai shirun nata ya tunzura Farooq hakan yasa cikin ɓacin rai ya ce"kee dan ubanki ni nake miki magana kina jina?" wani kallo tayi masa sai kuma ta haye sama da sauri batareda ta bashi amsa ba, kwafa Farooq ya yi ya tsaya for some minutes sai kuma ya bi bayanta.
Kwance ya tarar da ita sai rusa kuka take kamar wacce aka cewa Mami ko General ya mutu, cikin ɓacin rai Farooq ya ce" bari na sanar dake wani abu duk ranar dana sake ganinki da wannan guy ɗin wlh sai na lahira ya fiki jin daɗi sai na ɓata miki rai fiyeda tunaninki ki dinga kula ɗan iska yaro saboda kinason jawo mana abun magana" a fusace ta mike tana kallonsa cikeda tsiwa take cewa" wlh saina kulashi babu ruwanka da wanda zan kula da kuma wanda bazan kula ba abinda nakeso shine wanda zan yi ba wanda kai ka zaɓamin ba tunda kai ba ubana bane nayi maka biyayya a baya wacce hakan ta jefani cikin wani hali har yanzu kuma ban fita daga cikinsa ba saboda haka wannan karon bazan ji maganarka ba indai akan Khalil ne" ta shige toilet tana buga ƙofar da ƙarfi. Kwafa ya yi sannan ya juya shima ya fita daga dakin yana buga ƙofar, jingina tayi da kofar banɗakin ta fashe da wani sabon kukan inama bata bi Father ba, inama tayi zamanta a gida wataƙila bataga abinda zai tayar mata da hankali ba inama ace mafarki take wanda zata farka yanzu nan, ganin lokaci na tafiya yasa ta ɗauro alwala ta fito tayi sallah sannan ta kwanta kan gado ko zata samu sauƙin abinda takejin yana yi mata yawo cikin ranta.
*Al Olaya residence*
Da mamaki Zaki yake kallon tarin motocin da suka yi parking harabar gidan taɓe bakinsa ya yi sai kuma ya ɗauko Muhaira wacce har sannan take bacci ya shiga takawa da ita cikeda isa. Turus ya yi sanda ya shiga parlon saboda idanu biyu da sukayi da Dmash wanda yake zaune kan kujera shida tawagarsa a gefe, yana ganin ya shigo ya miƙe tsaye kana ganin fuskarsa kasan ransa a ɓace yake yana zuwa bai yi wata wata ba ya sauke masa lafiyayyen mari a fuska ji kake tassssss, runtse idanuwansa ya yi lokaci ɗaya jijiyoyin kansa suka tashi above 2mins kafin ya buɗe idanunsa yana kallon Dmash wanda yake tsaye gabansa da sauri Muhaira wacce ƙarar marin ya tasa ta fashe da kuka tana rungumeshi ta ce"Papinaaaa" gam Zaki ya riƙeta a jikinsa yana kallon Dmash ya ce".
*Dommmmmmmmmmm😂*.
# *Unconditional love*
# *Trafficking*
# *Incident*
# *Destiny*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!âœï¸*.[8/8, 8:11 PM] NanameeraðŸ˜âœŒðŸ»: *BA ITA BA CE!..💖💖*
*Nanameera*.
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 11```
# *The incident*