Sashe 12
Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taɓe baki Tyha tayi tana kallon Abra ta ce"wai dan Allah me kike nufi ne?, nifa inason Taj kuma zanyi duk abinda ya umarceni then what's ur problem?" girgiza kai Abra ta yi ta ce"ke ai saboda bakida hankali yasa kk gama yarda dashi kwata-kwata bakisan kanki ba bakiga gatan da Zaki ya yi mana ba, yaƙi siyar damu kamar yanda ya saba siyarda mata ya killacemu cikin gidansa sannan ya sakamu a makaranta dan mu samu kyakkyawar rayuwa amma ko kaɗan bakiga wannan ba kin gwammace ki cigaba da iskanci nidai wlh yanda Allah ya rufa mini asiri ya rabani da wannan rayuwar na barta har abada zan cigaba da karatuna dan nasan watarana zai amfaneni" tsaki Amrish ta yi ta ce"ai sai kiyi ta yin karatun mukam saidai idan bamu samu masu tayawa ba amma muddin muka samu wlh sai munji daɗin rayuwarmu" murmushi Tyha ta yi tana kallon Amrish ta ce"faɗa mata dai ni kunsan wane a target ɗina?" girgiza kai suka yi ta yi wannan murmushi tana cije baki ta ce"Zaki!" da sauri duk suka kalleta sai kin suka tuntsire da dariya haɗe rai ta yi Khady ta ce"lallai bakida hankali taɓ ke a ganinki Zaki zai kulaki?, to ni tunda nake a tarihi ban taɓa jin ya kula wata mace bama iya kaci shidai akawo masa ya siyar ko ya bada haya amma bansani ba ko sai dare ya yi tashi take zuwa" dariya suka yi duka ta ce"aikuwa ku zuba idanu kuga in sha Allah sai haƙata ta cimma ruwa sai nayi rayuwa a apartment ɗin Zaki" mikewa Abra ta yi ta ce"na fuskanci bakuda abunyi shiyasa kunga tafiyata school" da harara suka bita har ta fice daga parlon sannan Amrish ta ce"wai ke nawa Taj yake baki ne?" haɗe rai Tyha tayi ta ce"ina ruwanki banson gulma ke" murmushi tayi ta ce"nifa ina son guy ɗin nan dan shima ya haɗu" wani kallo Tyha tayi mata kafin ta miƙe batace komai ba ta shige bedroom ɗin. Ganin yanda take binsa da kallo yasa ya haɗe rai yana kallonta ya ce"bar kallona" murguɗa masa baki ta yi ta ce"to kai ya akayi kasan ina kallonka", baki buɗe Zaki ke kallonta da alama sai ya koyawa yarinyar nan hankali, ajiye turaren hannunsa ya yi ya ƙaraso gabanta yana kallonta sai kuma ya nemi waje ya zaune da hannu ya yi mata alama da tazo aikuwa ta tashi babu musu ta ƙarasa har zata zauna a ƙasa ya riƙe hannunta ya zaunar da ita kan cinyarsa turo baki ta yi cikin gunguni ta ce"nidai Allah kabari banason iskanci" ware idanunsa ya yi ya tamke fuska kamar bai taɓa dariya ba, tattausan hannunsa ya sanya kan lips ɗinta sosai ya yi laushi taɓe baki ya yi sannan ya murza da ƙarfi kuka ta saki tana yarfe hannunta ƙara murɗewa ya yi da duk ƙarfinsa. Kuka take son yi amma yaƙi bata damar hakan aƙalla yakai wajen 5mins sannan ya saki bakin yana jingina da jikin kujerar, rushewa tayi da kuka jin yanda bakinta yake raɗaɗi yayi wani irin jaa lumshe idanunsa ya yi above two minutes yana jin kukan nata ganin tana son rikita kwakwalwarsa yasa ya jawota ya matseta a faffaɗan ƙirjinsa luf tayi kamar bai rufe komai ba dan kwata-kwata Muhaira batada ƙiba, a hankali kamar mai koyan magana ya ce"shii...shiiiiiii ya isa haka" tura baki tayi gaba tana hawaye ɗago fuskarta ya yi ya ce"what's ur name?" shiru tayi masa ya haɗe ya ce"I'm ur mate?" girgiza kanta ta yi cikin shashshekar kuka ta ce"Muhaira" harararta ya yi ya ce"Malama ur real name" zumɓura baki ta yi ta ce"A'ishah" sakinta ya yi ya ce"ɗagani" ƙuri tayi masa da idanu ya ce"ta Allah ba taki ba kike wani kallona witch kawai" harararsa tayi ta ce"wlh ni ba mayya ba ce" girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce" rashin kunya kike min ko?, zanyi maganin bakin rashin kunyar" turo baki gaba tayi ya kai hannu zai riƙe bakin da gudu ta tashi daga jikinsa takoma can bakin ƙofa ta tsaya.
Murmushin mugunta ya yi ya ce"zan kama kine yarinya sai kin raina kanki" gwalo tayi masa tana dariya, kallonta ya yi tayi yadda dariyar tayi mata wani masifar kyau taɓe baki ya yi ya ce"aljana" sannan ya miƙe bai sake bi ta kanta ba ya yi waje.
*9ja*
*Prime University, kuje, FCT Abuja*
*10:40am*
Tafiya suke tana basu labari sai dariya suke banda Ma'eesha wacce ta haɗe ranta kamar bata taɓa dariya ba, lura da haka yasa Fateema ta ce"takwara what's wrong with you?" numfasawa Ma'eesha ta yi ta ce"bakomai kawai bana jin daɗi ne, nd inason naje gida" murmushi Fateemah ta yi ta ce"kedai ki daina zurfin ciki wlh, ko zaki ɓoyewa kowa wani abu ai ni nayi zaton zaki iya faɗamin dan Allah talk to me dear" kallonta Ma'eesha tayi hawaye kan fuskarta ta ce"Takwara ina cikin matsala bansan ya zanyi ba kuma bansan wa zan faɗawa ba hankalina a tashe yake" tsayawa Fateemah tayi tana kallon Ma'eesha ta ce"kin barni cikin duhu Ma'eesha faɗa min mene ne ya dameki?" share hawayen fuskarta ta yi ta ce"bari muje gida dan Allah" numfasawa tayi ta ce"to shikenan" suka cigaba da tafiya dan fita daga makarantar. Da sallama ta shigo parlon babu kowa gidan shiru kamar ruwa ya cinye da alama Mami ma ta fita ne, riƙe hannun Fateemah tayi suka shige apartment ɗinta, saida ta rage kayan jikinta sannan ta zauna da sauri Fateema ta ce"yanzu faɗa min" ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce"wlh nakamu da soyayya ne kuma da ɗan uwanmu gashi bansan taya zan tunkareshi da maganar ba, Fateemah bantaɓa jin son wani ɗan adam irinsa ba nikaina bansan yaushe nafara sonsa ba tun ina ƴar ƙaramar yarinya rabonsa da ƙasar nan, kuma har yanzu bai dawo ba amma ana saka ran nan bada jimawa ba zai dawo yanada mata harda ƴa yanzu ma anyi masa kucciya ne shine yabar ƙasar gaba ɗaya rannan Mami ta nuna min hotonsa tun daga ranar ban sake bacci mai daɗi ba kullum shi nake mafarki bansan ya xanyi ba takwara dan Allah ki taimakeni..." Ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka mai ban tausayi. Riƙe hannunta Fateemah tayi tana goge mata hawayen fuskarta ta ce" ya isa haka ƙawata, insha Allah za ki zauna dashi matsayin mijin aurenki karki sanyawa kanki damuwa kinsan yanayin lalurarki, kinada buƙatar kulawa ta musamman Ma'eesha dan Allah karki sanya komai cikin ranki yanzu yaushe ne ake saka ran zai dawo?" numfasawa ta yi ta ce"Mami bata faɗa min ba amma ni inason kafin ya dawo naje Masarauta dan inada buƙatar haɗuwa dashi" murmushi Fateemah tayi ta ce"shikenan karki damu zan taimaka miki in sha Allah kawai abinda ke zaki yi yanzu shine kiyi ƙoƙari ki gano sanda zai dawo ƙasarnan daga nan komai zai zo da sauƙi in sha Allah" rungumeta Ma'eesha tayi tana dariya ta ce"Nagode sosai takwara Allah ya barmu tare" tana murmushi itama ta ce"Ameen takwara, yanzu dai ba wannan ba kenan bazaki bawa Sir Najeeb dama ba?" harararta ta yi ta ce"nifa koda wasa bai taɓa burgeni ba wlh kuma har ma Father ya ce zai sameshi ya faɗa masa ya rabu dani akanme taɓ" dariya Fateema ta yi tana kallon ƙawarta ta ta ce"taɓ lallai ma ke ɗin nan maganar har wajen Father taje lallai abun naki ya girmama" miƙewa Ma'eesha tayi ta ce"uhnn naki wasane bari na kawo mana abinci".
*FAROOQ POV*
Murmushin takaici ya yi ya ce"Mommy nifa abun nan ya isheni nagaji kuma haba dan Allah duk sanda mukayi attempting nayi wani abu sai aikinmu ya ɓaci yanzu dan Allah ya zamuyi Mommy nifa nagaji da zama ƙasan General sonake duk dukiyar ta dawo ƙarƙashin ikona, sannan ya zamuyi da Ma'eesha? yarinya nema take tafara bamu ciwon kai bansan wace mai kama da ita wacce har ni kaina banganesu ba amma dole akwai wani abu a ƙasa saboda haka yakamata tun wuri musan abunyi idan ba haka ba zamu tashi a tutar babu." shiru Mommy tayi dan itama abun ya fara fin ƙarfinta tsawon shekaru sun kasa cimma komai kullum sune suke faɗuwa yaushe zasu yi nasara akan General ne??, ganin taƙi cewa komai yasa ransa ya fara ɓaci ya ce"Mommy naga baki ɗauki abun nan serious ba to bari ni zan ɗauki matakin daya dace tunda ke kin gaza" ya juya ya fice yana buga ƙofar, da kallo Mommy ta bisa sai kuma ta girgiza kai kwata-kwata tarasa me zatayi akan al'amarin duk wata dabararta ta ƙare idan mallaka ce ta saba da mallake General kuma Allah da ikonsa ya fita shiyasa ma ita tabar layin malamai dan da ace zasuyi aiki da ba'a kawo wannan lokacin ba da wannan tunanin ta kwanta dan gaba ɗaya agajiye take.
"Ma'eesha!! Ma'eesha!! Ma'eesha!!"
"na.. na'am Mami"
Kallonta Mami tayi ta harɗe hannayenta a ƙirji sunkuyar da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta, ƙarasowa Mami tayi ta dafata tace"kedawa Ma'eesha?" rungume Mami tayi tana fashewa da kuka, shiru Mami tayi tana shafa mata bayanta sosai tayi kuka jikin mahaifiyar tata sannan ta ɗago Mami ta ce"now tell me meyake damunki kwana biyu?" murmushi ta yi tana goge hawayen nata ta ce"kawai ji nayi inason nayi kuka Mami" wani kallo Mami tayi mata wanda ya sanya tasha jinin jikinta. Kama hannunta Mami tayi ta jata gefen royal bed ɗin suka zauna cikin sanyin murya ta ce"Ma'eesha kinsan bakida wacce ta fini duk duniyar nan, ni ce ya kamata nazama abokiyar hirarki da kuma shawararki saboda haka kar kiji komai ki sanar dani damuwarki please" riƙe hannun Mami tayi ta ce"Mami kinsan da akwai wani abun zan sanar daku wlh babu komai kawai nima banajin daɗi ne amma babu abinda aka yimin wanda zai sa ku shiga damuwa kawai ku tayani da addu'a" numfasawa Mami tayi ta ce"tunda kin ce haka shikenan Ma'eesha Allah ya yaye miki abinda yake damunki" murmushi tayi ta ce"Ameen Mamina".
*RIYADH*
*Al-Takhasosi Residence*.