← Book details Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 29

Sashe 18

Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a firgice ta buɗe idanunta tana kallon Mami sai kuma ta tashi zaune kallonta Mami tayi ta ce"mene y sanya ki bacci haka? har wajen 9am bakiyi sallar asuba ba?" hamma tayi ta ce"wlh Mami kaina ne yake ciwo tun jiya to banyi bacci da wuri ba shiyasa na makara sorry" girgiza kai Mami tayi ta ce"gashinan idanunki sun kumbura hala kuka kika yiwa ciwon kan?" turo baki tayi Mami ta girgiza kai ta ce"Allah ya shiryeki, maza kiyi sallah ki fito ki ci abinci sai a kira doctor yazo ya dubaki" gyaɗa mata kai tayi sannan ta tashi ta shige toilet ita kuma Mami ta yi waje. Kasancewar ranar Saturday ya sanya babu makaranta tana zaune wajejen 2:30pm Mommy ta fito, kallonta ta yi sai kuma ta ce"Mommy har za ki tafi?" gyaɗa mata kai Mommy tayi tana murmushi ta ce"General ya hana da mun tafi tare" Ma'eesha ta kwaɓe fuska ta ce"ai yau babu school kuma ba kwana zaki yiba ko?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"please zan biki" girgiza kai Mommy tayi ta ce"A'a tunda ya hana ki haƙura kinsan halin babanki ki bari next idan zani sai mu tafi tare" buɗe baki tayi zatayi magana Farooq ya fito yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda black colour ya sanya hula zanna akansa sai zuba ƙamshi yake, shiru tayi da bakinta sai kuma ta miƙe ta ratsa ta jikin Mommy ta haye sama. Da mamaki Mommy take kallonta har ta haye sama sai kuma ta kalli Farooq wanda shima ya bi Ma'eeshan da kallo, taɓe baki ya yi sannan ya ce"Mommy muje" "lafiya dai meya haɗaka da ita?" bai cewa Mommy komai ba ya yi waje hakan yasa dole itama tabi bayansa.

Da mamaki yake kallon wanda yake tsaye jikin motar ya harɗe hannayensa a ƙirji sanya yake cikin wata dakakkiyar shadda Madam gezner ash colour ya ɗora zanna ash akai hannunsa maƙale da rollex ya sanya Glass baƙi a fuskarsa hannayensa zube cikin aljihu da alama akwai wadda yake jira, tsayawa ya yi a wajen kamar statue can kuma yaji an buɗe ƙofsr entrance ɗin gidan Ma'eesha ce ta fito cikin wata Eigypt Abaya purple colour mai manyan flower a jiki white colour ta yi rolling fuskarta da veil ɗin Abayar hannunta riƙe da wayarta iphone 13pro max. Ta gabansu ta shige ta ƙarasa inda yake tsabar baƙin ciki yasa Farooq ya shiga binsu da kallo kamar wani dolu can kuma ya ƙarasa wajen yana tafiya kamar wani damisa. Tsaye ya gansu yana mata magana cikin ɓacin rai ya ce"kee dan ubanki zo ki shige gida" wani kallon sheƙeƙe tayi masa sai kuma ta ce" bazan shiga ba wlh kuma karka sake zagin ubana" sakar baki ya yi yana kallonta sai kuma ya kalli Khalil wanda ya nuna baima san dashi a wajen ba ya ce"kai kuma idan kanaji da tashen iskancinka kasan inda zaka dinga zuwa kana yi saboda akwai inda idan kayi ranka zai ɓaci, ka fita a harkar yarinyar nan idan ba haka ba wlh sai na saka kayi dana sani mara amfani babu ruwanka da ita kaji na faɗa maka idan kuma kaƙi jin abinda na faɗa maka ta lallami to ka sani zanyi maka Yaren dana tabbatar zaka fahimta kuma..."

"Haba yaya Farooq maganganunka sun fara tsauri kasan irin abinda zaka dinga furtawa idan ba haka ba kuma wlh nima zan yi maka abinda bakayi zato ba ni ba baiwar ka bace inada Æ´ancin nayi abinda nakeso ko mahaifina bai takura min ba balle kuma kai ka fita a harkata"

Girgiza kai Farooq ya yi ya ce"ke ai banida lokacinki yanzu amma ki bari anjima na dawo saina baki mamaki" yana faÉ—in hakan yabar wajen kamar zai tashi sama. Da harara ta bisa sannan tayi kwafa kallonta kawai Khalil ya yi sai kuma ya furzar da nunfashi ya ce"eesha wannan bai dace dake ba, da hankalinki ki dinga ihuu kowa yana jinki" wani kallo tayi masa tana kwace hannunta daga nasa ta ce"ni cikani!" yanda tayi maganar cikeda tsiwa ya sanya ya yi murmushi ya ce" to laifin kaina ya dawo?" harararsa ta yi ta ce a zafafe"karka sake zuwa gidanmu dan ni bazan auri ragowar wata ba kaje ka kula da matarka wlh" baisan sanda ya tuntsire da dariya ba yana girgiza kai ya ce"

# *Ameenatou ce✍️*
# *BA ITA BA CE!*.
[8/9, 12:19 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖*

*Nanameera*.

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

```Page 12```

# *Love*

"Narasa yaushe kika koyi tsiwa eesha da dai ba halinki bane" turo baki ta yi ta ce"sanda ka yaudareni sannan nikuma na koya" girgiza kansa ya yi dan yasan rigima take nema, kusan two minutes sannan ya ce"munyi magana da Dad jiya kuma ya ce zai yiwa Father magana" zaro idanu ta yi tana dafe ƙirjinta ta ce"nashiga uku wace magana kenan?, ban fahimta ba?" murmushi ya yi ya ce"maganar aurenmu mana koda kinyi zaton wasa nake?" haɗe rai ta yi ta ce"yaya Khalil ka daina yimin irin wannan wasan wollah banaso" cikin tafiyarsa ta isa ya ƙaraso gabanta ya kama hannunta yana murzawa ya ce"eesha stop joking kinji kinsan Ina sonki nd kuma ni ne wanda Father ya yiwa alƙawari sbd haka dan Allah ki furamin asiri kar kice a'a" girgiza kanta ta yi tana zare hannayenta ta ce"A'a ya Khalil yanzu kai ba tsarana bane kada ka manta a wancen lokacin ba kayi aure ba sannan baka kai matsayin daka taka yanzu ba jiya ban samu nayi bacci ba saboda tunane-tunane dan Allah karka sake karyamin zuciya ka barni da abinda yake damuna yaya Khalil" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamar roƙo. Hankalin Khalil ya tashi dan abinda take faɗa daga zuciyarta yake fitowa tuni jijiyoyin kansa suka tashi cikin rawar murya ya ce"ees... eeshana dan Allah karki barni karki jiyamin baya ki taimaka ki kasance dani a karo na biyu ki bani dama nayi miki alƙawarin bazan yaudare kiba dan Allah ki taimaka" kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kanta tana dariya mai haɗe da hawaye ta ce" wlh bazan iya ba yaya Khalil kamar yanda na faɗa maka yanzu zuciyata akwai wanda take muradi saboda haka leave me mu cigaba da kasancewa matsayin ƴan'uwa wannan ya wadatar please" tana gama faɗar haka ta juya ta koma gida da gudu sbd kukan da yaci ƙarfinta. Dafe kansa ya yi cikin tsananin tashin ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Allah ka taimakeni ka sassauta zafin zuciyar Ma'eesha ko na samu salama" ganin yana ɓata lokaci kuma tayi tafiyarta yasa ya shiga motarsa ƙirar Honda Accord ya bar gidan. Girgiza kai Mami tayi cikin son rarrashinta ta dafata ta ce"mene ne nayin kuka Ma'eesha?, tunda har Khalil ya baki haƙuri ya kamata ace kin haƙura kinsan halinsa bashida wani mummunan hali to me kike nema wajen namiji?" ɗagowa tayi daga cinyar Mami cikin kuka ta ce"Mami bazaki gane irin zafin da zuciyata ke yimin ba, Mami inaji kamar zan mutu yaya Khalil ya auri wata bani ba bazan taɓa samun kwanciyar hankali ba idan na aureshi saboda bazan iya jurar ganinsa da wata Macen ba" murmushi Mami tayi tana goge mata hawayen fuskarta ta ce"Ma'eesha kenan karki kuskura ki saka a ranki cewa ke mijinki naki ne ke ɗaya yanada damar aurar wacce yakeso matuƙar yanada halin riƙeta kuma daga gidanku kake fara koyar abu ni kaɗai ce a gidan nan?" girgiza mata kai ta yi, Mami ta ci-gaba da faɗin"saboda haka kima daina kawo wannan tunanin a ranki ki maida komai ba komai kinsan babu abinda zai hana babanki ya bawa Khalil aurenki sai ikon Allah sbd haka ki daina wannan damuwar matuƙar kin riƙe mijinki yanda ya kamata to bazai taɓa kufce miki ba koda ace ku huɗu ne a wajensa" shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya Mami ta miƙe ta fita a ranta tana jinjina yarinta irinta Ma'eesha.

Da mamaki ya ƙara sa gaban gadon yana kallon yanda duk ta naɗe cikin bargo ya ce"Ramlah!! Ramlah!! Ramlahhh" da sauri ta miƙe daga kwancen tana murza idanunta sai kuma ta langwaɓar da kai ta ce"wlh doctor banajin daɗi zuciyata zafi take yimin" zama ya yi gefen gadon sai kuma ya ɗora hannunsa kan ƙirjinta dan jin yanda zuciyarta ta ke bugawa, janye hannunsa ya yi yana miƙewa tsaye ya ce"bari na kawo miki drugs ɗinki da ruwa sai kisha" gyaɗa masa kai tayi sannan ya juya ya fita murmushi ta yi sannan takoma ta kwanta. Zaune ya samu Mommy tana kallon wani series da ake haskawa bai ce mata komai ba ya shige parlonsa ko minti biyu ba ayi ba ya fito hannunsa riƙe da ledar drugs kallonsa Mommy ta yi sai kuma ta ce"subhanallahi wace babu lafiya?" yana duba ledar drugs ɗin ya ce"wai Ramlah ce bata jin dadi shine zan bata magani" okay Mommy ta ce sannan ya juya ya koma bedroom ɗin, kwafa Mommy ta yi tana cewa"yaro baisan wuta ba sai ya taka jira zakaga abinda na aikata" sai kuma tayi wani kyakkyawan murmushi ta cigaba da kallonta cikeda nishaɗi. Sai bayan sallar isha'i sannan suka shigo gidan babu kowa a parlon daman kuma haka suka so kawai kowa ya yi part ɗinsa, taɓe baki Ma'eesha tayi dan tana kallo suka shigo suna sanɗa kamar wasu munafukai haka kawai taji yanzu bata sonsu musamman ma Farooq wanda take jin da tanada dama da tuni ta koreshi daga gidan murmushi tayi tana sipping coffee ɗinta Saboda tunawa da yaya Khalil da tayi idan ta ce bata sonsa to kowa zai gane ƙarya take dan ita kanta tasan tana mutuwar son Khalil kawai tana jin haushin auren da ya yi ya barta ne. Saida ta shanye tass sannan ta fito daga kitchen ɗin a hankali ta shiga tafiya saboda duhun daya mamaye parlon haka kawai taji tsoro ya rufeta.
Chapter 18 · 0% Book details