Sashe 2
Ba Ita Ba Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Durƙushe take gabansa ta zuba masa idanu tana kallonsa ƙaramar yarinya ce ba zata shige 4 to 5yrs ba tana sanye da kayan Fulani Blue colour as usual gashinta dake zube a gefenta wanda aka kalbaceshi irin manyan kalbar nan guda biyu yabi da kallon a hankali kuma ya sake lumshe idanunsa shi kaɗai yasan irin tsananin azabar da yake ji, kamar zatayi kuka take kallon mahaifin nata cikin wata siririyar murya mai Matuƙar zaƙi da ɗaukan hankali take cewa"Papina sannu zaka samu sauƙi kaji sannu dan Allah" bata rufe bakinta ba aka ɗaga labulen wanda ya kasance asabari ne suka shigo da sauri kuma cikin ɗaga murya Dada ta ce"Baba kura zo ki dubashi aradu mun higa uku ya Gani sannu Allah zai tashi kafaɗunki" da sauri wanda take cewa Baba kuran ya ƙaraso yana zuwa ya zube a gabansa hannunsa ya kai ya taɓa wuyansa sosai yaji zafi a jikinsa hakan yasa duk hankalinsa ya ƙara tashi a matuƙar razane kuma ya miƙe ya fice daga cikin bukkar, da kallo suka bisa kafin Dada ta kalleta da idanunta wanda suka sauya launi ta ce"kai Muhaira ɗebo ruwa a bashi yasha" da sauri ƴar ƙaramar yarinya ta miƙe ta ɗauki ɗan ƙaramin jallan ruwan tayi waje saidai kafin ta fita ta juya a hankali tana kallon fuskarsa ga mamakinta sai taga shima ita yake kallo wani tattausan murmushi ya yi mata dukda yanda bakinsa yake a bushe wanda ke nuni da asalin ciwon da yake ciki a hankali itama ta mayar masa da nata kyakkyawan murmushi ya ilahy wani irin sihirtaccen kyau ƴar yarinya ta yi tamkar wata ƴar aljanu haka ubangiji ya yi mata kyau kwayar idonta blue colour ce irin mai hasken nan sai wani irin sheƙi suke saɓanin na sauran mutane da suka kasance baƙaƙe. Da hannunsa ya yi mata alama da tazo hakan yasa ta ajiye jallan ta ƙara sa gabansa ɗan ƙaramin hannunta ya kama a hankali kuma ya buɗe bakinsa wanda yawo yake shirin ƙafewa daga cikinsa ya ce"Baddon Papi!" da sauri ta ɗaga kanta tana kallonsa wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa kan kuncinsa da sauri ta saka ɗaya hannun nata tana goge masa kwaɓe fuska ta yi cikeda shagwaɓa ta ce"Papi kadaina kuka kaji dan Allahhhh" shafa fuskarta ya yi hannunsa na kakkarwa ya gyaɗa mata kai dan bakinsa ya yi masa nauyi, Bani kura ne ya shigo bukkar shida wani mutum a bayansa da alama kuma mai magani ne. Bayan sun zauna ya kalli Papi sai kuma ya kalli Muhaira dake gefensa ya ce"Baddo maza jeki gidana ki karɓon ƙwarya" miƙewa Muhaira tayi ta fice tana tafiya da a sauri a hankali kuma take waiwayen bukkar tasu.
Tafiya kawai take da sauri da sauri dan ko wasa bata tsaya ba haka har ta baro rugar tasu, kasancewar su a cikin gari suke ya sanya ta ɗan yi tafiya mai yawa kafin ta ƙaraso ƙofar gidan, "Wundo!! Wundo!! Wundo!!" turo baki Muhaira ta yi bata ce komai ba har sannan, da sauri ya'acca ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce"ke kam Muhaira bakida mutunci ko?, banda iskanci ki shigowa mutane gida babu sallama sannan kuma ji ana waye kinyi tsif abinki ko?" sosai yarinyar ta tsorata da tsawar da tayi mata bakinta na rawa ta ce"unn...uhhhmm...dan...daman Bani kura ne ya ce a bashi ƙwarya" tsaki ya'acca ta yi ta ce"shine zaki tsaya kina mana shashanci" sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba amma duk a tsorace take, shiga ɗaki ta yi ta ɗauko ƙwaryar ta mika mata, da sauri Muhaira ta karɓa sannan ta juya da gudu tayi waje, tsaki ta yi tana kallonta ta ce"shashasha kawai".
Da sauri ta shigo cikin bukkar hannunta riƙe da ƙwaryar saidai me?, babu Bani kura wanda ya aikata haka zalika babu mai maganin da aka ɗauko sai Dada wacce ke zaune gefensa banda kuka babu abinda take yayinda Papi aka rufeshi da wani tsohon bargon, da sauri ta ƙarasa wajensa tsugunawa tayi gaban Dada tana cewa"Dadana Papi ya yi bacci?" kallonta Dada ta yi amma bata ce mata komai, sosai idanunta sukayi jajur ko ba'a faɗa maka ba kasan ba ƙaramin kuka tasha ba, kuka ta fashe dashi tana murza idanunta da kallo kawai Dada ta bita dan ita tama gagara magana ganin Dada bata kulata ba har sannan yasa ta kwanta a wajen tana birgima, Bani kura ne ya shigo shida masu maza a bayansa suna zuwa kai tsaye inda Papi ke shimfiɗe suka nufa ganin yanda take kuka yasa Bani kura ya ce"Aishatu ke dawa?" daga yanayin muryarsa zaki fahimci irin damuwar da take tare dashi, da sauri Muhaira ta tashi jin ya kira sunanta ta ƙarasa wajensa har Sannan kuma kuka take ta ce"Bani koba Dada bace" janta ya yi jikinsa ya rashe mata hawayen fuskarta sannan ya ce "to kiyi haƙuri zauna anan" shiru tayi ta zauna a gefensa tana kallon bargon da suka rufe Papi.
Ƙarasawa suka yi bayan sun yaye bargon suka kamashi suka fita daga cikin bukkar duk wannan abun da ake banda kallo babu abinda Muhaira ke yi dan ita bata gane ba mene ne abinda ya faru ba, Dada kuwa ƙara sautin kukanta ta yi jikinta na wani irin kyarma, tashi Muhaira ta yi ta koma kusada ita ta zauna amma bata ce komai ba sai kallon mahaifiyar tata take, ita kuwa Dada tunanin yadda rayuwarsu zaka kasance take, tunanin rayuwar Muhaira take, zuciyarta cike take da tausayin tilon ƴar tata, tabbas ƙaddara ta riga fata domin Papi ya tafi ya barsu a lokacin da suka fi bukatarsa. Tunawa da wannan yasa ta sake rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kuwa Muhaira bata fahimtar komai ƙanƙantar shekarunta da kuma ƙarancin shekarunta sune suka yi tasiri wajen gazawa kwakwalwarta ta fahimtar da ita duk a tunaninta Papi ɗin wani waje zasu kaishi wanda zasu dawo mata dashi. Amma saidai abinda bata sani ba shine Papinta ya tafi kenan tafiyarda duk wanda ya yi ta baya taɓa dawowa,tun tana tambayar Dada ina Papinta har ta fahimci cewa Papinta ya bar duniyar a hankali mintuna ke komawa awanni awanni ke komawa kwanaki kwanaki ke komawa sattituka sukuma suke juyewa izuwa wattani wattani kuma ke juyewa izuwa shekaru, tafiya ta tafi a ƙalla Papi zai yi shekaru uku da barinsa duniya zuwa wannan lokacin kuma Muhaira tanada shekaru 8 a duniya.
Wani irin sanyin ake mai ratsa ɓargon da jijiya sanyinne irin wanda ke haddasa cuttukan musamman Asthma, pneumonia, sickler dama wasu ciwukan, safiyar ranar juma'a ce gabaɗaya rugar Jama'are tayi tsit kowa yana cikin bukkarsa da iyalansa, tsugunne take gaban wata tukunya wacce aka ɗorata akan dutsuna guda uku wanda suka zama sune murhun da take girkin akai sosai take haɗe jikinta yayinda numfashinta ke wani irin fuzga ita kaɗai tasan azabar da take ji amma kuma burinta bai shige ta gama damawa Dada kokon ba. Cikin mintuna ƙadan ta kammala ta juyeshi cikin wani tsohon kofi sannan ta tashi da gudunt ta shige bukkar, tana nan yanda ta barta a kwance idanunta a rufe suke amma ba bacci take ba ajiye kofin hannunta ta yi sannan ta shiga kamata tana faɗin" Dada tashi, tashi kinji na dama miki kokon tashi kisha sai kisha magani" dakyar Dada ta buɗe idanunta ta kama hannun Muhaira ta miƙe daga kwancen ɗora kan Dadar tayi akan ƙirjinta dukda nauyin da tayi mata amma ko kaɗan hakan bai dameta haka ta ɗauki kofin kunun ta kai mata bakinta, girgiza kai Dada ta yi tana riƙe hannunta ta ce"A'a Muhaira bazan iya sha ba akwai abinda nakeson na faɗa miki tabbas wannan cutar tawa bata tashi ba ce saida... wani irin jan numfashi ta yi tana saukeshi a hankali runtse idanunta tayi hawaye suka shiga rige-rigen sakkowa kan kuncinta alama ta yi mata data bata kunnenta a hankali Muhaira ta kara kunnen nata kusada fuskar mahaifiyartata dan taji me zata faɗa mata. Above 5mins tana yi mata magana zuwa lokacin kuma banda hawaye babu abinda Muhaira ke yi gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak batada wata sauran dabara zuwa sannan kuma bata iya fahimtar abinda mahaifiyar tata ke faɗa mata. Shirun da taji Dada tayi yasa ta kalleta wata irin razananniyar ƙara ta fasa wacce ta yi daidai da shigowar Falmata cikin bukkar da sauri ta ƙaraso tana kallonsu duka ganin yanda Muhaira ta ƙamƙame Dadan har sannan kuma kuka take yi kallo ɗaya Falmata ta yi mata tasan cewa Ubangiji ya karɓi abarsa, ikon Allah kenan babu yanda mutum ya iya kamar yanda Papi ya mutu haka yanzu itama Dada tabi bayansa
"Dadata! dan Allah dan Annabi ki tashi karki mutu ki barni banida kowa Dadaaaa...ki taimaka ki tashi Dada ko kinfi son nayi kuka har ƙarshen rayuwata?, banida kowa Dada kema kuma bakida kowa Papina ya tafi har yau bai dawo ba kema shine zaki bisa??? kenan duk baku sona? meyasa Dada?, me nayi muku?, ina zani yanzu? wane zai kula dani Dadaaaaa..." maganar ta tsaye a maƙoshinta sakamakon wani irin nauyi da zuciyarta tayi da gudu ta miƙe ta fita daga bukkar saboda wani irin amai daya tawo mata saidai me???? madadin amai na abinci ko kuma na ruwa wani irin guda-gudan jini ne ya shiga fitowa daga bakinta sai kuma ta faɗi nan ƙasa sumammiya.
Allah sarki rayuwa tabbas babu abinda ke ɗorewa sai ikon Allah cikin ɗan lokaci ƙalilan Muhaira tarasa iyayenta guda biyu wanda hakan shine mafarin ƙaddararta, tabbas labarin rayuwarta akwai taɓa zuciya, musamman daya kasance tanada ƙarancin shekaru Hakazalika kuma babu wani wanda zata kama ta ce wannan danginta ne kasancewar iyayen nata Fulanin tashi ne, tarasa gatanta tun tana jaririya sannan kuma ta sake rasa waɗanda suka maye mata gurbin wannan gatan data rasa ya zatayi??dawa zata rayu?? wace irin ƙaddara ce ke bibiyar rayuwarta??...
*17 years*.
*Maitama district, Abuja*
*No:113*.
*Mai Zamani pov.*