← Book details Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 33

Sashe 9

Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Da sauri ya 'karasa inda take ya fara lallashinta"Reyhana please am sorry bada sani na bane ban lura ba kinji".

    Ai kamar zigata yake, hannunsa ta tankwa'be ta juya zuwa d'aki.Kan gadon ta fad'a tayita rera kukanta.

     "Dan Allah kiyi shiru Reyhana please am sorry". Ahmad ya fad'a sanda ya zauna a gefenta.

       " Kana sani kayi kuma dama haushina kake ji tuntuni".Ta fad'a cikin kuka.

       "Meyasa zanji haushinki ,ki tashi komai ya wuce please bana son wannan kukan".

          " Ba haushina kake ba ka'ki d'aga kirana kasan zan fita yau".Cewar Reyhana.

           Shi se yanzu ma ya tuna da wata fita unguwa."Reyhana ai na manta sam, meyasa baki tunan ba? Kinsan bazanyi haka ina sane ba ko na 'kuntata maki".

    "Kuma wayata ba charge d'azu da kika kirani ,sanda naga missed call d'inki zanyi calling back wayar ta mutu please kiyi ha'kuri".

       Shiru Reyhana tayi bata sake cewa komai ba amma ta tsagaita da kukan.

    " Azizaty".Ya kira sunanta.

     Reyhana bata amsa ba ,jin tayi shiru ya sake kira.

     "Azizaty".

     " Uhmm".Ta amsa a ciki.

     "Kin ha'kura yanzu?" Ya tambayeta.

     Kai ta kad'a ba tare da tace komai ba.

      "Toh kinci abinci ?"

  Nan ma kai ta kad'a,hannu yasa ya d'ago ta a hankali.Fuskarta tayi sha'be-sha'be da hawaye.

     Idanta ta sauke 'kasa ,hannunsa  yasa ya goge mata hawayen ya d'ago da ha'barta.

     "Please look at me". Ya fad'a.

       A hankali ta kallesa sannan ta sake sauke idanuwanta.

       " Am sorry kinji".Ya sake fad'a.

        A hankali ta kad'a kai alamar ta ha'kura.

      "Ok smile".Ya fad'a.

       D'an guntun murmushi ta saki ba tare da ta kallesa ba.

       " Maman Baby saura na baby baki masa murmishi ba ko bakisan tana kallonki ba duk abinda kike"?"

     Jin ya ambaci haka ta d'ago da sauri "Tana kallona kuma? Yana de kallo na".

       " Auu! Naki choice d'in kenan ? Nide itace ba shi ba".Ahmad ya fad'a.

      "Toh nikuma ba haka ba ". Cewar Reyhana.

     "Ok then we shall see ,nan bada dad'ewa ba". Ahmad ya fad'a tare da jawota jikinsa yana shafa bayanta.

          Nan take suka mance da fad'an kamar basu ne ba.

               ***
    Mommy sautin muryarta ne yake tashi a part d'inta kana doso wajen zaka jiyo muryarta.

    Waya take da Anty Asma'u kuma hira duk bata wuce ta Reyhana ba.

      " Yanzu wayar tata ta siyar ta bashi kud'in kenan?" Cewar Anty Asma'u bayan da Mommy ta labarta mata komai.

    "Eyyi taga zata iya se tai tayi". Mommy ta fad'a.

     " Ni yarinyarnan ma gani nake ciki gareta ".Mommy ta fad'a.

     " Ahaf ai na ayyana ,yanzu a wannan 'kuntacaccen gidan zata bari ta samu ciki".Cewar Anty Asma'u.

      "Eyyi bata da tunani ai ,ni naga d'an 'beran da za'a haifa gafa yadda take d'ura abincin lami a cikinta ko kifi babu a abinci ya kike tunani yaro ze kasance". Mommy ta fad'a tana kumfar baki.

     " Hmm Allah de ya sawwa'ke ,amma fa baza ki barta ta haihu a gidanta ba" Anty Asma'u ta fad'a.

      "Ahh dama yaushe ai dolensa ta dawo gida idan ba so yake jininta ya 'kafe ba kuma". Cewar Mommy.

       Sageer tun shigowarsa yake jin d'aga muryar Mommy ,kan wata kujerar d'akin ya zauna zaman jira ta gama wayar.

        " Mommy ku baku da zance se maganar Reyhana koyaushe Reyhana kubarta mana"Sageer ya fad'a bayan data gama wayar.

      "Dalla rufen baki, kai haryau yarone baza ka gane mey muke nufi ba daga kai har Reyhana d'in". Mommy ta fad'a.

       " Kuka san gaba mey ze faru".Sageer ya fad'a.

      "Koh? A hakan da certificate d'in diplomar zeyi arzi'ki?" Cewar Mommy.

       "ARZI'KI RABO de". Ya fad'a.

       " Kai kasani nide ina sa'kona dana aikeka idan bashi ya kawo ka ba ka iya bani space".Mommy ta fad'a.
      "Gashi". Ya mi'ka mata kud'in daya ciro mata a ATM.

             Yana bata ya fita ya koma sashensa...

AR²💖

     Please Read,comment and vote. Luv u all😘😘

Jasko💕 
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍

*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 0⃣9⃣

    Yau Reyhana tun 10:30am ta gama komai dan yau gida zata da wuri Ahmad dama yau alhamis  yana azimi shiyasa ko girkin rana batayi ba wajen 11:37am ta gama shiryawa.

      Sanda ta shiga gida Abba ze fita nan ya tsaya suka gaisa tukun ya fita.

       Tana shiga ciki inno ta gani tana goge-gige a parlour.

       "Ina kwana inno".Reyhana ta gaidata.

       " Reyhana kece a gidan? Lafiya lau ".Ta amsa.

        " Su Mommy suna d'aki ne?" Ta tambaya dan taga bakowa a parlourn.

        "Eh Walida ce bata da lafiya suna d'akinta dan basu jima da dawowa daga aibiti ba". Inno ta fad'a.

       " Tohh! Allah ya sawwa'ke bara na hau saman".Reyhana ta fad'a.

      A kwance ta isketa a gado se fad'a ake da ita wajen shan magani.

       Tana ganin Reyhana ta fara 'ko'karin tashi zaune.

      "Yi zamanki keda bakida lafiya". Reyhana ta fad'a.

         " Mommy ina kwana".Reyhana ta gaisheta bayan ta zauna a wata kujera dake d'akin.

        "Lafiya ". Mommy ta amsa.

         " Ya jikinnata ?"Reyhana ta tambaya.

        "Da sau'ki,tashi tayi da zazza'bi seda aka kaita asibiti". Cewar Mommy.

       Su Ikram da Sageer ma suka gaisa da ita.

  Bassam kuwa yana makaranta." Walida kisha magani kinji koh bakya so ki warke?" Reyhana ta fad'a.

     Kai ta girgiza alamar "A'a".

      " Toh maza tashi kisha".Ta fad'a.

      Da 'kyar aka samu tasha maganin sannan ta samu ta sake shan tea daga baya tayi bacci.Se lokacin ta barsu suka sarara dan Walida bade raki ba.

       Sageer ya wuce d'akinsa haka Ikram ma.Reyhana kuma d'akin Mommy.

       "Reyhana meyasa kike cutar rayuwarki?" Mommy ta fad'a .

        "Yanzu har takai ga kin fara sayar da abubuwanki ,wannan shine rayuwar da kika za'bawa kanki?" Cewar Mommy ranta a 'bace.

         "Mommy fa daman ta fara bani matsala wayar". Reyhana ta fad'a.

        " Bawani nan 'karya kike,nasan mijinki kika bawa kud'in".Mommy ta fad'a.

        Reyhana shiru tayi ta sunkuyar da kai dan ta rasa abin fad'a.

          "Ke bazaki ta'ba gane mey nake nufi ba ,ki duba kiga tun ba aje ko ina ba kun fara shiga cikin wannan halin ina ga kun fara yara,Ahmad sam ba tsaran aurenki bane baki dace dashi ba baze iya ciyar dake ba a haka kuma kike tunanin kuyi 'ya'ya dashi".

         Reyhana kwallar da take ma'kale take ta zubo kalaman Mommy suna tsorata ta.

      " Mommy umma ce fa bata da lafiya shine na siyar dan akaita asibiti".Reyhana ta fad'a murya na rawa.

        "Ummansa ce ba lafiya? Yanzu kinzamo kece mijin kenan". Cewar Mommy.

        " Reyhana ina tausaya maki amma ke gani kike kamar na matsawa rayuwarki ki".

       Sallamar Ikram ce tasa suka katse maganar da suke ,da sauri Reyhana ta goge hawayen idanuwanta.

        Mommy tashi tayi ta bassu suna ta hirarsu.Daga bisani suka shiga kitchen Ikram da Reyhana suka soya wainar flour dama gashi Walida tana so.

        Kasancewar Ahmad yana azumi yasa ta koma gida wajen 4pm saboda had'a masa abin shan ruwa.

         Mommy da hankalinta ya kasa kwanciya da al'amarin Reyhana yasa Abba yana dawowa ta zauna dashi ta zayyane masa komai.

       "Toh ke yanzu mey kike so nayi?" Abba ya tambaya.

       "Haba Abban Reyhana taya zaka fad'i haka kai da kanka ya kamata ka nemo abun yi". Mommy ta fad'a.

      " Nide na fad'a maki ba ruwana a cikin wannan zancen,ki bar yarinya kin'ki ke kullum complain tunda mike da ita bata ta'ba kawomin 'karar yarannan ba suna zaman lafiya kuma sena sa baki".Abba ya fad'a.

      "Aikuwa ni ina da abinyi tunda kai baza kace komai akai ba". Mommy ta fad'a.

      " Mey kike tunanin yi?" Abba ya tambaya yana jiran amsarta.

      "Ya sawwa'ke mata ,bazan bari ina kallo 'yata ta zauna a 'kuntatacciyar rayuwa ba". Mommy ta fad'a.

        " Ya sawwa'ke mata fa kika ce? Anya kuwa kina da tunani ?" Cewar Abba yana mamakin kalaman Mommy.

      "Toh wani abune? Ai gaskiya na fad'a baze iya ri'ke mana 'ya ba dan haka seya rabu da ita bamu gaji da ita ba".

      " Kinga kunnena baze iya d'aukan wannan abun ke iya fita ko kiyi shiru".Abba ya fad'a.

      Mommy bata sake cewa komai ba ta mi'ke tai ficewarta.Abba bayanta yabi da kallo kawai ya girgiza kai.

                ***
           Akwai lokacin da Mommy ana wani suna koda aka fad'a wa Reyhana ba ta samu zuwa ba saboda kud'in transport kuma bawai ta fad'a wa Ahmad ba yace baida kud'i,kawai ta san baida isassun kud'i shiyasa batai masa maganar sunan bama.Mommy kuwa tasha haushi nanma haka bata gaji ba seda ta fad'a wa Abba ita a lalle seya d'au action akai.

      Tun Abba baya biye zancen har shima abun ya fara damunsa kuma bawai ya fara 'kin Ahmad bane kawai de 'yar tasa ya fara tausayawa amma kuma sam be nuna wa Mommy hakan ba balle Reyhana.

      Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa da dad'i ba dad'i, Reyhana cikinta ya cika wata 8,zama da 'kyar tashi da 'kyar.Yanzu ta dena cin d'ata, mitimis da albishir ta tusa a gaba.

        Mommy kuwa tana kan bakatta na dawowar Reyhana gida,ita kuwa Reyhana ko Ahmad ma batayi wa maganar ba ta san baida ra'ayin mace ta koma gida wanka.

         Reyhana tana d'aki tajiyo 'karar wayarta a sitting room, koda taje dubawa taga wanda ke kira taga Mommy ce.Se a karo na biyu ta d'aga kiran.

         "Ina yini Mommy". Reyhana ta gaisheta.

         " Lafiya lau,bakya kusa da wayar koh?"

         "Eh". Reyhana ta amsa.

          " Toh ya maganar komowarki ,ko har yanzu baki fad'a masa ba?" Mommy ta tambaya.

        "Eh amma yau zan fad'a masa". Reyhana ta amsa.

         " Toh kide fad'a masa dan ba ruwana kika haihu a gida dan kinsan ni bani da wacce zan kawo maki atoh".Mommy ta fad'a.

     "InshAllah zan fad'a masa". Ta amsa.

    Daga haka sukai sallama ,Reyhana tunanin yadda zata 'bullo masa da wannan maganar take.

            ***

Ahmad kuwa a gurin aiki Umma ta kirasa take fad'a masa ya biyo ta gidanta.

    Dama lokacin tashinsa yayi dan haka ya biya gidanta.

     Bayan sun gaisa take ce masa Mommy ta kirata d'azu.

      " Mommy ce ta kiraki?"

      "Ehyi ta fad'a min Reyhana gida zata koma". Umma ta fad'a.

      " Gida kuma?" Ya tambaya cikeda mamaki.

      "Ehyi a can zata haihu". Ta amsa sa.

     " Toh ai ni bata fad'a min ba".Cewar Ahmad ransa a d'an 'bace.

      "Toh gashi mahaifiyarta ta fad'a".

      " Nifa bana son komawa gidannan fa".Ahmad ya fad'a.
Chapter 9 · 0% Book details