← Book details Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 33

Sashe 7

Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Seda ta amayar da abunda ke cikinta kaf,Ahmad ne ya wanke wurin ya taimaka ta koma d'aki.

Kan gadon ta zauna ta jingina Ahmad yana mata sannu.Daya ta'ba goshinta yaji ba zafin.

"Kin dena jin sanyin?" Ya tambayeta.

"Eh". Ta amsasa.

Kwanto da kanta jikinsa yayi yana shafa bayanta,a haka bacci yayi gaba da ita.

AR²💖

*Need your comments, votes and share.Love u all😘*

Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍

*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 0⃣7⃣        Ranar Reyhana wuni tayi a kwance ,Ahmad se ha'kura yayi da fita. Jollof taliya ya dafa musu taci kad'an ,shima be iya yaci dayawa ba.

Washegari da safe ya taimaka mata tayi wanka ta shirya.

"Reyhana tashi fa zaki mu tafi asibiti". Ahmad ya fad'a.

" Mu bari ze fa sauka zazza'bin".Reyhana ta fad'a murya tana rawa.

"Ba shawararki fa nake nema ba tashi zaki nace mu tafi yanzu". Ahmad ya fad'a in serious turn.

Tana turo baki ta tashi ta zira hijab da takalmi.A hanya yana mata hira ta'ki ko tanka sa.

Reyhana ba wani abu yasa bata son asibiti ba sedan tana tsoron allura(kamar ni😂).

Suna isa asibitin zuciyarta na sake tsorata a sanyaye ta shiga gun likita.

Koda ta gama zayyane masa abunda yake damunta test na mp da PT ya rubuta mata.

Data fito Ahmad yana tamabayarta takardar kawai ta mi'ka masa, nan suka tafi laboratory. Wajen blood collection da'kyar ta yarda aka d'auka jininta tund PT d'in serum ne.

Bayan kamar 20min aka bata result tana fitowa ko ta kansa bata bi ba.Yana mata magana amma ta'ki kula sa illa hannunta data ri'ke kamar wacce ta karye. Hakan yasa kamar yayi dariya amma dan kar ya had'a mata zafi biyu ya maze kawai.

Koda ta bawa doctor result d'in daya duba wasu 'yan magungunan ya rubuta kad'an sannan yace.

" Congratulation".

Kallonsa ta soma yi cikeda rashin fahimta.

"Kina d'auke da juna biyu,zaki je yanzu wajen scanning ga wasu maguguna da na rubuta maki Allah ya 'kara lafiya". Doctor d'in ya fad'a.

      " Ameen nagode".Reyhana ta fad'a bayan ta kar'bi katin.

    Lokaci guda tsoro da farinciki ya ziyarce ta,tana fitowa Ahmad ya 'karaso inda take "Azizaty me doc yace?"

       Mi'ka masa katin tayi ba tare da tace komai ba.

       "Azizaty wannan kike 'boyewa daman?" Ahmad ya fad'a fuskarsa d'auke da murmushi hatta ha'koransa seda suka fito.

     D'an waigar da fuska tayi tace"Nima ai d'azun ban duba ba ".

       " Maman baby me tsoro".Ahmad ya fad'a.

      Tafin hannunta ta d'ora a bakinta tana murmushi amma har lokacin bata waigo ba.

      Wajen scanning d'in suka 'karasa ba dad'ewa akai mata ya nuna 5weeks.

       Dad'i gun Ahmad baze misaltu ba itade Reyhana kawai takardan ta zubawa ido dukda kuma cikin ranta itama farincikinne.

      A hanyar dawowa ya sayi fruit da balangu suka komo gida a napep yana ta mata hira itade uhm da a'a ne amsarta.

     Suna shiga gida Ahmad ya sata a gaba seta sha fruit da naman.Kad'an ta samu taci tace ta 'koshi.

       "Kina so ki bar Babynmu da yunwa ne?Ahmad ya fad'a.

     " Nafa 'koshi anjima na sake ci".Reyhana ta fad'a.

    "Toh yanzu me kike so?" Ya tamabyeta.

     "Bacci"Ta amsa.

     " Laa! Azizaty yau bacci kike so ba niba".Ahmad ya fad'a dan so dayawa ya saba tamabayarta haka seta ce masa shi.

      "Toh nima shikenan ,babynmu nake so". Cewar Ahmad.

     Reyhana murmushi kawai tayi ,tashi tayi da niyyar tattare kayan gun da sauri Ahmad ya ri'ke hannun.

     " Azizaty rufan asiri mey ta kaikai yin aiki a wannan lokacin kwantawa zaki ki bacci ba abinda zaki ta'ba".Ahmad ya fad'a.

       Hannunta ya ri'ke suka nufi d'aki ,kan gado ya kwantar da ita ya saisaita mata fankar d'akin ,yana zaune gefen gadon har seda tayi bacci tukun ya koma sitting room.

      Kayan wajen ya tattare da kwanukan da suke ba a wanke ba ya d'aurayesu.

       Reyhana baccinta tayi ta 'koshi se wajen 2 ta farka tayi sallah nan ta tarar da abinci shinkafa da miya koda ta tambayeshi shi waya dafa yace ai umma ce ta turo yaro ya kawo.

      "Kenan fad'a mata kai bani da lafiya". Cewar Reyhana.

      " Ehyi ta kira kina bacci ma".Ahmad ya fad'a.

      "Ya babynmu ya tashi?" Ya tambayeta tare da d'ora hannunsa ya shafa cikinta dayake a shafe.

       Dariya tayi tana kallonsa "Taya zansani nikam?" Ta fad'a.

     "Kinjiki tun yaushe ma ni ai yanzu naji tunda ke baki sani ba". Ahmad ya fad'a.

      " Hmm!"Abinda kawai ta fad'a tare da girgiza kai tana murmushi.

       Da kansa yayi ta bata abincin kuma taci da yawa ba kamar jiya ba ,maganin ya 'ballan mata tasha.Zazza'bin ma ya sauka yanzu se kasala de gashi baccinma ba dika ya tafi ba.

               ***

     Se washegari ya koma aikinsa ,itama Reyhana ta samu sau'ki zazza'bin yawanci se da dare takeyi kad'an se bacci ba wuyar tayi bacci.

        A 'yan kwanakinnan haka take daga shingi'da se bacci ya kwasheta ,idan kuwa ya fita tana d'an yin abunda zatai se bacci wani sa'in ko shigowar Ahmad bata ji.

        Umma ma tazo ta duba ta har gida ,su Ikram ma sunzo  lokacin da bata jin dad'i.

         Yau tana zaune bayan tayi wanka ta shirya ,haka kawai taji tana son cin d'ata.

      Da farko tayi tunanin ko ta kira Ahmad idan ze dawo ya taho mata da ita,ganin bazata iya jiran har tsahon wannan lokacin ba ta yafa mayafi wasu 'yan chanjin dake wajenta ta d'auka ta le'ka 'kofar gida Allah yasa ta hangi wani yaron ma'kwafta nan tayi kiransa ta basa kud'in ya sayo mata.

      Bayan 'yan mintina ya dawo Reyhana ana rawar jiki aka amsa ta shige gida nan danan ta d'aureye ta fara gutsurar kayanta.

     Taci kusan uku jin amai ze tunkaro ta ta ha'kura.Ta kunna TV tajiyo knocking, hijab ta zira ta tafi bud'ewa.

     Tasha mamaki ganin Mommy a tsaye gefenta Anty Asma'u.

       "Laa! Ashe kune, sannunku da zuwa". Ta fad'a.

       " Yawwa".Suka amsata.

       Ciki ta 'karaso dasu,har 'kasa ta dur'kusa ta gaishesu.

       "Ina yini".

       " Lafiya lau".Suka amsa.

         Tashi tayi ta  had'o musu zo'bo da yake a fridge se ruwa ta jero musu a tray.

       "Ya jikin naki su Ikram sunce kinyi zazza'bi". Mommy ta fad'a.

        " Na samu sau'ki".Cewar Reyhana tana ajje tray d'in.

      "Toh Alhandulillah". Suka amsa.

      " Sageer ne ya kawo ku?" Ta tamabaya bayan ta zauna a kujera.

      "A'a shi ya tafi makaranta ma ,nina tu'komu". Mommy ta amsa.

     " Ya Ahmad d'in?" Anty Asma'u ta tambaya dan Mommy ba tamabaya zatai ba.

          "Reyhana inci?" Anty Asma'u ta  tambayeta lokacin da ta d'auki d'atar dake hannun kujera.

        Dariya tayi Reyhana sannan tace "Laa kici mana Anty".

      Anty Asma'u dama tana son d'ata inde ta hangeta a hanya takan tsaya ta siya.

      Mommy kuwa ganin d'atar yasa hankalinta ya kasa kwanciya ,a sanyaye ta kalli Reyhana ta lura da sauyin da tai.

       Ta 'kara fari ga ta d'an murje.

         Kitchen ta shiga ta had'a miya dan tattasan dama a soye yake.A 'yan mintina ta 'karasa ta zubo musu couscous d'in.

         Mommy idanta na kan abincin da Reyhana take zuba musu a plate so take taga koda nama ko babu.

     Aiko de babun ta gani a take ta ta'be baki.

      D'an kad'an taci tace ta 'koshi gara Anty Asma'u ta d'an ci dayawa.

        Reyhana ganin d'atarta biyu ne ya ragu yasa ta tashi ta shige d'akinta ta kira Ahmad.

      " Yaya ya aiki?" Reyhana ta tambaya.

        "Lafiya my Azizaty, ya babynmu?"

        "Lafiya lau". Ta amsa.

        " Yaya d'ata nake so".Reyhana ta fad'a.

        "Iye! Babyn mu zeci d'ata,kunyar first born kike koh".Ahmad ya fad'a.

          " Kunya kuma?" Reyhana ta fad'a tana turo baki.

           "Ehyi idan ba kunya kike ba  repeat what i will say".

           " Babynmu zeci d'ata".Ya fad'a.

           Shiru tayi a hankali tace "Babynmu zeci d'ata ".

         " Banjiba".Ahmad ya fad'a.

         "Kafa jini".Ta fad'a kamar zatai kuka.

         " Azizatyn Ahmad karki kuka shikenan zan taho maki dashi".

         "Mommy fa sunzo suna parlor ma". Ta fad'a.

         " Ki gaida min dasu kafin na dawo".Ya fad'a.

         "Toh seka dawo".

         " OK bye I love u two ki shafamin babynmu".

         Dariya tayi sannan tayi hanging ,komawa tayi wajensu Mommy suka cigaba da hira.

         Wajen 4:30pm suka tafi Ahmad be samu ganinsu ba.

       Reyhana shikenan kuma yanzu bata zama ba d'ata koyaushe cin d'ata wani sa'in ma ta gwammace taci d'ata da abinci abun har ya ishi Ahmad.

       "Yau fa ba cin d'ata ni babynmu ya gaji". Ahmad ya fad'a yana zira takalmansa.

       " Dan Allah Yaya ka taho min da ita yau bansan inda zansa kaina ba idan ban ci ba".Reyhana ta fad'a cikin shagwa'ba.

     "Shikenan amma yau sekin ci abinci sosai zaki ci kin yarda?"

      Kai ta d'aga alamar eh ,daga haka  sukai sallama ya fita.

        Haka rayuwa ta cigaba a kwana a tashi yau cikinta wata biyar ya fito.Ta fannin aikin sa de se addu'a inda Allah ya taimaka Reyhana mace me ha'kuri so da dama Mommy seta tayiwa Abba complain akan zaman Reyhana a gidanta dan yanzu ta gano baya teaching d'in.

      Abba idan ya kira ya tambayi Reyhana koda wata matsalar seta ce a'a,wani sa'in yakan tura Sageer ya kai mata kud'i ko kuma idan tazo ya bata. Sede kwana biyunnan 'kwaras suke basuda kud'i gashi Umma bata jin dad'i ana ta zarwar kaita chemist amma ciwo seya dawo,a kaita asibiti abu ya gagara.

      Reyhana tana zaune tayi nisa cikin tunani wani idea d'inne ya fad'o mata aikam da sauri ta kira sageer a waya tace yazo gidanta.

      Daga school ya samu ya biyo.

     "Sageer kaga dama phone d'ina nake so ka sayar mini seka sama min ko 'karama ce amma fa promise me bazaka fad'awa Mommy ba". Reyhana ta fad'a.

      " Kai yaya ya zaki sayar da phone naki ki fad'awa Abba mana idan kud'i kike so".Sageer ya fad'a.

       "A'a bazan fad'a masa ba kana kallo ko sati ba'ayi ba ya bani 10k kuma sannan na sake tamabyarsa,nide kawai inda zaka sayar mini". Reyhana ta fad'a.

      " Toh shikenan kawo wayar".Ya fad'a.

         "Promise baza ka fad'a mata ba".

         " Bazan fad'a mata ba ".

         " Good".Cewar Reyhana tana zare sim d'inta da mcard.

          Wayar ta mi'ka masa ya tafi,dama tuntuni bata jin dad'i taga Ahmad yana ri'ke 'karamar waya ita kuma babba(Allah sarki Reyhana).
Chapter 7 · 0% Book details