← Book details Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 33

Sashe 5

Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        "Kaji Mommy, wai dan Allah meyasa ta'ki zuwa ko su Anty Asma'u ai sa zo sekace banida dangi har kunya nake ji". Reyhana ta fad'a tana nuna alamar damuwa.

      " Tana gida na barota ma Anty Asma'un".Sageer ya fad'a.

       Tashi tayi ta kawo masa ruwa da zo'bon data had'a d'azu.

        Yana zaune Ahmad ya shigo, shiru tayi batace komai ba dan taji ba dad'i be dawo da wuri ba kuma be kirata ba.

         Koda suka gaisa da Sageer d'aki ya bita dan yaga mood nata ya sauya.

        "Azizaty mey nayi". Ya tambaya.

         Shiru tayi masa harta d'auki abinda zata d'auka saboda haka ya shige toilet ya watsa ruwa.

          A sitting room kuwa alewoyi da chewing gum da Saudat ta kawo mata ta bawa Walida. Ba dad'ewa yasa kaya ya fito.

      " Sageer bade tafiya ba". Cewar Ahmad.

        "Gobe da islamiyya ne". Ya amsa.

      " OK".Cewar Ahmad.

     Har mota Reyhana suka rakasu sannan suka dawo ciki.

AR²💖

*Need you warm comments,vote and shares.*

Jasko💕

🎍 *ARZI'KI RABO*🎍

*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 0⃣5⃣

Koda suka komo ciki bata yi masa magana ba illa zama a kan kujera data yi ta shiga latsa waya.

Zama yayi kusa da ita yace "Azizaty mey nayi?" Ya tambaya.

Shiru tayi bata ce komai ba.

"Please say something ko naji sanyi my Azizaty".

Yanda yayi maganar yasa ta kusa dariya amma seta maze ta cigaba da kallon waya.

" Ayya azizaty inde dan ban dawo da wuri bane ina me neman afuwa ,dubiya muka je da abokaina wayata kuma ba charge shiyasa ban kira ki ba". Ahmad ya fad'a.

"Toh amma kasan zan damu dayawa aikoh da seka kirani da wata wayar". Cewar Reyhana cikin shagwaba.

" Sorry my Azizaty next time haka bazata faru ba kinji".

Kai kawai ta kad'a bata ce komai ba.

"Kin ha'kura?" Ya tambaya tare da tallafo ha'barta.

"Smile my one and only always and forever". Ya fad'a.

Hakan yasa ta saki murmushi ,shi kuwa hugging d'inta yayi tightly " I love you Azizaty.Ya furta

"I love you too dear". Ta fad'a itama ta sake 'kan'kameshi.

***

Ta 'bangaren Mommy kuwa Walida bayan sun koma take nuna wa Ikram alewar da Reyhana ta bata.Mommy ta'ba baki tayi dan tana zaune a palour.

" Wai sunan gidan Amarya aka je shine aka 'kare da wannan mtchhwww!" Mommy ta fad'a tare da tsaki.

Ita Walida bata ji me Mommy tace ba amma Ikram taji tayi gum da bakinta.

Washegari...

Kasancewar weekend Ahmad yana gida throughout be fita ba ,suna sitting room abunsu suna kallo a TV Reyhana ta d'ora kanta a cinyarsa.

Wayar Reyhana ce tayi ringing hakan yasa ta tashi,koda ta duba taga Mommy bayan sun gaisa Mommy take fad'a mata bikin wata cousin tasu Reyhana da za'ai.

"Mommy kisa Ikram ta kawo min invitation dan Allah". Reyhana ta fad'a.

" Idan ba'a kawo ba kenan bazaki jeba?" Mommy ta tambaya.

"A'a ba haka nake nufi ba wai da sena bawa ya Ahmad na d'aurin aure".Reyhana ta fad'a a sanyaye

" Bikin danginki ake ko nashi? dole seya je?" Mommy ta tambaya cikin fad'a.

Allah yasa lokacin Ahmad ya fita daga d'akin da ze iya ji.

"Eyyi baki amsan ba". Cewar Mommy.

"A'a ,toh Mommy Allah ya kaimu"Reyhana ta fad'a kwalla na cika a idanunta.

Daga haka sukai sallama gefe ta ajje wayar takaici ya isheta.Furucin Mommy ya bugi zuciyarta sosai taji ba dad'i koyaushe bata da buri irin Mommy ta dena tsanar mijinta ita da danginta."ko su Mommy basu kawo IV ba ai gidansu Amaryar sa kawo".Abinda ta fad'a a ranta kenan.

Tana cikin wannan batunne sega Ahmad ya shigo da sauri tayi 'ko'karin saita kanta karya gano wani abun.

" Da Mommy kikai waya?" Ya tambaya.

"Eh tana gaisheka".Reyhana ta fad'a.

Toh ina amsawa". Ya fad'a.

" Dama maganar biki ce ranar alhamis za'a fara". Reyhana ta fad'a.

"Ok toh Allah ya kaimu". Ahmad ya fad'a ba tare da ya sake cewa komai ba.

" Ranar friday d'aurin aure kuma". Ta fad'a.

Nan ma Allah ya kaimu yace.Reyhana a zuciyarta haushi ya mamaye dabadan ba da ba abinda zesa ta fad'a masa zancen d'aurin auren dande karya fuskanci ko da wani abun.

Haka abubuwa suka cigaba da gudana an biya Ahmad albashi ya d'anyi musu 'yar siyayya ta kayan tea da sauran 'yan abubuwa haka Umma ma.

Yau take alhamis ranar kamu,Reyhana ba ita ta shirya ba se 4:30pm ,su Mommy kuwa su ajinsu ko zata je da wuri gidansu Amarya idan yaso lokacin kamun yayi se a rankaya a tafi amma suka ji shiru.

Da Ikram tace zata kirata Mommy ta hana ta.Wajajen 5 kowa ya hallara hatta Amarya tazo waje ya cika ana shagali mutane dayawa suna tambayar Reyhana Mommy har ta gaji da cewa tana hanya.

Reyhana ba ita ta 'karaso ba se 5:35pm saboda yanayin hanya.Walida ce ta hangota da sauri ta 'karasa gunta.

Mommy tana zaune kan kujera suna gaisawa da wasu ta hangesu suna 'karasowa.Tun daga nesa Mommy take hararar Reyhana har ta 'karaso.

Seat ta samu ta zauna ta gaisheda mutanen wajen sannan Mommy da ta gama 'kulewa.

"Ina wuni Mommy". Ta gaisheta.

" Bansani ba,sannunki da 'ko'kari kowa ya gama hallara banda ke se tambayarki ake harna gaji da yin magana,kin kyauta kenan?" Mommy ta fad'a rai a 'bace.

"Mommy naga wai da yamma ne". Cewar Reyhana.

" Ke a matsayinki yaci ace se yamma zaki zo sekace ba 'yar uwakki ba".

Ai Mommy tana cikin yi mata fad'a sega Anty Asma'u itama ta fara zazzaga mata nata,Reyhana jitai bikin dama bata zo ba gashi ba abinda ya sake ci mata rai irin yadda rashin zuwan nata ya shafi Ahmad. Shi suka koma blaming suna cewa "Watoh shi kulle yake seya ga dama zaki fito". Mommy ta fad'a.

'Kila ma seda ta gama yi masa girki". Anty Asma'u ma ta fad'a.

Wani zazzafan hawaye ne ya sakko mata ,Allah sarki Ahmad abinda shi ke ta tuna mata tayi sauri ta shirya yamma nayi shine aka la'kaya masa abinda beba.

Ganin ta fara hawaye yasa suka rabu da ita karta tara musu dangi dan idan ta fara kuka ba kanta,kowa seya san tana yi.

Reyhana ko hoto da Amarya batai ba tana zaune gu d'aya Ikram ce daga baya tazo take bata ha'kuri dan su Mommy sun tashi daga gun.

Ganin Maghreb na shirin yi yasa ta tashi,zuwa tayi har inda su Mommy suke tayi musu sallama ta tafi duk cikinsu ba wanda yai maganar tafiyarta da wuri.

Mommy basu suka tafi ba se wajen 9:00pm.Aiko Walida bayan sun koma gida suna shiga ta nufi Abba da suka tarar zaune parlour.

" Abba kasan mey Mommy sukai wa yaya?" Cewar Walida.

"A'a Walida sekin fad'a". Abba ya fad'a tare da tattaro attention kanta.

" Wlhy kuka tayi suna mata fad'a". Ta fad'a harda zaro ido.

Mommy kuwa da tin shigowarsu suka haye sama ita da Ikram dan a gajiye suke.

"Da gaske Babyna?" Abba ya tambaya yana son sake tambatarwa.

"Da gaske nake Abba ka tambayi Ikram ma kaji hadda Anty Asma'u sukai ta mata.." Bata 'karasa ba Abba ya katseta.

"Ya isa aje a kwanta dare yayi kinji". Cewar Abba yana lalla'bata.

Kan kice me ta haye sama abinta Abba kuwa ya shiga tunanin abinda sukaima Reyhana.

Ita kuwa Reyhana sanda ta koma gida Ahmad ya kula da yanayinta amma seta ce ciwon kai take ji.Ko abincin dare bata iya girkawa ba dama akwai ragowar na rana suka ci suka kwanta.

Washegari da safe kasancewar d'aurin auren 11am ne Reyhana da kanta tace wa Ahmad ya ha'kura da zuwa tinda yana da makaranta,ko ba dan haka ba dama bata so yaje dan tana gudun kar a wula'kantashi.

Ita kuwa sunyi dashi zata tafi gidan bikin 12pm amma yana fita ta dawo tayi kwanciyarta koda ta farka aikace-aikacen gidanta tayi ta d'ora girkinta.

      Mommy kuwa suna can ana ta hotunan d'aurin aure ,gefe guda ta ware tayi dialing number Reyhana.

      " Reyhana lafiya baki zo ba?"Mommy ta tambaya.

      "Na tashi banda lafiya ne".Tayi 'karya harda narke murya.

      " Bakida lafiya? Har ankon dinner gashi kuma anyi miki".Mommy ta fad'a.

      "Idan na samu sau'ki sena shigo anjima". Reyhana ta fad'a.

       " Toh Allah ya sawwa'ke".Mommy ta fad'a sannan ta katse wayar.

      Reyhana kuwa koda rana tayi bacci ta koma abinta dama Ahmad ze biya gidan Umma daga makaranta.

    Haka aka gama biki bako d'uriyarta ,Ahmad daya dawo ya tamabayeta tace masa ciwonkan be dena ba.

    Mommy dama ta fidda ran zuwanta,akayi dinner ba ita.Washehari ma yini bata jeba haka aka 'kare biki ba ita.

     Ranar sunday da safe Abba yana gida yayi kiran Mommy, ita bata kawo akan Reyhana bane bama.

       "Mommyn Walida me Reyhana tayi miki?" Ya tamabayeta bayan ta zauna.

      "Bangane ba". Mommy ta fad'a tana neman 'karin bayani.

       " A biki mana an fad'amin kun saka tayi kuka a dalilin mey?"

       "Ita Reyhanan ce kenan ta fad'a maka ,amma meyasa bata fad'a maka dalili ba?" Cewar Mommy.

       "Sam ba ita bace and tambayarki nayi ba canayi ki tambayan ba". Abba ya fad'a ba watsa cikin lamarin.

    D'an  gyara murya tayi Mommy kafin tace." Fad'a ne bata so,dan me zata zo biki kusan to 6 kowa yana tambayarta amma shiru abinda tutuni an fad'a mata".

     "Yanzu akan bikin shine kuka rifeta da fad'a? Yayi kyau Maryam kece da ita ko mijinta idan yayi niyyar hanata zuwa ya zakiyi? Dole fa ki ha'kura wannan yaran mijinta ne ko ki yarda ko karki yadda ,kuma bana so haka ya sake faruwa idan ba haka ba rai ze 'baci walhy". Abba ya fad'a cikin fushi.

    Mommy da ta gama 'kuluwa yana gama maganar ta tashi ta fita bako bada ha'kuri.

     Ai d'akin Ikram ta wuce direct,bacci ma take taji ana d'ala mata duka a cinya.

      " Tashi zaune nace!" Mommy ta fad'a.

     A zabure ta mi'ke dan dukan ya shigeta"Mommy !"Ta kira kamar zatai kuka.

       "Kece kika fad'a wa Abbanku nayi wa Reyhana fad'a a gidan biki?" Mommy ta tambaya.

     "A'a bani bace". Ta amsa.

      " Waye idan bake ba?"

       "Sede Walida". Ikram ta fad'a.

      Mommy kai ta kad'a ta wuce d'akin Walida,itama tana bacci ta tasheta.

      " Kece kika fad'a wa Abbanki nayi wa yayarki fad'a koh?"
Chapter 5 · 0% Book details