Sashe 17
Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru yayi bece komai ba ,ita kuma ta tafi kitchen had'a karin kumallo.
***
Ahmad kalaman Umma da Sadiq ne suka fara tasiri a zuciyarsa,dan yana ganin inde ya cigaba da zama haka zuciyarsa ce zata mutu gara ya mi'ke ya zama cikakken namiji.Zuciyarsa ta fad'a.
Sede fa yana tunanin kuma barin Umma ita d'aya haka bayanan waze dinga kula da ita?
Haka yayi ta tunaninsa gashi koyaushe cikin addu'a yake Umma ma bata dena ba.Cikin ikon Allah yaji 'kuncin da yake zuciyarsa yana raguwa kuma scholarship d'in ya soma kwanta masa a rai.
5days later ,da kansa yace wajen Sadiq ya fad'a masa ya amince ,sosai Sadiq yaji dad'i .Ba 'bata lokaci yayi applying cikin ikon Allah yaci jarabawar,sauran month ya rage su tafi.
A cikin 'yan kud'ad'en aikinsa yayi wa Nasreen siyayyar 'yan kayan pampers da sabulun wanka.Umma da kanta ta kai wa Reyhana ,cikin girmamawa suka gaisa da Umma ranar Mommy ma bata gida.
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa da dad'i babu ,tafiyar Ahmad ya rage week shida Umma sunje Zaria yayi sallama da wasu 'yan uwan ,wani yayan Umma ya bashi 30k ,shima wasu 'yan kud'ad'en nasa ya had'a dasu kad'an daga ciki yayi wa Umma 'yan siye-siyen kayan abinci.
Ana saura kwana biyu tafiyarsa ya kira Reyhana suka gaisa yake tambayarta Nasreen, sede beyi mata maganar tafiyarsa ba,da ba zeje gidan ba seda Umma tayi da gaske yaje,Nasreen ta sake wayo kamanninta dashi sun sake bayyana yayi mata pics a sabon wayarsa da ya siya.
Umma harda kukanta amma bata nuna a gabansa ba ,ranar da ze tafi shi kansa ya kasa cin abinci har airport Umma da Sadiq suka rakasa ✈(Nima nayi 'kwalla😧).
AR²💖
Readers! Ya kuka ga page d'in? 🔥🔥pls comment,vote ,luv u all😘
Jasko💕
Pls share
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD @dijensy*
*Thank you so much for your warm support Ummeeytr,sisi kema ban manta dake ba ina godiya ,masoyan littafinnan na whatapp godiya mara adadi Allah ya barmu tare 😘 Ameen.*
🅿 1⃣8⃣
Umma da
suka dawo tare da Sadiq jikinta a sanyaye ,tana tunanin yadda ze gudanar da rayuwarsa har tsahon lokacin da ze gama karatunsa,dan d'an nata be ta'ba yin nisa da ita ba kamar wannan karan.
Around 8pm Umma taji ringing d'in wayarta ,koda ta duba international number ta gani,dama a cikin ranta tayi tunanin Ahmad d'inta neh.
"Umma". Ya kira sunanta.
" Ahmad kaine".Umma ta fad'a da saurinta.
"Eh". Ya amsa.
" Kun isa lafiya?" Ta tambaya.
"Lafiya lau Umma". Ya asa.
"Toh kuna makaranta ne ko kuwa?" Ta tambaya.
"A'a mun samu Apartment ne tare da wasu 'yan kano da muka tafi dasu". Ahmad ya fad'a.
" Toh abinci fah ?" Ta tambayesa.
"Zanci". Ya amsa.
" Toh ka samu de kaci karka zauna da yunwa kaji".Cewar Umma cikeda damuwa.
"Toh inshaAllahu". Ya fad'a.
" Yawwa ka kula sosai".Ta fad'a.
"InshaAllah". Ya amsa.
Daga haka sukai sallama,bayan nan ya kira Sadiq ma ya sanar masa ya isa.
Ahmad ya samu yaci abinci kad'an duk da kuwa yana jin yunwa ,kawai kewa ce da ba'kunta suka sa ya kasa ci dayawa.
Sauran da suke apartment d'aya dashi suna falo su uku se surutu suke kamar ba wanda yau neh zuwansu na farko ba,Ahmad kuwa rufo 'kofar d'akin da yaye ya kwanta dukda ba shi kad'ai ne a d'akin ba.
Da'kyar ya samu bacci ya kwashe shi dan daya rufe idanuwansa Reyhana yake gani.
Washegari,6:08am ya tashi,hayaniyarsu ce ta tashe shi.
Da sauri ya mi'ke yayo alwala yayi sallah.D'ayan room mate nashi yaga ya baje se narkar bacci yake da alama beyi sallah bama.
'Karasawa yayi gadon da yake ya tasheshi,daga nan ya komo ya zauna.
Ba jimawa sauran guda biyun sukai knock a d'akin.
" Shigo". Ahmad ya fad'a.
"Assalamu Alaykum". Sukai sallama.
Ahmad ya amsa musu ,'karasowa sukai wajensa sukai handshake.
Nan suka sake introducing kansu.Da Ibrahim da Idris se room mate na Ahmad, Imran sunansa.
Kusan shine sa'an Ahmad sauran kuwa baza sufu 22 zuwa 23 ba.
Tare dukansu suka fita cin abinci a restaurant bayan sun shirya.
Shawara sukai a junansu suka siyi kayan abinci ,inyaso sa dinga girkinsu a gida.
Hrs later Ahmad ya kira Umma suka gaisa ,basiyi wani hira mey tsaho ba credit ya 'kare.
Shi gashi ba mey hira ba sosai,yana hangosu a falo suna ta hirarsu kowa yana bada labarinsa banda shi da ya ma'kale a d'aki.
***
Duba da sun fara shiga class Ahmad ya bada attention akan karatunsa,inda yaci sa'a shima Imran yana son karatu,kuma a kwana biyu ya fara sakin jiki dashi sede har yanzu duk cikinsu ba wanda yasan Ahmad ya ta'ba yin aure.Suna waya da Umma amma ba koyaushe ba ,Sadiq ma.
Tunanin Reyhana da Nasreen kuwa kullum dashi yake kwana yake tashi gashi har yanzu be sake yin waya da ita ba.
***
Nigeria ***
Umma ganin an d'an kwan biyu bata jin labarin 'yar jikallenta Nasreen dan ba waya take da Reyhana ba haka yasa ta shirya zuwa gidan.
Lokacin da inno tayi mata iso falo sisters d'in Mommy suna nan sun baje se hira sike irin ta mata sun cika falon da hayani.
Umma kan kujera ta zauna ,Anty Ummi ce ta lura da shigowarta ta gaisheta.Suma sauran suka gaisa da ita ba nuna alamar sun ganeta,Mommy tare da Anty Asma'u suka sakko daga bene.
"Kamar babar Ahmad nake gani". Cewar Anty Asma'u 'kasa-'kasa.
" Ehyi itace".Mommy ta amsa.
"Toh ita kuma mey tazo yi?"Cewar Anty asma'u.
"Kema kya fad'a". Mommy ta fad'a.
Shiru sukayi basu sake magana ba lokacin da suka 'karaso inda Umma take.
Umma bayan ta gaisa dasu take tambayar su Reyhana.
"D'azu yara sun fita da ita za'ai mata photo,Reyhana kuma tana bacci". Mommy tai 'karya dan kuwa tana d'aki tare da Reyhana.
" Ayya!"Umma ta fad'a a ranta bata ji dad'i ba.
Daga haka shiru ya ziyarci d'akin,su kansu masu hirar shiru sukai suna 'kus-'kus Anty Ummi se alamu take musu da siyi shiru suka 'ki.
Hakan yasa Umma ta tsargu,tana jiyo wata daga cikinsu tana cewa Anty Ummi "An rabu kuma meye na bibiya".
Umma in ranta yayi dubu ya 'baci,a ranta tana fad'in "Zuwa ka duba 'yar d'anka ma ya zama laifi".
Mi'kewa tayi taiwa Mommy sallama ta fita, bata kai bakin gate ba tajiyo kukan Nasreen kasancewar window na d'akin Reyhana a bud'e yake.
Umma jin kukan Nasreen yasa ta gano 'karya Mommy tayi mata,ba yadda ta iya haka ta fita.
Se bayan tafiyar Umma Reyhana taji Ikram da Sageer suna maganar,ji tayi dama ta sakko falo lokacin." Sema ta d'auka ko ina sane na'ki fitowa".Ta fad'a a ranta.
***
Umma tana isa gida taga Sadiq a 'kofar gida.
"Umma unguwa kika jene?" Ya tambayeta.
"Naje gidansu Reyhana duba Nasreen ne". Ta amsa .
Daga yadda ya kula da fuskarta ya gano wani abu,seda suka shiga ciki ya sake tambayarta.
"Ta 'kara wayo koh?"
"Ai dayake ban samu na ganta ba". Umma ta fad'a tare da shimfid'a tabarmar dake jingine a tsakar falon.
"Toh ya akai haka?" Cewar Sadiq yana son sake jin 'karin bayani.
"Cha sukai wai an tafi kaita photo". Umma ta fad'a.
" Cha sukai? Kuma Umma kin yarda? Toh ina ita Reyhanan?" Sadiq ya tambaya.
"Nide ban ganta ba tana bacci suka ce".Umma ta fad'a.
"Rainin hankali". Ya furta.
Umma kaf ta bashi labarin abinda ya faru ,Sadiq dama akwai saurin fushi lokaci guda ya hau masife -masife shi har Reyhana d'inma yayi blaming.
Umma seda tayi ta bashi ha'kuri wai seyaje gidan yayi musu rashin mutunci.
Cyprus 10:07pm ,Ahmad yana zaune kan kujera yasa litattafi a gaba yana karatu wayarsa tayi ringing.
Koda ya duba yaga Sadiq,fuskarsa d'auke da murmushi yai picking.
"Saddiqu". Ahmad ya kira sunansa.
" Ya ,ya karatu?" Ya tambaya.
"Alhamdullilah gashi muna tayi". Ahmad ya fad'a.
" MashaAllah,toh bari na barka".Sadiq ya fad'a.
"No !wait". Cewar Ahmad.
" Wani abune?" Sadiq ya tambaya yasan Ahmad idan yana so ya fad'i abu haka yake.
"Umma tana zuwa ganin Nasreen kuwa?" Ahmad ya tambaya.
"Danme zata ke zuwa ana wula'kantata". Cewar Sadiq ba tare da yasan ze fad'i hakan ba.
"Bangane ba Sadiq? Zuwa tayi suka wula'kantata!?" Ahmad ya tambaya ,pen d'in dake hannunsa ma ya ajje.
Shiru yayi kafin ya fad'a masa duk yadda akai.Bayan sunyi sallama dashi ya ajje wayar gefe yana mey jin zafin abinda sukaiwa Umma.
Da tunanin abin ya kwana ko karatun ma 'kin cigaba dayi yai ya rife littafin.
°°3 years later°°
Abubuwa da dama sun sauya ,Reyhana har yanzu bata sake wani auren ba duk wanda yazo yana sonta korarsa take tace ita bata shirya ba,tun Mommy tana magana har ta gaji ,ta koma Masters ma ta'ki aikin ma a nemo mata bazatai ba.Abba kuwa duk abinda tace bataso baya takurata ,Mommy ma sanin dalilinta Reyhana ke zawarci yasa bata takura mata.
Nasreen ta 'kara girma ,3yrs da 'yan kai kamanninta da Ahmad ba abinda ya sauya sede 'karuwa ma.
Ikram ce ta fito daga d'akinta taci kwalliya,yanzu ake jin 'yanmatanci tana 21yrs, biki ake a dangin Abba shine zasi dinner.
D'akin Reyhana ta shiga inda ta tarar da ita ko d'auri batai ba se fama take da Nasreen ita a lalle setayi kwalliya ,kuma kawai salon 'bata fuska ne da kayan kwalliyar kansu.
"Kai! Yaya ko d'auri baki ba haba dan Allah wannan ai har a gama dinner d'in". Ikram ta fad'a.
" Inyee irin wannan d'auri haka pls nima d'auran irinsa".Reyhana ta fad'a.
"Anty nima ki d'aura min". Nasreen ta fad'a cikin muryarta da bata gama fita ba.
" Kinga fuskarki kuwa!" Cewar Ikram sanda ta kalli Nasreen.
"Barni da ita nide gama d'aurin". Reyhana ta fad'a tana mi'ka mata d'ankwalin matiriyal d'in.
Sky blue ne ,d'inkin ya hau jikinta sosai doguwar gown ce ta shawu,itama Ikram irin kayan ne a jikinta.
D'auri Ikram ta tsantsarawa Reyhana ga kwalliya data 'kara mata sosai ta fito kamar ba itace mey 3yrs daughter ba.
Farin gyale d'an siriri ta yafa se purse silver ta zira takalminta me tsini silver.
" Ummie zan biki". Nasreen ta fad'a tana miko hannunta.
"Allura akewa yara a wajen,ki zauna da anty Walida". Reyhana ta fad'a tana spraying turare a jikinta.