← Book details Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 33

Sashe 29

Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Gidan Umma suka je kenan? Toh ko beyi aure ba daman?" Ta fad'a a zuciyarta.

Daga baya Nasreen ta shiga yin wasanta ta bar Reyhana da tunani.

°°°

Su Anty Asma'u yau Sageer ya kaisu gidansu Fatiman sa ,Mommy tana gida tana jiran su dawo taji bayani Abba sam besan da wannan batu ba.

Suna dawowa Mommy ta shiga tambayarsu ya aka 'karke.

"Matsalar daga kece Maryam". Anty Asma'u ta fad'a.

" Kamar ya ?" Ta tambaya tana neman 'karin bayani.

"Mahaifiyar yarinya tayi mana bayanin komai,tace dalilin daya sa suka guji Sageer shine sun samu labari ke bakya yarda 'ya'yanki si auri talakawa ,shiyasa suka ji tsoron abinda ze biyo baya kada daga baya azo ana da an sani".

Shiru Mommy tayi ta kasa cewa komai." Zancen duniya baya 'buya ,shedar da aka yi mata kenan ashe tin sanda tasa Ahmad ya saki Reyhana ". Ta fad'a a zuciyarta.

" Dama wannan dalilin ne yasa suka guji Sageer?"

"Ehyyi haka ta fad'a mana mahaifiyar yarinyar ,kinga kece sila ashe". Wata daga cikin yayyin Mommy ta fad'a.

Mommy kai ta dafe ta kasa cewa komai, tana mey jin haushin kanta ,gashinan halinta yasa d'anta ya shiga cikin wannan halin".

Har sisters d'inta suka tafi ta kasa sakewa,d'aki ta shiga ta zauna tana tuna irin takurawa Ahmad datai a baya ,ta d'ora masa karan tsana har seda tasa ya saki Reyhana,shi Sageer da bema yi auren ba amma ga irin halin da ya shiga shikam Ahmad harda 'ya a gaskiya bata kyauta ba ,batai musu adalci ba.

"Ashe irin halin da mahaifiyarsa ta shiga kenan sanda ya rabu da matarsa ,ya Allah na tuba Allah ka yafemin".

Mommy nadamar abinda tayi ta shiga yi tana dana sani.

Da kanta taje gidansu yarinyar ta fahimtar da ita ,ta fad'a musu bazata 'ki d'iyarsu ba.Se bayan Abba ya dawo da daddare take fad'a masa ,dama shi baida buri kamar Mommy ta gyara halinta kuma yanzu yaji dad'i tunda ta gane kuskurenta na abinda tayi a baya ,dan haka yace mata taje gidansu Ahmad ta bawa Umma ha'kuri.

•••

Kwana biyu Reyhana bata ganin kiran Ahmad haka text d'insa daya saba turo mata shima shiru.Tunani ta fara yi ko lafiya ,wata zuciyar kuma tace koh fushi yake?

" Toh ni nayi masa laifi neh da zeyi fishi ,oho masa".Ta fad'a.

Tashi tayi ta sauka 'kasa ,Walida ce kad'ai a parlorn.

"Walida ina Mommy?" Ta tambaya.

"D'azu ta fita tace bazata dad'e ba". Ta amsa.

" Ina taje?"Ta sake tambaya.

"Nima ban saniba". Ta amsa.

Kai kawai ta gid'a sannan ta shiga kitchen.

°°°

Umma tana parlor taji sallamar Mommy, abinda bata ta'ba tsammani ba kenan.

Iso tayi mata ta shigo parlor Mommy a sanyaye tana mey jin kunyar abubuwan da tayi a baya.

"Ina wuni". Mommy ta gaisheta.

" Lafiya lau ,ya yara?" Umma ta tambaya.

"Yara lafiya lau". Ta amsa.

Shiru ne ya ziyarci parlorn kafin daga bisani Mommy ta fara magana.

" Umman Ahmad, abubuwa da dama sun faru a baya wanda kowa beji dad'insu ba ,ni na zamo silar komai dan Allah ina neman yafiyar ku kiyi ha'kuri da abinda nayi miki inshaAllahu hakan baze sake faruwa ba nasan nayi kuskure ,kiyi ha'kuri".Mommy ta fad'a cikeda nadama.

"Mommyn Reyhana Allah ma ana masa laifi ya yafe ,kuma mu d'an Adam neh muna kuskure fatan mu dama idan minyi laifi mu gano kuskuren mu kuma tunda Allah yasa aka gano hakan an gode Allah ,komai ya wuce dama rayuwa ta gaji haka Allah ya yafe mana baki d'aya".Umma ta fad'a.

" Ameen ,nagode sosai".Ta fad'a.

Zainab da lokacin ta dawo daga school ta shigo parlorn.

"Ina wuni".Ta gaida Mommy cikin rissinawa.

" lafiya lau".Mommy ta amsa.

"Kun dawo kenan". Umma ta fad'a.

" Eh".Ta amsa.

Daga haka ta fita daga parlorn, Umma kuwa bata 'boyewa Mommy ba ta fad'a mata Zainab itace wacce Ahmad ze aura.

Mommy fatan alkairi tayi taja bakinta tayi shiru,seda Ahmad ya shigo shima suka gaisa cikin mitintawa,shima seda ta bashi ha'kuri yace mata ba komai shi dama be ri'ke ta ba.

A yanzu ne Mommy taji sakat da ta nemi yafiyarsu,ranta fyas ta koma gida ta tarar da yaran duka sun dawo kowa yana gida ,hatta Sageer shima yau yana parlor damuwa ta tafi komai ya dedeta.

Sannu da zuwa sukai mata duka yaran bayan ta amsa ta wuce d'aki.Bayan maghrib ta kira Reyhana ta fad'a mata taje gidansu Ahmad.

"Reyhana kema nasan kina..." Bata 'kare ba ta katseta.

"Mommy komai ya wuce dama Allah ya riga daya tsara ba yadda zami ,ki dena tunanin wani abu".Reyhana ta fad'a.

" Toh Nasreen fa zaki fad'a mata yanzu? "Mommy ta tambaya.

" Mommy ni ina ganin a bari nan gaba da kanta zata fahimci hakan".

"Idan yayi aure kina ganin baze kar'bi 'yarshi ba?"

"Mommy ya za'ai ya d'auke ta ,ni bazan yarda ba gaskiya".

" Toh ya zakiyi za'a cigaba da zama a haka ne?,kema wataran ai auren zaki ko wane namiji ne ze ri'ke 'yar da ba ta shi ba?"

Shiru tayi batace komai ba ta tur'bune fuska dan bata so taji ana maganar rabata da Nasreen d'inta.

"Baki ce komai ba?" Mommy ta fad'a.

"Toh Mommy ai bece ze kar'beta ba".

" Lokaci na zuwa,Ummansa ta nuna min wacce ze aura". Mommy ta fad'a.

Wani iri taji jin abinda Mommy ta fad'a, abu de yana shirin tabbata, gaske ne abinda take tsammani Ahmad Zainab ze aura?"

"Kema ya kamata ki kira Umman tashi ki bata ha'kuri ". Mommy ta fad'a.

Se lokacin ta bar tunanin da take ta amsa da " Toh".

Har bayan ta koma d'akinta bata dena tunanin abinda Mommy ta fad'a mata ba.

°°°

Bayan fitar Mommy daga gidan Umma take tambaya Ahmad shirye-shiryen biki ,shi sam baya so take tuna masa.

Duk abinda ta tambayeshi "uhm" kawai yake ce mata, ganin Mommy yasa ya sake karkata wajen Reyhana yana ganin yanzu baida wata matsala gameda dawo da Reyhana tunda Mommy ta ha'kura.

8pm yana d'aki lokacin, number Reyhana yayi dialing ba kamar koyaushe ba yau a kiran farko tayi picking.

"Assalamu Alaykum". Tayi sallama.

" Waalaikumussalam". Ya amsa.

"Nasreen d'in tana kusa?" Ya tambaya.

"A'a". Ta amsa.

" Ok toh shikenan". Ya amsa sannan ya kashe.

Wayar tabi da kallo ta rasa ma mey zata yi,ba abind a ya bata haushi kamar yadda ya kashe maimakon ita ta zama ita ce ta katse.

Washegari kamar yadda Mommy ta fad'a haka tayi, ta kira Umma ta bata ha'kuri.

Tana ajje wayar sega Walida ta shigo d'akin.

"Yaya ga ya Sameer yazo shida sisters d'inshi".

" Yanzun?" Ta tambaya.

"Ehyi suna parlor". Ta amsa.

"Toh kice musu ganinan".Ta amsa.

•••

Yau Ahmad da kanshi ya d'akko Nasreen ze kawo ta gida ,tun daga nesa Nasreen ta hangi motar Sameer.

" Kalli motar Uncle Sameer yazo gidanmu".Ta fad'a tana nuna motar.

"Uncle Sameer?" Ya tambaya.

"Eh Uncle Sameer". Ta fad'a.

Seda suka 'karasa ya lura da Reyhana da take tsaye a 'kofar gidan gefe kuwa Sameer ne suna magana amma besan mey suke cewa ba.

Ita kuwa Reyhana rakiya ta fito koda sisters d'in nashi suka shiga mota Sameer ya tsayar da ita suna magana sega Ahmad.

Yana parking Nasreen tayi sauri ta fito " Ummie yau Uncle ne ya kawo ni!" Ta fad'a tana 'karasawa inda sike.

Sameer se lokacin ya dubi motar ya hangi Ahmad sannan ya dawo da kallonsa kan Reyhana.

"Ahmad, shine mahaifin Nasreen". Reyhana ta fad'a.

Kai ya d'an gid'a sannan ya mayar da kallonsa kan Ahmad.Da Ahmad beyi niyyar fitowa ba amma ganin Sameer yasa ya fito ,a hankali ya tako har inda sike.

AR²💖

Don't forget to tap on the star below, comment and share.Love you all.Tell me if you are ready to see the pic of those three ,four right? Including zee😂

Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍

*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 3⃣2⃣

  Yana 'karasawa wajensu ya mi'ka wa Sameer hannu su gaisa,beyi musu ba ya mi'ka masa shima.

       Sede kowa a zuciyarsa da abinda yake tunani.Ita de Reyhana ido ne nata.

         "Sannu koh". Ahmad ya fad'a yana kallon Reyhana

          " Yawwa".Ta fad'a ciki-ciki.

       Daga haka ya wuce ya shiga gidan,yana gaisawa da Mommy ya fito dede lokacin Reyhana tana shigowa.

       Kallo d'aya tayi masa ta d'auke idonta ta wuce ta barshi a tsaye ta shige,shima ba tare da yayi magana ba ya fita ,har ya koma gida be dena tunanin Sameer daya gani ba.

        Lokacin daya shiga parlor Umma bata nan se Zainab.

      "Sannu da dawowa ya Ahmad". Ta fad'a.

        " Yawwa".Ya amsa.

         Shiru ne ya ziyarci parlorn kafin daga bisani Zainab ta sake wata maganar.

        "Yaya naga sa'ko na gode". Ta fad'a.

       " Uhm?" Ya tamabaya cikeda neman 'karin bayani.

       "Na agogo da ka bada a bani". Ta fad'a.

        "Uh..ok". Cewar Ahmad yana tunane-tunane.

       " Sadiq?" Ya fad'a a ransa.

       "So ,shine ya bata agogo yace ni na bashi ya bata.." Ya fad'a a ransa.

       "Ka dawo kenan" Umma ta fad'a sanda ta shigo.

        "Eh na dawo". Ya amsa.

         Tashi yayi ya fita ya koma d'akinsa ya d'auki way a ya dannawa Sadiq kira.

       " Na zee".Sadiq ya fad'a yana dariya.

        "Sadiq zan maka wula'kanci". Ahmad ya fad'a.

        " Daga nayi maka abin arzi'ki,dan'kon soyayya na 'kara maku fah".

        "Bana son irin wannan ". Cewar Ahmad kamar yana ganinsa.

        " Kode kishi kake? Gaya mini in baka so nake mata magana sena dena".

        "Ni na saka ka saya mata agogo har kace nina ce ka bata?"

        "Beyi kyau bane agogon?" Sadiq ya tambaya cikeda rainin hankali.

     Ahmad dan tsabar takaici kashe kiran yayi ,ya ajje wayar gefe.Tunani Sameer da Reyhana ne ya sake dawo masa a take ya d'auki wayarsa ya kira ta.

     Seda ya kira sau uku tukun tayi picking.

    "Assalamu Alaykum". Tayi sallama.

     " Waalaikumussalam,nayi sa'a an d'aga min  kira". Ya fad'a bayan ya amsa.

      "Eh ai saboda ban gane number d'in ba shiyasa banyi picking da wuri ba". Ta fad'a.

     " Au dama har yanzu number ta bata chanchanta ayi saving ba?"

       "Eh". Ta amsa a ta'kaice.

         " Toh yanzu ina fatan kingane mey magana?" Ahmad ya tambaya.

           "Ina fatan bazaka sake yimin irin wannan tambayar ba?"

       "Ni na isa". Ahmad ya fad'a.
Chapter 29 · 0% Book details