← Book details Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 33

Sashe 4

Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Da kanta ta za'ba masa kayan sawa yana fitowa ya gansu ta ajje a kan gado ,T-shirt ce dark blue da ba'kin jeans ,da sauri ya saka ya shirya tsaf tukun ya fito.A kitchen ya taddata tana soya dankali.

      "Ina kwana". Ta gaisheshi.

       " Lafiya,ya bacci Azizaty jiya da wuri haka kika kwanta". Ahmad ya fad'a.

        "Eh toh naga kana ta marking". Ta fad'a.

           " Toh me ake dafa wa?" Ya tambaya.

           "Hmm dankali ne". Ta amsa.

           " Sannunki da 'ko'kari".

           "Yawwa dear". Ta amsa.

       Bayan mintina ta kammala ta kawo masa." Azizaty ke ba yanzu zaki ci ba?"

      "Se anjima".Ta amsa.

     Ba jimawa ya gama breakfast d'in,takalmi ta d'akko masa a d'aki yasa sannan ya tafi ,ita kuwa ta koma baccinta.

              ***

     Haka abubuwa suka cigaba da gudana ,Ikram da Walida sunzo sun wuni sageer ma yazo, Abba ne har yanzu daya cewa mommy suje seta ce ba yanzu ba ,sede yana waya da ita.

      Yau aurensu wata uku kenan,Reyhana na kitchen tana girki yau Saudat zata zo.

        " Azizaty 'kawar taki bata karaso ba kenan".Ahmad ya fad'a sanda ya fito tsakar gidan.

        "Minyi waya tace ta taho". Reyhana ta fad'a.

         " OK,bara zan d'an le'ka waje ba dad'ewa zan ba".Ya fad'a yana zira takalma.

         "Toh shikenan seka dawo".

        'Yan mintina 'kalilan ta 'karasa dama couscous da miyan ne se lemon cucumber tun jiya dama tayi mata cake ga exotic guda biyu daya ragu ta had'a mata da d'aya.

        2:45pm Saudat ta 'karaso gidan ,Reyhana tana d'aki tajiyo knocking d'inta da sauri taje ta bud'e."Besty!" Reyhana ta fad'a tare da hugging Saudat.

     "K'awas kai nayi  missing d'inki sosai sosai". Saudat ta fad'a.

      " Toh mu 'karasa ciki". Reyhana ta fad'a tare da breaking hug d'in.

        Sitting room tayi mata jagora suka 'karasa kowacce farinciki ya mamayeta."Amarya ashe zan sake ganinki".Cewar Saudat sanda suka zauna a kujera.

       "Ke d'ince koyaushe sa rana kin kasa zuwa,ya su Mama". Reyhana ta tamaya.

       " Duk lafiya suke,sunce a gaisheki".Saudat ta amsata.

        "Bari ina zuwa". Reyhana ta fad'a tare da fita.

         Abincin da sauran kayayyakin ta jero a tray ta kawo mata." Sakko ki ci se ai hirar".Cewar Reyhana.

          "Ohni Saudat du ni kad'ai".

          " Ehyi ke kad'ai.Ta amsa.

       Sakkowa tayi ta fara da,suna d'an hira tana ci."Ya Mommy kuwa tazo". Saudat ta tamabaya.

       "Ai Mommy har na fiddaran zuwanta har yanzu bata zo ba kuma Abba yana so zuzo amma shiru de,su Ikram de sunzo amma ko sisters d'in Mommy basu zo ba,na fad'a maki nifa bana ba'ki shiyasa kika ga ina azar'ba'bi kizo". Reyhana ta fad'a fuskarta na nuna tsantsar damuwa da hakan.

      " Ayya 'kawata karki damu inshaAllah komai ze dedeta kiyi ta addu'a,amma kede kina waya da ita koh?" Saudat ta tambaya.

      "Eyyi ina wayo dasu".Ta amsa.

      " Toh hakan yayi kyau".Saudat ta fad'a.

       Bayan ta gama cin abincin sega Ahmad ya dawo ,suna gaisawa da ita ya shige d'aki.

     Ranar ta musu dad'i sunsha hira abinsu da selfie,se wajen 5:30pm  Saudat ta tafi.

              ***
    Gidan Mommy..

          "Bafa inda zaki na fad'a maki". Mommy ta fad'a tana zaune kan sofa na parlour.

      Walida dake tsaye ta yafa mayafi ita a lalle seta je gidan Reyhana.

     " Mey ke faruwa ne?" Abba ya tamabaya sanda ya sakko 'kasa dan yajiyo d'aga muryarta.

        "Abba dan Allah kace Mommy ta barni naje gidan Yaya". Ta fad'a kamar zatai kuka.

      Abba Mommy ya kalla da ta 'kura wa TV ido kamar bata san suna gun ba." Mommyn Ikii ki barta taje mana".

      "Na fad'a mata ba inda zata gara ma ta ha'kura". Mommy ta fad'a ba tare da ta kallesa ba.

    Hakan da tayi ya 'kona masa rai." Walida jeki d'aki zan kira ki anjima".Abba ya fad'a.

       Ba musu ta haye steps da sauri, Abba kuwa takawa yai ya 'karasa wajen Mommy ba tare da ya zauna ba yace"Bana son abinda kike yi taya ina maki magana ki kauda kanki ,kuma wannan yarinyar gidan yayarta zata meye aibu a ciki tunda ke kin'ki zuwa seki barsu su dinga zuwa bafa kya kyautawa yarinyarnan duk abinda ze faru ya riga ya faru kowa da kika gani bada arzi'ki aka haifeshi ba a duniya ya samu ki duba mana".

        "Allah ya taimaka 'kofa ce a bud'e take sesi ta zuwa suke kwana ma". Mommy ta fad'a ta bar parlourn.

     Abba yana tsaye ya kasa ta'bika komai wani hali sena Mommy sam idan taso tsiya sede ya rabu da ita.Girgiza kai kawai yayi" Allah ya sawwa'ke".Ya furta tare da barin parlourn.

      Around 4:30pm Reyhana taji knock ya shigo,hijab ta zira ta tafi bud'ewa dan bata tunanin Ahmad ne.

      "Abba!" Reyhana ta kira tana me mamakin ganinsa.

      "Sannunku da zuwa ku 'karaso ". Reyhana ta fad'a ta bud'e'kofar widely.

       Walida da sauri taje ta rungumeta,itama Reyhana haka suka shiga ciki.

          "Ina yini Abba". Ta gaisheshi cikin rissinawa.

          " Lafiya lau Reyhana ". Ya amsata.

        Sageer dake gefe shima suka gaisa,se Walida dake manne da ita.

         Allah ya taimaka tana da ragowar cake dayai saura jiya se exotic d'aya ta kawo musu da ruwa." Ikram da Bassam fah?" Cewar Reyhana tana kallon Walida.

      "Suna gida su". Ta amsa.

    Ba jimawa sega Ahmad ya dawo suka gaisa ya d'an zauna a sitting room d'in suna hira da Abba.

         Da suka zo tafiya Walida tayi 'kememe baza ta bisu ba seta kwana.Ba yadda basi da ita ba " Walida ba'a taho da kayanki ba fah".Sageer ya fad'a.

         "Abba ku barta ta kwana mana na kawota d kaina". Reyhana ta fad'a.

       Haka suka ha'kura suka tafi ,Reyhana taji dad'i sosai ta samu 'yar hira.

             ***

Suna komawa gida Mommy tana parlour ita da su Bassam sun baje ice cream suna sha.

      " Abba sannu da dawowa".Yaran suka fad'a.

       "Ina Walidan kuma?" Bassam ya tambaya.

       "Mun barta can ta nace seta kwana". Sageer ya amsa.

         Mommy ko tanka musu batai ba,illa shan ice cream d'inta data cigaba.

       Suma shirin sukayi Abba ya wuce d'aki Sageer ma sashensa ya wuce.

               ***

    Walida kwai surutu har Maghreb tana hira da Reyhana daga baya ta 'karbi wayarta ta fara game. Reyhana se lokacin ta shiga kitchen girki dama kuma taliya zatayi jollof.

     Ahmad kuma ya tafi masjid har lokacin be dawo ba.Tana kammalawa ta ziba musu ,suna cikin ci ya dawo.

       " Sannu da dawowa".Reyhana ta fad'a.

       "Yawwa".ya amsa yana 'ko'karin zama kan kujera.

      Ita ma walidan sannu da dawowan tayi masa  ta cigaba da cin abincin.

      Reyhana tashi tayi ta zubo masa nashi shima tukun ta cigaba da ci tana mata labarin makaranta.

        Wajajen 9:30 Walida ta soma gyangyad'i ,d'akin gado ta kwantar da ita kamar yadda Ahmad ya bu'kata shi seya kwanta a sitting room.

      Chan cikin dare aka d'auke light gashi weather d'in da zafi kad'an Walida ba son zafi take ba tuni ta farka.

         Ga mosquito net shiyasa ta takura,Reyhana fifita ta hau yi mata sannan ta koma, ita kuwa Reyhana se wajen 4:14pm ta koma bacci.

        Ahmad koda ya tashi asubah kamar ko yaushe ya tashi Reyhana ya fita.Rashin bacci da bata samu ba yasa ta koma ba tare da ta ankare ba.

         Koda ya dawo 6:48am ya tarar bata tashi ba seda ya sake tayar da ita,da sauri ta mi'ke ganin hasken gari.

         " Ya salam!" Ta furta.

         "Tabb! Kice baccin kika koma har 7 ya kusa fa". Ahmad ya fad'a.

         Da sauri ta shige toilet tayi alwala sannan tayi sallah,nan ta yaye net d'in ta tashi Walida da 'kyar dan akwaita da nauyin bacci.

       Kafin nan 7:15am yayi, data fito ta tarar ya d'ora ruwan tea hakan ya nuna ya sauke ma na wankan.

        Kitchen d'in ta shiga tana tunanin abin breakfast dan potatoes ya 'kare gashi doya ma baze ishesu ba dan kad'an ya ragu ,tuna tana da flour kawai ta fere doyan nan da nan ta soya da ragowar egg dan shima yazo 'karshe.

        Flour d'in kuwa ta kwa'ba fanke nan da nan tunda garin da d'an rana.

       Doyar ta d'iban masa ta had'a tea ta kaimasa ,sauri-sauri yayi breakfast d'in dan yayi late 7:39am ya fita.

       Ragowar doyar ta bawa Walida ta had'a mata tea tasha, ita kuwa seda ta jira ya tashi fanken ta soya taci. Kafin tayi breakfast tayi shara ya rage wanke-wanke da sauran ayyuka.

         " Walida a ajje game d'in ga ruwan wanka na had'a maki".Reyhana ta fad'a sanda ta shigo sitting room taga tana ri'ke da wayarta.

        "Yaya bari na fad'i sena ajje". Walida ta fad'a hankalinta na kan wayar.

     Reyhana murmushi kawai tayi a ranta tana fad'in" Yarinya baki da damuwa".

      Wajen 12:00pm ta gama shirinta gida yayi tsaf,saura girkin rana kuma.

     Shinkafa da miya ta dafa dan kayan abinci sunyi 'kasa shinkafa ce ta ragu da taliya rabin carton ,se sauran kayan alatun d'and'ano dama kayan gara ne da aka had'ota dasu yanzu kuwa sun kusa 'karewa,gashi har wata ya 'kare ba'a biya albashi ba.

                   ***

    Yau Anty Asma'u tazo gidan Mommy nan take fad'a mata Walida tana gidan Reyhana.

      "Ai yau d'innan Sageer ze d'akko ta". Mommy ta fad'a.

     " Tana wani d'okin gidan Amarya ba uwadda zasu bata se shinkafa".Mommy ta fad'a.

       "Hmm yaro kenan ita a jinta za'a had'ota da kayan 'kwalama.Anty asma'u ta fad'a.

        Sageer yana jinsu shi haushi hirar take bashi ,besan lokacin da zasi dena aibata Ahmad ba sam basa ta'ba yabarsa.

        " Sageer anjima kaje ka d'auko yarinyar nan kajini ko".Mommy ta fad'a.

       "Mommy ku barta mana". Ya fad'a.

       "An'ki d'in kana kallo yau da akwai school amma Abbanka ya 'kyaleta saboda sangarta". Mommy ta fad'a cikin fad'a.

        " Toh ai gobe Saturday ".

         " Seta je islamiyya ,na fad'a maka anjima zaka d'aukota".Ta fad'a.

     Daga haka be sake cewa komai ba sema d'akinsa daya koma.

                ***

     Reyhana wajen Asr suna zaune da Walida akai knocking.Walida da sauri ta tashi ta bud'e 'kofar."Kai ya Sageer meye na zuwa d'in". Ta fad'a tana turo baki.

     Ciki ya 'karaso ita kuwa Walida kamar zatai kuka nan danan ta zauna gefe guda tana turo baki.

      "Kai Sageer da wuri haka, ni na zaci koh kayanta ta kawo". Cewar Reyhana tana d'aga labilen d'akin.

         " Mommy ce ta takura sena d'akkota". Sageer ya fad'a.
Chapter 4 · 0% Book details