← Book details Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 33

Sashe 8

Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Later wajen 4pm ya dawo ,an sayeta 16k ya saya mata 'karama 5k saura 11kya bata.

      Ahmad sanda ya dawo gida bayan yaci abinci ta d'akko kud'in.

     "Yaya kaga nace wannan kid'in me ze hana akai umma asibiti dasu".Ta fad'a tare da mi'ka masa.

       " Ina kika sami wannan d'in?"Ahmad ya tambayeta.

       "Uh..wayata ". Ta amsa.

        " Wayarki".Ya kalleta cike da mamaki.

        "Dama fa ta fara samun matsala shine na sayar na sayi wata wannan kuma sauran kud'inne". Tayi 'karya dan ba wani matsala da wayar ta samu.

       " A'a bazan kar'ba ba meyasa kikai haka ,taya zaki sayar da wayarki".Ahmad ya fad'a dan beji dad'i ba.

        "Lefi ne idan nayi hakan?" Reyhana ta fad'a kamar zatai kuka.

        "Nide na fad'a maki bazan kar'ba ba".

       Nan take Reyhana ta fara zubar da hawaye hadda shishshi'ka.

       " Kukan kuma na miye daga nace bazan kar'ba ba".Ahmad ya fad'a duk ya damu dan baya son kuka.

       "Toh kafi so mu cigaba da kallon umma a haka?"Ta fad'a cikin kuka.

        "No amma..." Be 'karasa ba ta katse sa.

      "Dan Allah Yaya ka kar'ba ,naji wataran ka bani amma yanzu ka kar'ba". Ta fad'a duk da kuwa ko wataran ya bayar ba kar'ban zatai ba tayi hakan ne dan ya kar'ba.

         Shiru yayi bece komai ba ya tafi tunanin halin da umma me ciki dan ko yanzu daya barota tana kwance.

        " Ok naji zan kar'ba,shikenan?"

       Reyhana kai ta kad'a tana murmushi,shikuwa kallonta yai  a ransa yana jin 'kaunarta ,jawota jikinsa yayi yana shi mata albarka.

         Washegari da safe yaje gidan umma ya tafi da ita asibiti, malaria ne yaci 'karfinta har ruwa aka 'kara mata se allurai da magunguna da aka rubuto mata,se yamma suka komo gida ,har 'yan siya-siye yayi mata bashi ya komo gida ba se bayan maghrib ya komo gida dama akwai wata 'yar uwassu da take a kano ita take kula da ita.

        "Ya jikin umman ?" Reyhana ta tambaya.

         "Ta samu sau'ki ammata 'karin ruwa sai maguguna da allurai dasuka bata".

         " Allah ya 'kara sau'ki,Yaya gobe zani fa na sake dubata".Reyhana ta fad'a.

         "Toh Allah ya kaimu Azizaty ta,ya babynmu?" Ahmad ya fad'a yana shafa cikin.

    Reyhana murmushi tayi itama ta d'ora hannunta kan nasa.

                 ***

    Mommy de an samu Abba ya tisata a gaba sunje duba umma ,Abba yayi mata siyayya ta dubiya suka kai.

     Hakan ba 'karamin yima Reyhana dad'i yayi ba.

      Cikin ikon Allah Umma taji sau'ki sosai.Akwai wani biki daya taso a Zaria Umma datace zata je Ahmad ya'ki yace ta ha'kura ai bata jin dad'i.

     Reyhana kuwa yana fad'a mata tace su suje mana,ba yadda beyi da ita ba ta'ki ha'kura har umma ta fad'awa ita kuwa ta goyi bayanta dole ya ha'kura.

      Reyhana se d'oki ake tun ana washegari ta gama had'a kayanta shi Ahmad dariya ma yake mata.

       "Maman baby kwana nawa za'ayi ne irin wannan shiri haka".

        " Kwana uku mana".Ta amsa.

       "Uku ? Babynmu kuma yace d'aya". Ahmad ya fad'a.

       " D'aya haba de zami fa ziyara".

       "Ziyara? Toh ai duk wa'anda za'a je gidan nasu zaki gansu gurin bikin".Ahmad ya fad'a.

         " Toh naga gari".Ta fad'a.

         "Maman baby yawo de ,babynmu baya son yawo".

      Haka sukai ta  fafatawa har sukai bacci ,ita a lalle kwana uku.

        Washegari wajen 10am suka nufi Zaria tunda 12pm za'ai d'aurin auren.

       Kafin su isa 'kafarta tayi tsami,an tarbesu cikin mitintawa sun gaisa da 'yan uwa da abokan arzi'ki,gidan wani yayan umma suka kwana washegari aka rarrakasu gidajen wasu 'yan uwan kowa yana murnar ganin matar Ahmad ,around 3:30pm yace su tafi Reyhana haushi ya kamata dan ita sam bata gaji ba.

       Wata 'yar'kanwar umma ana ce mata Zainab tare suka dawo kano da ita tunda ana hutun makaranta ,bata fi 13yrs ba wasu lokutan dama tana zuwa hutu gidan umma.

            ***
   Mommy suna zaune da Ikram tana so a turawa Reyhana wasu necklace sample ta za'ba Abba ze siya musu.Ikram koda ta duba  last seen nata taga an dad'e.

        " Mommy anya kuwa zata gani naga bata hawa fa yanzu".Ikram ta fad'a.

         "Ni ayya bata ma siyar da wayarta ba da rannan da muka je duba sirikarta 'karama ce a hannunta". Mommy ta fad'a.

        " Anya kuwa bara de na kira".Cewar Ikram.

        Bayan Reyhana tayi picking da Ikram ta tambayeta seta ce wayar ta samu matsala be.

        "Mommy wayarce wai ta samu matsala".Ikram ta fad'a still wayar na kunnenta.

            " Toh anjima Sageer zezo ya kai mata gyara ".Mommy ta fad'a.

     " Yaya sageer zezo ya kai miki gyara".Ikram ta fad'a.

        Reyhana jin haka yasa ta hau inda-inda "Uhmm..ai..ai yanzu na siyar da phone d'in dan ya 'baci sosai" .

         "OK toh dama sar'kane zaki za'ba Abba ze saya mana".

            " Toh kawai ki za'ba min ba damuwa".Reyhana ta fad'a.

        Daga haka sukai sallama,Mommy kuwa ko ba'a fad'a ba ta riga da ta gano.

           4:17pm Ahmad ya koma gida daga wajen aiki sede yau ba key a wajen gashi yana ta knocking bata bud'e ba.

         Reyhana kuwa bacci take lakadan,Ahmad har d'an 'karamin dutse ya d'auka ya bubbuga amma shiru.

       Ransa har ya fara 'baci dama a yunwace yake ga gajiya daya kwaso.

      Seda yai kusan 20min a tsaye kunnanta ya jiyo ,sede Reyhana tashi daga baccin da tai jikinta har rawa yake dan be isheta ba.

        "Mtchww!" Ta buga tsaki jin an sake yin knocking,hijab ta zira ranta a 'bace ta bud'e.....

AR²💖

        *Ha! Long page koh,i just enjoyed typing it A&R🔥*

      *Please comment,vote and shares love u all wallah😘*

  Jasko💕

*ARZI'KI RABO*

*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿-0⃣8⃣

Cikeda takaici yake kallonta a ciki-ciki yai sallama itama a hankali ta amsa ta matsa ya wuce.

     Shi ba abinda ya sake bashi haushi kamar yadda itama ta wani shareshi bako sannu da dawowa sema turo baki dayaga tanayi wanda besan dalili ba.

         Kayan jikinsa ya rage seda ya watsa ruwa tukun ya fito  da ba'kar T-shirt da blue jeans.Kitchen ya nufa ya zubo abincinsa da kansa, tana kallo ya shiga sitting room.

      Ta kula da yadda yake ta cin magani haka yasa ta shige d'aki abinta .

      "Kajimin mutum ya tashe ni a bacci da bugun 'kofa kuma yana cimin magani". Reyhana ta fad'a a  a hankali.

     Ita sam bata san ya dad'e yana bugu ba.

        Har ya gama cin abincin be nemi inda take ba illa shingid'a kan kujera da yayi.

      " Instead ta bani ha'kuri shine zata shige d'aki aiko naga meyiwa wani magana".Ya fad'a a ransa.

        A haka har akai maghrib ya tafi masallaci be dawo ba har seda yayi isha'i tukun ya komo gida dama ya fita da key d'insa.

       Sanda ya shiga cikin d'aki yaga bata ciki ,waje ya samu ya zauna.

      Reyhana lokacin tana sitting room cin abinci,taji shigowarsa sarai amma ta share dan haryanzu bata huce ba gashi dama ba wuyar yanzu tayi fushi abinka masu ciki.

      Around 9:30pm Reyhana ta fito daga sitting room, koda ta shiga d'akin.

        Yana kwance a kan gadon kuma bawai bacci yake ba.Ita kuwa toilet ta fad'a ta shiga ta watsa ruwa sannan ta zira sleeping dress nata ta hawo gadon.

      Duk abinda take yan kallonta,itama tana jin idonsa a kanta amma tayi burus kamar bata gani ba ,juya masa baya tayi tai kwanciyarta bayan tayi addu'ointa.

      Hakan ba 'karamin sake sashi tunzura yayi ba ,shima kwanciyar yayi ya juya baya.Kowa a cikin zuciyarsa da abinda yake tunani.

               ***
Washegari da asubah bayan tayi sallah yunwa ta hanata komawa ,seda ta zubawa cikinta tukun ta komo d'akin.

     "Ina kwana". Ta gaisheshi.

      " Lafiya".Ya amsa ciki-ciki.

       "Wai yaya laifi nayi koh meh?" Reyhana ta tambaya dan yadda ya amsa mata yasa taji hasushi tund ita ba haka ta gaidashi ba.

        "Bakisan mey kikai ba kenan?" Ahmad ya fad'a.

          "Kamarya ? Nifa kayiwa laifin ma,gafa yadda ka tasheni ina bacci jikina yana kyarma na bud'e amma kayi biris kamar bakasan ina gunba". Cewar Reyhana.

       " Lalle kuwa nida kika ajje a waje na shafe kusan rabin awa baki ko damu ba illa damuwa da bacci kawai".

       "Amma de ai kasani kullum da key naka kake fita, kuma ai da idona biyu bazan'ki bud'ewa ba". Reyhana ta fad'a.

     "Au haka ma zaki ce ?"

       "Toh Allah ya huci zuciyarka". Reyhana ta fad'a.

       Shi hakan ma sake 'kona masa rai yayi ,bece komai ba sakamakon kiransa da akai a waya.Koda yai picking yaji daga wurin aiki ne ogansu yana nemansa,dan haka ya mi'ke da sauri yayi wanka ya fito.

       Reyhana tana kallo ya sanya kayansa be ce mata ko 'kala ba.

      " Na tafi". Abinda yace mata kenan sanda ya zira takalmi.

      Shiru tayi har ya fice tabi bayansa da kallo.Ba abinda ta tsana irin taga ya fita beyi breakfast ba.

       Reyhana agogon d'akin ta kalla taga 7:17am ,mi'kewa tayi kan gadon ta koma baccinta.

      Reyhana se wajen 10:34am ta farka, tashi tayi ta gyara gidan yayi tsaf se lokacin ta tuna da walima ta graduation d'in saudat 'kawarta data kammala university.

     Gashi bata da isassun kud'i hannunta,tunani tayi 'kila ma da biyu yayi hakan dan ya rama shiyasa yai ficewarsa.

      Koda rana data kira wayarsa beyi picking ba kusan 2missed call,daga baya ma jitayi wayar a kashe ba mamaki kashewa yayi.Abinda tayi tunani kenan a ranta.

       Tana zaune 3,4:30 har 5 lokacin ta gama fiddarai ranta yayi matu'kar 'baci.

        Dama ta had'a wani leman tsamiyarta ,saboda haka ta tashi ta d'auko a fridge yayi sanyi gwanin sh'awa sitting room ta kai ta ajje.

     Bayan data ajje ta shige toilet, ba jimawa sega shigowar Ahmad ganin da akwai light yayi saurin shiga sitting room dan saka charge a wayarsa,a garin hakane 'kafarsa ta shura center carpet d'in lemo ya kelaye 'kasa😱

       Reyhana dede lokacin take shigowa d'akin.

      "Ya salam!" Ya furta.

   Jug d'in ya d'aga gashi tuni carpet d'in ya kusan tsotse  lemon dan haka ya mi'ke zai d'akko mopper.

       Nan fa ya lura da Reyhana dake tsaye a bakin 'kofa ko ba'a fad'a ba yasan ta hau sama(up up🔥).

      Lemanta dako sha bata yi ba tana azar'ba'bin tasha ko taji sanyi shine ya zubar mata duka goma da ashirin(😀bani nace ba Reyhana ta fad'a).

     Kan kice me hawaye tarr ya fara kwaranyowa dama tuntuni ya tsaya a ma'koshinta kawai dama ce bata samu ba yanzu kuwa tana da dalili.
Chapter 8 · 0% Book details