← Book details Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 33

Sashe 23

Arziki Rabo 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Dama sun fito sallah basu koma ba dan haka ya kamo hannunta suka zauna daga wani bench a compound d'in makarantar.Ita de Nasreen tana jin d'ar-d'ar musamman idan ta tuna abinda Ummienta tace.

        "Nide ummiena ta hanani kula mutanen waje".Ta fad'a.

        " Kinmanta ni Uncle ne? Na kawo maki wannan ".Ya ciro mata Twix guda biyu daga aljihunsa.

        Aiko da sauri ta mi'ka hannu ta kar'be" Amma karka fad'a wa Ummiena kaji".Ta fad'a harda zaro ido.

       "Toh". Ya amsa tare da kad'a kai.

        "Karatu zaka koyamini wai?" Ta tambaya tana 'bare ledar.

        "Eh amma yanzu zaku shiga aji se anjima idan kun tashi ina waje ina jira".

        " Kai zaka kaini gida?"Ta tambaya.

        "A'a".

        " Dan Allah ka kaini gida  ,kullum kullum semun dad'e ake zuwa d'aukan mu".

       "Ai zanyi hira daku kafin a zo d'aukanku".

        Kai ta kad'a tana cigaba da shan chocolate d'inta.Ba jimawa ta koma aji,kamar yadda ya fad'a seda ya jira aka tashesu.

       Tana fitowa ta ganshi a bakin gate da gudu ta 'karasa inda yake taji dad'i ganin ya jira an tashesun kamar yadda ya fad'a mata.

     Kan mota tasa ya d'orata suma sauran yaran ma'kotan nasu haka kafin driver yazo.

    Littafinta ta bud'o se nuna masa H/W d'inta take da C/W,kusan seda suka 'kara 15min driver yazo da sauri yaran suka je,Nasreen ce 'karshe sam drivern be kula bama ya jasu suka tafi ita kuwa se waving bye take wa Ahmad.

       Ya kasa dena murmushi har ya isa gida,ya ji dad'in yadda Nasreen ta sake jiki dashi dama hakan yake so.

       Yana shiga gida be jima ba ya fito waje ,Zainab ya gani tana tahowa se sauri-sauri take daga gefenta kuwa wani saurayine da alama magana yake mata amma ta'ki sauraronsa.

      Har 'kofar gida yana biye da ita ,se a lokacin Zainab ta kula da Ahmad dake tsaye .Shikuwa yiyai kamar be gansu ba dan kauda kansa yayi gefe kamar besan da mutum a gurin ba.

       "Assalamu Alaykum". Yaji anyi masa sallama.

     Se lokacin ya lura Zainab har ta shige gida.

      Hannu ya mi'ka masa suka gaisa,ita kuwa Zainab data shiga gida wuf ta shige d'aki ko Umma bata ji sallamarta ba.

       Tana cikin sa'ke-sa'kenta a d'aki taji shigowar Ahmad, kunya taji ta lullu'beta tana jiyo muryarsa yana magana da Umma gudun karya fad'awa Umma yasa tayi sauri ta fito.

       " Zainab dama kin dawo?"Umma ta tambaya.

       "Eh yanzu ban jima ba ". Ta amsa.

      Tana had'a ido da Ahmad taga yayi mata murmushi ko ba'a fad'a ba tasan ma'anar murmushin,a take ta sauke kanta katsa.

       Umma ce ta koma d'aki tabarsu a tsaye gun,Zainab ma da sauri zata juya ya tsaida ita da fad'in.

     " An bani sa'ko".

      "Yaya sa'ko kuma?" Ta tambaya.

       "Eh ba'konki na waje shi yace na fad'a miki".

        " Mey?" Ta tambaya tana had'e gira.

        "Wai yana sonki". Ya amsa.

         Bata sake cewa komai ba ta koma d'aki ,kafin ya sake wata maganar yaga ta bace masa dan haka ya koma d'akinsa.

     A d'aki tunani ta shiga yi shin wace amsa Ahmad ya bashi? Ko zeji haushi? wata zuciyarce tace mata" Be damu ba".

      Jitai ba dad'i dan batai tsammanin haka ba,a tunaninta ze nuna kishi a fuskarsa sede taga ba hakan ba harda ma yimata murmushi.

  •••

    Koyaushe Ahmad inde ya dawo daga aiki seya biya school d'insu Nasreen, ta saba dashi sosai har home work yake koya mata idan taje gida ta fad'a musu se sike tunanin ko Uncle na school ne.

     Ta 'bangaren Sageer kuwa abu kullum gaba yake ko abinci yanzu be fiya ci ba a d'aki yake zama ya'ki fitowa ga wani mugun rama da yayi Mommy tun abun baya damunta yanzu ya soma ,kuma tambayar duniya baze fad'a mata ba Reyhana ma ta'ki fad'ar abinda ke damunsa.

     Reyhana kuwa data yiwa Saudat magana akan Sameer shawara ta bata akan ta cigaba da addu'a.

      Yau wasu 'kannen Umma  banda mahaifiyar Zainab suka zo daga Zaria,sanda suka zo Ahmad baya nan se Zainab yau bata da lectures.

      Tunda take da Ahmad basi ta'ba maganar Reyhana ko Nasreen da ita ba,yau tana jinsu Sister's d'in Umma suna hirar zasi je gidansu Reyhana suga Nasreen.

     Tana daga d'aki amma kunnanta yana kwashewa,ita jitai tsoro ya shigeta kada ace fa Ahmad ya dawo da Reyhana.

       Umma tana kallo suka fita wajen 4pm,hadda yi mata siyayyar kayan biscuit.

     Sanda suka shiga Walida suka tarar a falo, ita taje ta fad'awa Mommy da tana d'akinta Anty Asma'u tazo.

       Da farko Mommy bata gane su ba seda sukai bayani.Anty Asma'u tasa Walida ta kira da tana d'akin Mommy.

                    °°°
        Ahmad daga aiki ya wuce wajen Nasreen ,yana zuwa aka tashesu.Kamar koyaushe tana ganinsa ta ruga da gudu ta d'ale shi.

      "Uncle ina chocolate d'ina?"

       "Gata".Ya d'akko a aljihunsa.

        Tana tsalle ta kar'be suma sauran abokan tafiyarta ya basu nasu.

°°°
  Reyhana datai waya da driver yake fad'a mata yana kwance baida lafiya dan haka daga gidan Saudat tayi makarantarsu Nasreen.

       Daga gefen gate tai parking ta fito ,'yan tsirarin student dake wajen ta kalla ko zata ga Nasreen.

       Daga can nesa ta hango Nasreen d'are-d'are a kan mota.Mutum taga tsaye a kusada Nasreen amma kuma ya juya baya.

     'Karasawa tayi har inda suke,seda ta 'karasa kusa tukun Nasreen ta ganta.

      " Ummie!!!"Ta kira sunanta da 'karfi.

      Ahmad daya ji ta 'kwala kira ta ambaci Ummie hakan ya tabbatar masa Reyhana ce.Cak ya tsaya ya kasa motsi balle juyowa.

     Da gudu ta 'karaso inda Reyhana take ta rungumeta.

     "Yau da kanki kika zo d'aukanmu?" Ta tambaya.

     "Eh". Reyhana ta amsa.

     " Ummie kinga Uncle".Nasreen ta fad'a tana nuna inda yake.

       Se lokacin Reyhana ta dawo da kallonta kansa.

      "Uncle kaga Ummiena". Nasreen ta fad'a.

      Ya rasa mey zeyi ,wata zuciyar tana cewa kar ya waigo ? "Toh idan ma be waigo ba ya zeyi baida choice dole ta ganshi".Ya fad'a.

     A sanyaye ya juyo idanunsa suka sauka kan Reyhana, wani irin blinking ido tayi tana so ta tantance gaske ko mafarki.

       Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi ganin ba mafarki take ba,duk cikinsu kowa ya kasa magana kuma basu dena kallon juna ba...

AR²💖

           Shocked right??
Comment
Vote
Share

Jasko💕   

🎍 *ARZI'KI RABO*🎍

*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 2⃣5⃣

   Duk cikinsu kowa ya kasa fad'ar koda 'a' ce ,daga cikin zuciyarsu kuwa tambayoyine iri-iri musamman Reyhana.

     Kamar 'kiftawar ido yaga taja hannun Nasreen sun shige mota,'ki'kam yayi be motsa ko ina ba kamar wani gunki.

       Nasreen cikin rashin nuna damuwa tayi ta waving bye ,cikin 'kan'kanin lokaci yaga wayam.Se a lokacin yayi 'kwa'kwarar 'kifta ido.

     "Meyasa ma na barta ta tafi?" Ya fad'a  a ransa.

      "Am stupid!" Ya daki saman motar.

       Gwiwa  ba 'kwari ya shige mota sannan ya bar gurin

       Reyhana da ikon Allah ta iya tu'kin motar dan hankalinta baya wajen,Nasreen da take mata hira ko sauraronta bayi take ba.Suna shiga gida taga Anty Asma'u da Mommy se maganganu suke suna kumfar baki.

        "Banda rainin hankali kai tsaye su sunzo ganin 'yarsu  bako tunani". Cewar Anty Asma'u.

         "Nasreen jeki d'aki gani ina zuwa". Reyhana ta fad'a da'kyar dan bakinta yayi nauyi.

      Ba musu ta wuce sama,su Mommy kuma lokacin sun bar hayaniyar da suke." Mommy meya faru?" Reyhana ta tambaya.

     "Yanzunnan 'yan uwan Ahmad suka fita ,saboda tsabar rashin kunya irin tasu wai gurin Nasreen suka zo harda wani tarkacen ledarsu sunan sunyo mata abin arzi'ki ca akai musu bata ci kowa irinsu neh mitsiyaci!"

    "Kuyi shekara shida baku waiwayi yarinya ba shine seyau ku kwaso tarikican 'kafarku kuce kunzo ganin yarinya". Anty Asma'u ta fad'a.

      Reyhana ta kasa cewa komai illa zame jiki datai ta haye sama dan kanta yana shirin bugawa ta rasa da wanne zata ji,ganin Ahmad koh zuwan wa'acen?

       Da'kyar 'kafafuwanta suka kaita zuwa d'akinta,a sanyaye ta zauna kan gadon Nasreen da har ta 'kwa'be uniform d'inta ,'karasowa tayi inda Reyhana take.

    " Ummie ki d'akko min kayan da zan saka".

     Sam hankalinta bayan gurun ta tafi nisan tunanin seda taji tana jijjiga mata kafad'a ta dawo hankalinta.

      "Ina zuwa ".Ta fad'a tare da mi'kewa ta bud'e wardrobe ta ciro mata.Nasreen tana gama sa kayan ta fita.

     "Shine Uncle da take magana? Meyasa se yanzu? may be aure yayi ya haifi wasu 'ya'yan shine ya tuna da Nasreen koh matarsa tasa yazo wajen 'yarsa ? Naughty brain nashi be fad'a masa abinda ya kamata ba seda.. No it can't be..what if yayi auren ai it's possible but...Ohh " Abinda yake ta mata yawa a 'kwakwalwarta kenan ,se yanzu kuma abunda su Mommy suka fad'a mata ya dawo mata.

°°°

Ahmad yana zuwa gida ya shige d'akinsa ya rufo 'kofa ,se yanzu yake daya sani.Tunani ya shiga yi koh ya kira ta a waya wata zuciyar tace"Kana gani koh magana bata had'aku ba a fili ma kenan balle waya".

     "Reyhana am sorry!" Ya fad'a a fili cikeda nadama kamar tana kusa dashi.

      Yana wannan tunane-tunanen har maghrib tayi be samu zuwa masjid bama se a gida yayi sallahr,se bayan ya idar da sallah tukun ya fita zuwa parlor.

         Umma tana zaune kujera fuskarta ba walwala shi be kawo komai a ransa bama,opposite da kujerarta ya zauna.

       Tunda ta amsa sallamarsa bata sake magana ba se yanzu.

       "Ahmad meyasa kayi min 'karya?" Ta tambaya.

       A razane ya d'ago da kai ya kalli Umma se lokacin ya kula da yanayinta.

     "Abinda kayi ka kyauta kenan? Ashe duk zaman da akai iya tsahon lokacinnan kusan shekara biyu kenan ni gani ka maida ni bansan mey nake ba koh? Ka janyo wa iyayenka wula'kanci da cin mutunci yanzu wa gari ya waya?" Se lokacin ta tsaya da magana.

      Yanzunne ya gane mey ya faru,Aunty's nashi sunje gidansu ,finally Mommy ta fad'a musu 6yrs rabonsa daya taka 'kafa gidansu Reyhana.

       "Ya Allah ka taimakeni". Ya fad'a a zuciyarsa.

    Ya bud'e baki zeyi magana Umma ta katseshi.

      "Ina tunaninka da iliminka ? Ha'k'kin 'yarka dayake a kanka duk ka mance ba ruwanka haka kake kuma jin dad'in bacci ni gani ka d'auke ni shashasha ashe kallon wawiya wacce batasan abinda take ba kake min ban isa na fad'a maka abinda zakai ba kai, gaka ka girma ka zama banban mutum koh? mahaifiyarka za kaiwa 'karya".
Chapter 23 · 0% Book details