← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 8 OF 29

Sashe 8

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Gani ta yi Baba Habiba ta nufi hanyar zauren ƙofar gida, duk cikinsu babu mai takalmi a ƙafarsa, a hankali Baba Habiba ta zare sakatar ƙofar gidan suka buɗe suka fita a hankali, suna fita suka zura da gudu babu kowa a titin saboda dare ne hakan ya basu damar gudu akan titi, gudu kawai suke ba su san inda suke saka ƙafafunsu ba.A can cikin gidan kuwa mazan sun sami nasarar haura katangar su duka uku, shigarsu gidan ke da wuya suka fara duba ɗakunan domin aiwatar da abin da ya kawo su, suna dubawa suka fahimci babu kowa a cikin gidan suka duba ƙofar gidan ganinta a buɗe yasa suka fahimci cewa masu gidan sun gudu ne da alama sun musu laɓe ko dai makamancin haka A take suka mara musu baya domin sun ci alwashin sai sun aiwatar da ƙudirinsu a yau ɗin nan!

Ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane haka gudu da juriyar da namiji zai yi ba lallai ne mace ta yi ba.Wannan dalilin ne yasa mazan nan suka fara hango su Ridallah da ke sheƙa gudu, sai dai akwai tazara a tsakaninsu.Baba Habiba da yake suna gudu tana waiwayowa amma duk da layikan unguwanni da suka yi canjawa amma sai da suka lura suna biye da su hakan yasa suna shan wata kwana kafin mazan su ƙaraso Baba Habiba tasa suka shiga cikin wani kwalbati wanda babu ruwa a ciki suka kwanta rubda ciki yadda ba za a gansu ba suna fata da addu'ar kar Allah yasa su gansu domin babu mai cetonsu sai Allah, gashi talatainin dare kowa yana gidansa yana bacci.

Mutanen nan na ƙarasowa kwanar nan su duka ukun suka tsaya, suna ta waige-waige sai haki suke na gajiyar gudun da suka yi kamar an sa su dole. Tafiya suke suna ɗan duba wa amma ba su gan su ba, haka suka zo har dai -dai kwalbatin nan suka tsaya, gaban Baba Habiba da na Ridallah sai bugawa yake da ƙarfi suna fatan kar Allah yasa su gansu.Ɗaya daga cikinsu ne yave zai yi fitsari dan haka ya ƙarasa bakin kwalbatin da su Ridallah suke, daga tsaye ya shiga yin fitsari a cikin kwalbatin, su Ridallah fuskokinsu suka sanya a tafukan hannayensu suka rufe suna jin yadda mutumin nan ke tsula fitsari a jikinsu domin fitsarima ba wai a wuri ɗaya yake yi ba kawai wasa yake da fitsarin yana watsawa ko ina, har sai da ya gama fitsarin sannan ya gyara wandonsa, sai ya juya ga sauran yace

"ina ga fa sun bi wancan layin" Ya faÉ—a yana musu da hannu.A guje suka tafi dan duk a tunaninsu su Ridallah suka marawa baya.

Suna tafiya, jin su Baba basa jin motsin kowa alamar sun yi nisa haka suka tashi suka fito daga cikin ramin, basu damu da fitsarin da ke jikinsu ba dan burinsu kawai su tsira da mutunci da rayuwarsu.Hanya suka canja suka cigaba da gudu har sai da suka yi nisa sosai, dan gabaɗaya ma hanyar barin garin suka ɗauka dan sun tsorata sosai haka suke gudu ga tsananin gajiya sai da suka yi nisa da gari sosai sannan suka samu wata ƴar siririyar hanya suja bi hanyar ga tsananin duhu haka suka shiga wurin a ƙarƙashin wata bishiya suka yada zango suna ta haki saboda gudun da suke yi.Haka suka kwana a wurin cike da tsoro da fargaba, da asubar fari suka yi taimama suka gabatar da sallar asuba, da duku-duku suka cigaba da tafiya dama saboda kar wanda ke nemansu suje tashar mota shi yasa suka ƙi zuwa tashar sannan yanzu ma suna iya biyo bayansu, sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa sannan suka tsaya a hanya bakin titi suka tsayar da motar haya suka shiga direban ya tambayesu garin da za su sauka Baba Habiba ta ce garin Gumel.

Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa sannan hankalin Baba Habiba ya ɗan kwanta, ita kwa Ridallah dama tun da ta ɗora kan ta akan cinyar Baba sai wani bacci mai nauyi mai cike da tarin gajiya ya ɗauketa saboda basu runtsa ba.Har sai da suka shia cikin garin Gumel sannan ne Baba ta tasheta, a nato aka sauke su Baba ta kunce gefen zaninta da akwai kuɗin da ta ƙulle ta ɗauka ta baiwa mai mota.Napep suka tare suka shiga Baba ta ce a kai su unguwar ɗantanoma, a dai-dai wani gida aka saukesu ta sallami mai napep ɗin suka sannan suka shiga cikin gidan.

Sallama Baba ta yi, aka amsa musu tare da basu izinin shiga, suna shiga matar gidan ta ce

"Habiba?" Ta faÉ—i hakan cike da mamaki akan fuskarta.

Murmushi Baba ta yi ta ce

"Na'am Rahma"

Cikin kulawa ta musu iso har cikin É—aki tana ta faman musu sannu da zuwa tare da nuna jin daÉ—inta da ganinsu.Ridallah ce ta fara gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da nuna jin daÉ—inta.Sannan suka shiga gaisawa da Baba Habiba cikin kewa da yaushe gamo.Ruwa ta gabatar musu duk da akwai tarin tambayoyi birjik a bakinta dan ganinsu da ta yi wujiga-wujiga ko takalmi babu.

Bayan sun ɗan huta Rahma ta ce Ridallah ta shiga wanka, ba musu kwa ta shiga dan lokacin kusan sha biyu na rana dama watan buƙatar watsa ruwa a jikinta.Bayan shigarta wanka Baba ta shiga yiwa Rahma bayanin dalilin barowarsu hadejia , Rahma ta jimanta abin tare da yiwa Baba jaje akan abin da ya so samun su tare da murna akan tsallake rijiya da baya da suka yi.

A nan Rahma ta shiga yiwa Baba bayani akan
tun bayan mutuwar mijinta aka bata timunin takaba take zaune a gidan sai Æ´an siye d siyarwa da take da kuma aikin abinci a wata makarantar kwana ta mata da take cikin garin Gumel É—in.

MMN AFRA😍😘

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Page1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣

_Hajiya Hauwa_

Zaune take a bakin gado ta haɗa hannaye biyu a kumatun ta, ta yi tagumi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa, abubuwan da suke faruwa ba ƙaramin ɓata mata rai suke ba ace kullum magana ɗaya yanzu tun da class mate na Iftihal suka kammala primary school Alhaji ya sakota a gaba wai da gangan take hana Iftihal ɗin ziyartar makaranta yanzu gashi nan tana neman ta mata asara.

Iftihal ɗin ce ta shigo ɗakin ko sallama babu bare neman izini, sanye take da wata doguwar riga ƴar kanti wacce tsayinta iya gwiwarta ne, sai phone ɗinta riƙe a hannunta tana jin waƙa, headphone ɗin ta zare daga kunnenta, sannan ta ɗan buga jikin Auntyn nata a ɗan firgice ta ɗago domin kwa ta yi nisa cikin tunani, kallonta Auntyn ke yi tana ƙarewa gabaɗaya jikin Iftihal ɗin kallo kamar dai yau ne ranar farko da ta fara ganinta sosai yarinyar halittar ta da surorinta ke haɓaka kamar wacce ta ke shirin kammala secondry school kallonta take daga sama har ƙasa tana hasasho yadda idan ta kasa hajarta za ta samu ciniki sosai da kuma riba mai tarin yawa, wani murmushi ne ya maye gurbin ɓacin ran da take ciki wanda hakan yasa Iftihal ɗin cewa

"Aunty yanzu nan fa kika yi shiru tare da yin nisa a cikin tunani amma kuma yanzu gashi kina kallona kina murmushi"

"Iftihal kenan akwai dalilin da ya sani shiga cikin damuwa, wanda ba komai bane hakan illah yadda Abienki ke takura min akan rashin zuwanki makaranta, amma nasan ba komai ke sanyashi yin hakan ba sai rashin sani wanda ya fi dare duhu! Baisan irin ƙudurin da nake da shi akan ƴata ba shi yasa yake faɗan rashin zuwanki makarantar.Amma kuma dana kalleki sai na tuna da wani abu wanda wannan abun shi ne ya sanyani murmushi" Aunty ta kai ƙarshen maganar tana dafa kafaɗar Iftihal ɗin da ta zaunrta kusa da ita tana murmushi.

"Hakane Aunty amma kuma sai in ke ganin kamar koma menene a bayan karatuna yake domin ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa kuma shi ne sinadarin zaman duniya har ma da lahirar baki ɗaya domin ba fa boko kaɗai kika hanani zuwa ba har da islamiya, kuma kullum in na tambayeki menene kudurin naki a kaina bakya faɗa min"

"Kar ki damu Iftihal ni dai nasan babban abin da ke sanya mutane neɓan ilimi a wannan zamanin shi ne kuɗi! To kuwa indai kuɗi ne tabbas babu makawa har sai kin taka naira da ƙafafunki, kuma batun ilimi gishirin koma menene duk wannan bai taso ba domin a wannna ƙasar tamu masu yanzu idan da za a ce a lissafo wanda suka kammala karatunsu amma basu samu aikin yi ba yo wallahi lissafasu ma kaɗai aiki ne, dan haka ki kwantar da hankalinki kuma indai kudurina ne a kan ki zan faɗa miki nan ba da daɗewa ba domin na hango lokacin na nan tafe ya ma kusa zuwa"

"To shikenan Aunty na yarda domin kuwa uwa ba za ta taɓa yin abin da za ta cutar da ƴarta ba"

Wani murmushin Auntyn ta sake yi domin Allah kaÉ—ai ya san kudurin da ke ranta, kafin ta ce

"Yawwa Iftee na shi sa bani da tamkar ki"

"Ni ma haka Aunty shi sa ma kika ga na fi bin umarninki fiye da na Abie na"

Wani daÉ—i ne yasa Auntyn sanya hannu ta rungume Iftihal É—in suna dariya a tare.

Bayan sun É—an tattauna Aunty ta shiga koyar da Iftihal É—in tafiya, da kwarkwasa da dai abubuwa duk da Iftihal É—in bata san manufar hakan ba amma dai tana jin daÉ—i a ranta ganin mahaifiyarta na koya mata abubuwa da kan ta.

_Momma_
Chapter 8 · 0% Book details