← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 17 OF 29

Sashe 17

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Tana dab da ƙarasowa saitin inda suke Hizbullah ya dawo daga shork ɗin da ya shiga, cikin zafin nama ya tafi gareta yana zuwa kawai ya sha gabanta cikin wata iriyar murya ya fara magana.

"Ridallah dama kina raye? Ya aka yi kika zo ƙasar nan? Yaushe kika yi watsi da tarbiyarki kike irin wannan shigar Ridallah, yanzu ace ko tunani na ma bakya yi kin manta da ni ina nan ina cikin damuwar rashin sanin takamai man inda kike, a raye ko a mace amma kina nan lafiya ƙalaw hankali kwance kin...

"Wai ƙwalƙwalwarka ta taɓu ne? Ya daga ganin mace ka zo kana mata wasu surutai cikin gushewar hankali, shin ka manta ba a Nigeri'a kake ba? Ko kuwa wannan ta maka kama da bahaushiya dan Allah ka rufa mana asiri Hizbu" Abulkairi da ya ƙaraso gabansu ya ce yana bin Hizbu da kallon takaici, ita kwa Iftihal da ta langaɓar da kai gefe idanu kanne fuska a yatsine dan ita takaici ne ma ya hanata magana dan tana jin komai su ne ke mata kallon kamar ba bahaushiya ba.

"Wai ni kake yiwa eaÉ—annan maganganun? Shin ka É—auka bana cikin hayyacina to Ridallah ce wannan kuma ni nasan tana jin hausad shi yasa ka ga ina mata magana, kai...

Ƙaran wayar Iftihal ɗin ne ya katse Hizbu daga maganar da yake ƙoƙarin ƙarasawa.Kallonsu ta yi tare da banka musu wata uwar harara kafin ta buɗe baki ta ce

"Dallah malamai ku ja jikinku a nan, ko an faÉ—a muku nan ma Nigeri'a ce inda kuka saba yaudarar Æ´anmata to ko a Nigeri'a ai na wice ajinku da gani ma wannan gwabnati ce ta biya muku karatu kuka samu damar ketowa hazo"

Ta faɗa tana gyara glases ɗin fuskarta.Baki sake Abulkairi ke kallonta jin hausa a bakinta kamar jakin garinsu Kano dan bai taɓa tunanin ta san inda hausa ma take ba ganin hasken fatarta da kuma yanayin shigarta duk da musulman ma na irin shigarta a nan ɗin ma amma ko hula suna sanyawa su rufe kan su ko ɗankwali amma ita haka gatsal kamar inyamura.

"Au bahaushiya ce ke ashe, to koma menene waye ma zai so mace irinki ko a ƙafa aka ɗaura mana ke sai mun kunce, shi ma wannan dan bashi lafiya ne amma mai zai yi da ke ba zia taɓa ƙaunark...Hannu Hizbu yasa ya rufewa Abulkairi baki yana jin kamar ya hau shi da duka.

"Wai me yake skaa kake min haka ne ya za a yi macen dana fi ƙauna duk duniya bayan uwata ka ce bana ƙaunar...

Hannun da Iftihal ta ɗaga za ta ɗauke Hizbu da mari Abulkairi ya yi saurin damƙe hannun shi ya dakatar da Hizbu daga maganar da yake yi

MMN AFRAH

Page3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣

"Ridallah ni za ki mara?" Hizbu ya ce cikin mamaki yana ƙanƙance idanu, dan shi ganin abin yake kamar almara, yana gani wai Ridallah ɗinsa ce ke nuna bata san shi ba har tana ɗaga hannu za ta mareshi taɓɗi lallai akwai lauje cikin naɗi kenan dama ba son shi take ba? Kenan dama so ne na yarinta yanzu ta girma idanunta sun buɗe ta manta da shi ta barshi shi yana fama da tunaninta kullum cikin kallon ɗankunne da flower da ta bashi yake ba ya son ko kaɗan ya manta da ita ko da na second ɗaya ne dan yana ganin ya ci amana ya ci amanar ƙaunar da take masa da ma wacce yake mata baki ɗaya.

Kallon shi ta yi a raine tare da buga wani uban tsaki, ta fido wayarta da ke ta faman ƙara daga kiran ya katse sai wani ya shigo, tana dubawa ta ga Alhajin nan ranta ya ƙara ɓaci dan tana ganin duk shi ya jaza mata wannan bala'in da sun wucewarsu Hotel da duk haka bata faru ba yanzu gashi nan ya sanya wannan mai kama da mahaukatan yana kiranta da wani suna da bata ma taɓa jin mai irinsa ba.

"Ina jinka" Shi ne kawai abin da ta ce.

"Ya na jiki shiru ko dama baki taho ba?" Alhajin ya tambayeta daga ɗaya ɓangaren.

"Ka taho wajen hanyar fita ina wurin wani ya hanani tafiya" Ta ce dan bayan ta ɗaga wayar ma ta yi ƙoƙarin tafiya amma Hizbu ya janye Abulkairi daga gabansa ya je ya sha gabanta zai cigaba da jefa mata tambayoyi marar kai da ƙafafu.Tana kashe wayar ta kalli Hizbu cikin takaici ta ce

"Za ka gane shayi ruwa ne dan sai nasa an kulleka an koya maka karatun da baka da ilimi a kan sa tun da baka da hankali" Ta ce tana É—auke idanunta daga kallonsa.

"Shikenan Rida na ji baki sanni ba kamar yadda kika nuna amma inaso ki faɗa min ina Baba take shin tana raye? a nan ƙasar take ko tana Nigeri'a?" Wani kallon baka da hankali ta masa ta ɗauke kai dai dai nan Alhajin ya ƙaraso dan ta tura masa hotonta yana hangota ya ganeta.

Babban mutum ne dan da ganinsa ma ya haifi Iftihal ɗin sanya yake da wandon jeans da riga mai dogon hannu sai wani uban ƙaton tunbinsa tari guda yana reto kana ganinsa kasan kuɗi sun sami wuri sun tare.

"Baby Iftee menene hakan me ke faruwaa ne?" Ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta dan yana ganinta ya ji wata kasala ta baibayeshi, ganin irin shigar da ta yi mai bayyana surorin jikinta.

"Kalli wannan baƙauyen ne yake kirana da wani suna ya kafe dole ya sanni bayan ni ko a mafarki ban taɓa ganin ko da mai kama da shi ba" Ta kai ƙarshen maganar tana wani karkaɗa jiki dan Alhajin ya ji daɗin ɗaukan mataki.

Wani haushi da kishi ne suka turnuƙe zuciyar Alhajin lokaci guda ya kalli Hizbu da ya babbake a gaban Iftihal ya ce

"Malam halan daga turu ka fito ko? Ka taɓa ganin yadda ake niƙe mutum a maidashi dambun nama? To akan wannan yarinyar zan sanya a dandaƙa ka har sai cikinka ya haɗe da bayanka, dan haka ka fita harkarta ko a mafarki babu kai babu ita" Yana kai ƙarshen maganar yasa hannu ya hankaɗa Hizbu gefe guda sannan ya kama hannun Iftihal suka juya suka fara tafiya dan maimakon su shiga ciki hanyar fita suka nufa, ya maida hankalinsa kwacakwam kan ta ita kwa sai wani rausaya jiki take dan ƙara ɗauke masa hankali dan tana so ta samu kuɗaɗe masu yawa daga wurinsa dan Auntynta ta faɗa mata cewa ta tabbatar ta yi iya yinta dan ta wanki gara.

Hizbullah ganin Alhajin nan ya ƙara saka masa damuwa kenan Ridallah ta ma wuce inda yake tunanin wato shigar jikinta kaɗai da kuma yadda Alhajin nan ya kamata ya tabbatar da ta sanya kan ta a wata rayuwa dan da gani ba mijinta bane dn da mijinta ne da yace masa mai ya haɗashi da matar aure? Yana hango sun shige ƙofar ta rufo cikin hanzari ya fara taku zai bi bayansu dan yau sainya ga abin da ya turewa buzu naɗi ba zai taɓa barin Ridallah ba, taku ɗaya biyu Abulkairi ya yi ya damƙi rigarsa dan shi abin na Hizbullah ya fara bashi tsoro dan ya tabbata dai Ridallah ta fara masa gizo.Duk da dai bai taɓa ganin yarinyar ba ko a hoto bare ya ce ita ce ko ba ita ba ce dan Hizbullah memorinsa mai ɗauke da hotunansu ya faɗi a ranar da zai baro Nigeri'a dan haka yanzu ko hotonta bashi da shi, amma abin da ke baiwa Abulkairi mamaki me yasa bata taɓa masa gizo akan duk mutane ba sai akan wannan lallai akwai ayar tambaya tun da dai yarinyar bahaushiya ce alamu sun nuna ƴar Nigeri'a duk da a yadda Hizbu ke bashi labari ba ya jin yarinyar za ta yiwa Hizbu haka amma kaidin mata yawa gareshi kuma rayuwa da burika suna canja mutum.

"Ka saka ni kar su ɓace min"Hizbu ya ce cikin ɓacin rai.

"Haba abokina ka dawo hayyacinka mana me yasa kake hakane, shin ƙauna da tunanin Ridallah har zuciyarka ta fara ɗakko fuskarta tana ɗorawa a gangan jikin wata kana yiwa wata kallon Rifallah?" Abulkairi ya faɗa yana kama duka hannayen Hizbu da ƙarfi ya riƙe dan ya ga sai fisga yake yana so ya ƙwace ya bi bayansu.

"Abulkairi ka sake ni na ce idan suka ɓace min sai ka gwammace baka sanni ba"Hizbu ya ce yana zazzare idanu dan ya kasa ƙwace riƙon da abokin nasa ya masa saboda rauni da damuwar da ya tsinci kan sa a ciki sai ya ji gabaɗaya ƙarfinsa ma ya bar gangan jikinsa

*Gumel*

Ridallah har an shiga Senior secondry scul yanzu haja tana S.S 1 sun yi hutun first term dan haja yanzu tana gida hutu ake yi.Sanye taje da doguwar rigar jar atamfa an mata manyan fulawoyi baƙaƙe da la'asar sakaliya ne, share tsakar gidan take cikin nutsuwa.Sai da ta gama sharewa tas ta kwashe sannan ta wanke ƙafafunta da hannunta sai kuma ta je ta iza wutar da take dafa miya dan har ta gama tuwo, da ta gama wanke -wanke sai ta kwashe tuwon shi ne ta yi shara.

ÆŠakinsu ta nufa inda Baba Habiba take dan Mama Rahma ba ta nan ta fita unguwa gidan barkar haihuwa, zaune ta samu Babarta ta ta yi shiru shigowar Ridallah ya katse mata shiru da take yi.

"Wai Baba ko zafi bakya ji kin zauna a É—aki ga tabarma can na shinfiÉ—a miki a inuwa ki fita kisha iska amma kin zauna a É—aki kamar boka" Cewar Ridallah tana murmushi ta samu wuri ta zauna a kan katifar da ke lailaye da shinfiÉ—ar wankekken zanin gado dan Ridallah ba dai tsafta ba komai nata tsaf gwanin sha'awa.

"Kawai dai na fi son zaman É—akin ne"Baba ta faÉ—a cikin sanyin murya.

Ɗago kai Ridallah ta yi tana kallon mahaifiyarta ta dan kwata-kwata amsar ba ta gamsheta ba dan ba haka Babar ta saba mata magana ba musamman ma ta kan mata barkwanci su rinƙa dariya abinsu.

"Baba wai ko bakya jin daɗi ne yau tun safe nake ganinki cikin damuwa?" Ridallah ta ce tana matsowa kusa da Baba ta ɗora hannunta a kan cinyar Baba, hannu Babar ta sanya ta riƙo hannun Ridallah ta ce
Chapter 17 · 0% Book details