Sashe 6
Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Zuwanta da wata biyar sai ciki ya ɓullo a jikin Hajiya Azima, hankalinta ya yi matuƙar tashi haka suka dinga shigi da fice akan kar ta haihu amma cikin hikimar ubangiji lokacin haihuwa na yi ta haifi ɗanta namiji a asibiti sai dai kwanan yaton ɗaya a duniya ya amsa kiran ubagiji.Murna a wajen Hajiya Hauwa ba a cewa komai sosai ta yi farinciki.Hajiya Azima kwa ta ji babu dali ganin yadda suka ƙwalla fa rai akan cikin har ma da ɗan lokacin da ya zo duniya ita da Alhaji Hamza da duk wani masoyinta, amma haka suka fawwalawa Allah komai.
Sai da Hajiya Azima ta shekara shida da haihuwar ɗan da ya koma, sai kuma ciki ya bayyana a jikin Hajiya Hauwa, sai wani iyayi da sanabe take wai ita mai ciki za ta haifi magajin Alhaji ya gaji dukiya, shi ne fa da cikin ya isa haihuwa ta haifi Amina ana kiranta Iftihal.Hajiya Hauwa tun da ta haifi Iftihal take zaton Alhaji zai juyawa Hajiya Azima baya saboda bata haihu ba sai ta ga saɓanin hakan dan babu wani abu da ya canja hakan shi ne ke baƙanta mata tana ganin kenan dai duk da ta haihu bata samu martaba da kimar da Hajiya Azima ta samu ba a wurin Alhajin.
sai kuma ta fara zargin ko Alhaji ya fi ƙaunar a haifa masa namiji, shi yasa take ganij bata samu wani matsayi da take son ta samu a wurinsa ba.Amma kuma daga baya dai ta fahimci Alhajin bashi da wani zaɓi sai abin da Allah ya bashi ko mace ko namiji duk yana so hakan yasa take fatan Allah ya ƙara bata haihuwa ta haifi namiji duk da tana jin tun da Hajiya Azima bata haihu ba babu yafda za ayi ta haɗa kan ta da ita duka da cewa mace ta haifa.
wannan kenan.
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
💕ALAƘAR YARINTA💞
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
NA
MMN AFRAH
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
Page 1ï¸âƒ£3ï¸âƒ£&1ï¸âƒ£4ï¸âƒ£
_Hizbullah_
Bayan shekaru biyar
Shaƙuwarsa da Ridallah kullum ƙaruwa take, hakan yasa gabaɗaya bashi da wani wanda ya shaƙu da shi sai Ridallah, bayan iyayensa Umma Sadiya, da kuma mahaifinsa Malam Auwalu,babu wani wanda ya shaƙu dashi sai Ridallah Ita ma Ridallah haka ne a nata ɓangaren in ban da mahaifiyarta Baba Habiba dan mahaifinta ya rasu sai mahaifiyarta kaɗai ce a raye.
A haka suka taso ko yaushe suna tare babu abin da ke raba su sai bacci, tare suke zuwa makarantar boko tare suke zuwa islamiya, tare suke cin abinci tare suke komai idan ɗaya bashi da lafiya to ɗayan ma haka zai wuni a kwance wani lokacin ma shi ma ɗayan kamuwa yake da jinyar da ɗayan ke yi wannan shi ne babban abin da ya ƙara sanya iyayensu ƙarfafa zumuncin maƙotaka a tsakaninsu dan un ban da maƙotaka babu wani abu da ke tsakanin su na ƴan uwantaka.
Rayuwa na ta tafiya, da kaÉ—an -kaÉ—an ranaku ke rikiÉ—ewa su koma sati, sati ya rikiÉ—e ya koma wata da sannu su ma watannin ke haÉ—uwa su bada shekara hakan ya kan sa shekarar ta haÉ—u da wata shekarar har su bada shekaru.
Hakan ne yasa wucewar shekarun ya kawo mu lokacin da Hizbullah ya kammala karatunsa na secondry school, a lokacin Ridallah tana primary 5 dan dama lokacin da take primary 1shi kuma yana J.s.s 1. Yana zaman jiran fitowar jarabarwar su ta SSCE sai kuma wani mummunan abu ya faru, wanda ya yi sanadin wargaza gabaÉ—aya farincikin sa da ma sanya mahaifansa cikin damuwa saboda halin da ya tsinci kan sa a ciki. A wata ranar asabar ce aka tashi aka nemi Ridallah da mahaifiyarta Baba Habiba aka rasa babu wanda ya san inda suka tafi, dan ko kaya ma ba su É—auka ba haka suka tafi gidan ma ko rufewa ba a yi ba.
Sosai Hizbullah ya shiga damuwa da ƙunci na tashin hankali, dan yanzu ya daɗe da gano cewa ba wai shaƙuwace kawai tsakaninsa da Ridallah ba tabbas akwai wata ɓoyayyar soyayya a cikin zuciya, Umma Sadiya sun rasa yadda za su yu dashi sun yi lallashin sun yi faɗan sun yu lallamin amma dai Hizbullah ya yi nisa sosai baya jin kira.Da yake lokacin da Baba Habibabta dawo gidan da ke kusa da na su Hizbullah, lokacin Hizbullah yana ƙarami bai sani ba amma dai da wasu ƴan rani ne a gidan mata da miji da yaransu to da suka koma garinsu sai Baba Habiba ta kama gidan dan dama gidan haya ne me gidan yake bayarwa haya.
Dan haka Umma Sadiya ta shiga masa bayanin duk yadda abun ya faru tun daga lokacin da Baba Habiba ta dawo gidan da zama lokacin Ridallah tana ƴar jinjira, sosai sabuwar haihuwa ce, to lokacin ne da Hizbullah ya ƙyalla ido ya ga Ridallah sai yake zuwa gidan wurinta.Ganin halin da ya shiga har ta kai ga kwantawa jinya dan duk inda suke zaton za su gan su sun cigita amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa.Hakan ne yasa Malam Auwalu ya nemi mai gidan da Baba Habibar ke zaune domin jin ko daga ina Baba Habibar take tun da shi ya bata hayar gidan, amma abin mamaki mutumin yace wallahi bai san daga inda take ba, shi dai kawai abu ɗaya ya sani maƙocinsa ne ya haɗa shi da ita, shi ma kuma maƙocin ba wai ya san ta bane kawai dai ta je wurinsa ne akan tana neman taimakon inda za ta zauna ko da gidan haya ne tana so wai mijinta ne ya rasu ya barta da tsohon ciki shine kuma bayan ta haihu ƴan uwan mijin suka koreta akan wai ba za su bata gado ba, hakan yasa ta baro garinsu ta dawo nan.Shi ma tausayinta yasa ya haɗani da ita na bata gidan ta zauna amma ko kuɗin hayar baya karɓa.
Wannan jawabi da Malam Auwalu ya zo da shi, shi ya ƙara saka Hizbullah a cikin matsananciyar damuwa, dan dama yana tunanin a wurin mi gidan za a samu ɗan labarin garin da suka fito dan abi sawu to kuma sai aka samu akasin hakan.Da farko ma an yi tunanin ko kidnapers ne suka ɗauke su amma daga bisani an fahimci ba haka bane.Duk wanda ya ga Hizbullah sai ya matuƙar tausaya masa saboda rabuwa da abin da ka shaƙu ba ƙaramin abu bane, akwai damuwa sosai duk ya ƙare ya yi baƙi baya iya cin abinci kullum yana keɓance a ɗaki dama ba wani abokai gareshi ba Ridallah ita ce aboki ƙawa sannan ita ce komai nasa.Yanzu kwa da bata nan sai ya zama abin tausayi.Kullum yana ɗaki a rufe yana kuka rashinta ji yake zuciya da jijiyoyinsa ba za su taɓa iya jure rashinta ba, idan son ganinta ya ciyoshi haja zai fita ya yi ta yawo wuri-wuri yana nemansu gani yake kawai zai iya ganinsu idan ya gaji da yawo sai ya ya je bakin ruwa ya zauna masu kamun kifi suna ganin kamar zuwa ya yi domin yake kallon yadda ake kama kifi amma shi bai ma san me suke ba gangar jikinsa ce a tare da su amma zuciyarsa ta lula duniyar tunani da jimamin halin da ya tsinci kan sa a ciki na rashin abar ƙaunarsa ƙanwarsa wacce ya shaƙu da ita Ridallah.
A wannan hali da yake ciki ne jarabawarsu ta fito ya yi ƙoƙari sosai, domin ya cinye jarabawar gabaɗaya, amma shi ko murnar hakan ba ya yi sai dai iyayensa ne ke ta murna da farincikin hakan.Ganin hakan da Malam Auwalu ya yi, ya samu abokinsa Malam Iro da maganar halin da Hizbullah ɗin ke ciki, dan yana jin tsoro kar damuwar da yake ciki ta shafi karatunsa.Malam Iro ya baiwa Malam Auwalu shawara akan ya sanya Hizbullah ya cike scholarship ko Allah zai sa ya samu idan ya samu ya fita wata ƙasar karatu zai fi maida hankali ga karatun nasa idan ya ga ya yi nisa da ƙasar ma baki ɗaya ba kamar anan ba ko yaushe zai ke tunanin zai ganta ko zai haɗu da ita.Wannan shawara ta yiwa Malam Auwalu daɗi sosai dan yana ganin hakan shi ne mafita dan ita damuwa a cikin zuciya take babu wani wanda zai iya cirewa wani daga zuciya sai ko a taya mutum da addu'a akan Allah ya cire masa.
Duk da Umma Sadiya bata ƙaunar Hizbullah ya mata nisa domin kuwa shi kaɗai ne ɗan da Allah ya mallaka mata, amma saboda suna so ya samu kyakkyawar rayuwa da ilimi mai nagarta hakan yasa suka amince masa ya cike form ɗin schoolarship ɗin amma a ɓangaren Hizbullah shi dai bashi da wani zaɓi dan shi komai yanzu ba ya jin daɗinsa, sai dai baya so kwata-kwata ya bar ƙasarsa ta haihuwa saboda ya san akwai ɓarin jikinsa, mahaɗar rayuwarsa burin zuciyarsa a cikin Niger'a wato Ridallah.
Cikin ikon Allah Hizbullah yana daga cikin wanda gwabnati ta biya wa karatu zuwa ƙasar china, iyayensa sun yi matuƙar murna da sanya albarka a cikin lamarin.Haka aka yi ta shirye-shirye aka yi passport sannan aka masa biza da komai da komai har Allah ya kawo ranar tafiyar, ta Dutse da ke Jigawa State za su tashi haka iyayensa suka masa rakiya har airport ɗin ya yi sallama da iyayensa suna masa fatan alkairi suna kukan rabuwa da shi, shi kuma kuka biyu yake ɗaya kukan rabuwa da iyeyen nasa ɗaya kuma kuka rabuwa da ƙasar da masoyiyarsa ke ciki tun da har yau babu labarin su Ridallah ɗin.