← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 14 OF 29

Sashe 14

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

GabaÉ—aya Malama Zainab ta ruÉ—e da ganin mahaukaciyar dan duk tunaninta ma mutuwa ta yi, Malam Idin ne ya shiga kwantar mata da hankali akan ba mutuwa ta yi ba haka aka watsa mata ruwa Malam É—in ya shiga tofa mata addu'a cikin iko da hikimar ubangiji sai ta kawo hankali.Tun da ta falka take ta bin su da ido, amma bata ce komai su kuma dama sun san mahaukaciya ce dan suna ganinta a layin duk da ba wata hauka tuburan take ba sai dai kana ganinta kasan tana da gushewar hankali.

Ganin alamomin yunwa a tattare da ita yasa Malama Zainab zubo mata abinci ta kawo mata, Malam Zainab na ƙoƙarin ajiye mata abincin sai ta sanya hannu ta warci kwanon abincin, cikin sauri ta sanya hannu tana ci hannu baka hannu ƙwarya, Malam sai jijjiga kai yake alamar tausayi Malama Zainab kwa ban da hawaye babu abin da ke zuba daga idanunta saboda tsabar tausayi da kuma ƙara godewa Allah da take da ya iyota cikin masu hankali lallai komai Allah ya baka yana daga cikin baiwar ubangiji.

Dan mutane da dama ba sa gane baiwa da ni'imar da Allah ubangiji ya musu ba wani kullum bashi da burin da ya wuce suke kallon wata ɗinbin dukiya da gidaje da tarin motoci da Allah ya baiwa wasu, suna mantawa da hatta lafiya da Allah ya basu babban arziƙi ne.Lafiya idan aka karɓeta daga bawa aka jarabceshi da rashinta, sai ki ga duk tarin dukiyarsa ya ƙarar da ita a neman magani amma lafiyar bata samu ba shi yasa idan Allah ya baka rai da lafiya to ka gode masa duk wani abun duniya samamme ne kuma ƙararre matuƙar kana da rai da lafiya da rufin asirinka ka ɗauke idanunka daga kan abin duniyar mutane Allah kai ma yana sane da kai wani ma abin da zai ci gagararsa yake amma kullum cikin godewa Allah yake Allah sa mu da ce.

"A gaskiya Malam sosai wani imani ya ƙara shiga ta ganin halin rashi na hankali da matar nan take ciki, lallai rai da lafiya, hankali ji da kuma gani su kaɗai Allah ya baka to ya baka babban kyauta! Duk da waɗan nan abubuwan da na lissafa abin tambaya ne ga duk wanda aka baiwa su" Ta faɗi hakan ƙwalla na cikowa daga idanunta ganin yadda mahaukaciyar ke cin abincin ko na bakinta bata cinyewa ba take ƙara tura wani.

"Wannan haka yake Zainabu amma mutane ba ma la'akari da hakan kuma wasu ba sa amfani da abubuwan wajen gyaran lahirarsu, suna duk abin da suka ga dama da su"

"To Allah ya ganar da mu gaskiya, ya bamu ikon amfani da baiwar da ya mana ta hanya mai kyau"

"Amin" Cewar Malam yana sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, tare da kallon mahaukaciyar da ta kammala cin abincin ta yi wurgi da kwanon, ta shiga waige-waige da alama ruwa take nema.

"Zainabu ki É—akko mata ruwa "

"To Malam" Zainabun ta ce tana tashi ta ɗakko ruwan a wani kofi mai ɗan girma ta miƙa mata madadin ta sha ruwan sai kawai ta karɓa ta ajiye sai kuma ta sanya ƙafa ta ture ruwan ya zube gabaɗaya a ƙasa.Kallan kallo aka shiga yi tsakanin Malam da Malama Zainabu dan ita Malamar har wani tsoro ta ji ya ɗarsu a ranta, ita kuwa mahaukaciyar ko a jikinta ta tashi ta nufi randar da ta ga Malama ta kwalfo mata ruwa har ta buɗe sai kuma ta rufe da ƙarfi har murfin ya yi ƙara da yake wani farantin silba ne ƙarami aka rufe randar dashi.

Sai da ta je kan randar ta ƙarshe da yake randunan uku ne ta buɗe ta sanya kofin da aka kai mata ruwan da shi ƙasan sa ma akwai ƙasa haka ta dulmiya ta kwalfo ruwan da ta fito da hannun nata gabaɗaya ya jiƙe dan har hannun ta sanya a randar ta ɗakko ta kafa kai ta sha sai da ya ishe ta, sannan ta dangwarar da kofin a wurin ta juyo ta dawo inda ta tashi ta zauna. Su Malam dai kallonta kawai suke.

"Uhmmm Malam tun da ta warware kuma ta ci abinci dama ina ganin yunwa ce ta sanya ta faɗi, ai sai a nuna mata ƙofa ta tafi ko?" Cewar Malama Zainab tana kallon Malam ɗin da ya yi shiru kamar mai wani nazari.

Shirun dai ya yi bai bata amsa ba har sai da ta ƙara maimaita masa maganar sannan ya huro da iska daga bakinsa, sai kuma ya ce.

"Hakane Zainabu amma ba wai na ƙi ta taki bane sai dai ni ma akwai abin da nake hange wanda nake ganin kamar ke baki hango ba, inaso dan Allah ki bani haɗin kai mu riƙe matar nan a gidan nan" Ya ce yana kallon Malama da ta yi saurin miƙewa tsaye cikin kaɗuwa.

"Me kake faɗa haka Malam? Mahaukaciyar kake cewa ta zauna a gidan nan, haka kawai ba sanin halinta ba muka yi yo da Allah na tuba mahaukaci ma ai ba a saka shi a lissafi ba son ta je ta cutar da mu" Malama Zainab ta ce tana kallon inda mahaukaciyar ke zaune tana ta wani kurta layi da yatsanta a ƙasa sai wani maganganu take da baka gane ko fahimtar me ma take cewa.

"Haba Zainabu ya kamata ki fara saurarata ki ji manufata kafin ki yanke hukunci, kuma insha Allah za mu ajiyeta ne dan mu taimaka mata mun yi hakan da kyakkyawar niyya da yardar Allah babu abin da za ta mana"

"To ina sauraranka Allah kuma ya sa haka"Ta faÉ—a tana komawa ta zauna.

"Amin" Ya ce kafin kuma ya É—ora wata maganar.

"Hakiƙa Allah yana baiwa bayinsa baiwa haka kuma yana jarabtarsu ta duk inda ya ga dama, amma cikin iko da hikimar ubangiji na gano wani sirri tattare da matar nan, Allah ya bayyana tare da nuna mini wani ɓoyayyen al'amari a tattare da ita"

"Me kake so ka ce ne Malam" Malama ta katse shi.

"Inaso in ce miki wannan matar ba wai da haukar nan aka haifeta ba, asalima ba mahaukaciya ba ce daga baya abin nan ya sameta, tabbas akwai wani sihiri a tattare da ita" Malam ya faɗa idanunsa kafe a kan mahaukaciyar da zuwa lokacin kuma kawai ɗaga kai take yi sama tana saukewa ƙasa.

Ƙanƙance idanu Malama Zainabu ta yi ta kalli matar tana son gano abin da Malam ɗin y faɗa amma kuma bata ga komai ba dama ta yi zaton hakan dan tasan bata da baiwar da mijin mata yake da shi"Yanzu Malam kana nufin ka ce min matar nan da asali ba mahaukaciya ba ce, kenan ta taɓa zama da hankalinta?"

"Tabbas haka nake nufi, kuma na ƙudurci taimaka mata insha Allahu za a dace za ta dawo ras kamar bata taɓa yin haukar ba"

"Amin ya Allah, kai duniyar nan abin tsoro ce wallahi wannan wane irin rashin tsoron Allah ne da kuma son duniya za a mayar da mutum mahaukaci kawai yake yawo a gari kai Allah ka karemu sharrin mutum da aljan"Malama Zainabu ta ce tana jijjiga kai.

"Amin, ke dai bari rayuwar yanzu sai a hankali"

"To Allah tayamu riƙo ya bata lfy"

"Amin, yanzu abin da nake so da ke wancan É—akin da ake sanya kayayyaki, za a kirawo almajirai guda biyu ko uku su kwashe su haÉ—a a É—aya É—akin, sai a gyara mata ta zauna a ciki"

"To Malam, amma wani hanzari ba gudu ba kan ganin za ta yadda ta shiga É—akin kwa?"

"Eh za ta shiga yanzu kafin su gama gyarawa akwai wani magani da zan yayyafa mata a jikinta zai taimaka wajen shigarta É—akin"

Da "to" Malama ta amsa masa.

Kafin meye wannan almajiran Malam sun shiga gyara ɗakin, ita kwa mahaukaciyar tana nan kwance a inda take da Malam ya watsa mata maganin anan ta ɓingire tana bacci, har sai da ɗaki ya zama tsaf sannan aka shimfiɗa tabarma da ƙaramar katifa, tana falkawa Malama Zainab ta nuna mata ɗakin cikin ikon Allah kwa babu abin da ta yi kawai shiga ɗakin ta yi ta zauna tare da miƙe ƙafa duk da baccin dama ba wani isarta ba ya yi da alama, ɗakin kawai take bi da kallo.

_Bayan sati biyu_

Jiki ya yi kyau sosai dan har sai da Malam ya mata addu'a ya kafeta a cikin gidan dan gudun fita saboda tana ta yunƙurin a barta ta fita, yanzu ma duk haukar ta yi sauƙi sai dai ta zauna ta yi shiru, ko aiki Malams Zainab take a tsakar gida sai ta fito ta zauna a ƙofar ɗaki take ta bin Malamar da ido duk inda ta yi.

Yanzu jikinta ma fes yake saboda hatta kan ta sai da Malama Zainab ta wanke mata shi ta gyara mata ta tufke mata, saboda ta fahimci bat son kitso da an kama kan sai ta rinƙa jijjiga kai alamar bata so.Kayan Malamar ne yanzu ma a jikinta dan har wanka take mata sosai sauƙi ke samuwa shi kwa Malam kullum ciki haɗa rubutu da maganin ita ce gashi yana jin daɗin yadda Zainabun ke yiwa matar ba kyara ba tsangwama.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YATINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

PAGE2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣

_Ridallah_

Karatu ya kankama sosai ta maida hankali a karatun ta dan yanzu duk class ɗin nasu babu wacce ta fita ƙoƙari Malamai har mamakin irin ƙoƙarinta suke saboda iliminta har nema yake ya zarce ajin da take.Ko yaushe cikin nazari da duba litattafai take babu ruwanta da shirme ko biya ƙawaye ƙawarta gida ɗaya Anisa Bello ƴar garin Dutse ce ita ma yarinya ce mai ƙoƙari da hazaƙa shi yasa ma tasu ta zo ɗaya da Ridallah.

Shugaban makarantar shi ne ya mata siyayyar madara cornflakes da makamantan su, tabbas Principal ya yi musu alkairi da ba za su taɓa mantawa ba saidai Allah ya biyashi. Baba da inna Rahma suka mata sauran siyayyar kayan yaji da mai da sauran abubuwan buƙata yanzu ta zama ƴar makaranta, hankalinta kwance dan kullum sai ta ga su Baba hakan ke sa ta ji kamar ma ba boarding school take ba.
Chapter 14 · 0% Book details