← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 16 OF 29

Sashe 16

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Tun da Abie ya tafi shi kuma Daddyn Amal ya koma wurin aiki dan dama shi baya dawo wa daga office sai magrib in ya fita tun safe, hakan ne ke baiwa Mummy damar cin karenta babu babbaka.Dan haka yanzu ma ta cigaba da nuna musu hanya marar ɓullewa sai yaran suka ɗora daga inda suka tsaya dan dama kowaccen su ta tsufa a harka yaran ƙanana da su amma an ɓata musu rayuwa, sosai suke samo kuɗaɗe wanda Mummy ke haɗasu da manyan mutane suke sheƙe ayarsu, idan suka basu kuɗi sai ta ɗauki kasonta ta basu nasu sauran kuma ta aikowa Aunty su raba da ita da ƙawarta Hajiya Suwaida sosai Auntyn ke siyan kadarori da kuɗaɗen tana jin daɗin irin yadda harkar ke tafiya dan koyaushe idan suka yi waya da Iftihal sai tana jaddada mata akan ta maida hankali wajen janye ra'ayoyin abokan tarayyarta dan dama batun karatu ma ba ta shi suke ba duniya ce kawai a gaban su.Shi kwa Daddy bai san wainar da suke toyawa ba bare kuma Abie da ke can hankalinsa kwance yana ganin ƴarsa tana can tana karatu da yace ko hutu aka yi ba za ta zo ba sai dai su je su gan ta dan baya so ta zo Aunty ta tsiro da wani abun da ban.

Mummy hatta mai lesson ɗin da aka ɗaukarwa Iftihal ta ja masa kunne akan kar ya kuskura ya faɗawa Daddy cewar ba a karatun sai take bashi kuɗi ta toshe bakin, dan Aunty ta ce ko mai koya musu karatun addini ma da ake koyawa a maƙota Daddy yace suna zuwa dan kamar islamiya ce wata mata take koya musu karatu amma haka suka hana yaran zuwa, ni kwa na ce Allah wadaran naka ya lalace.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

Page 29-30

Haka rayuwar Iftihal da Amal ta cigaba da kasancewa cikin ƙazantacciyar rayuwa kullum idanunsu na buɗewa ashe mai makarantar da aka sanya Iftihal ɗin ma inda acan aka sanya Amal ita ma dai da ba zuwa take ba ba a ce makarantar su ba shi ma ɗan hannu ne dan haka suna lasa masa zuma a baki hakan yasa ya rufi bakinsa bai taɓa sanar da Daddy cewa basa zuwa makaranta ba sai dai akwai ranar tonon asiri.

*Bayan shekaru uku.*

Iftihal girma ya ƙaru kai ya ƙara fashewa idanu sun ƙara buɗewa, ta ƙara zama babbar yarinya kuɗi ya zauna, dan yanzu hatta motar da suke yawo a ciki wacce Daddy ya siya musu sun canja ta, amma Daddy kamar ma bai sani ba dan yanzu da Mummy ta sanar da Aunty yana neman ya harbo jirginsu sai suka sanya aka rufe masa baki ruf daga shi har Abie ɗin dan haka ynzu babu wani ɓoye-ɓoye dan babu wani abu da ya isa ya yi, iya shekarun nan da ta yi Abie bai ƙara ziyartar ta ba sai dai Aunty ta zo ita ma dan ta kawo musu kayan mata na gyara dan hatta zuwan ma Abie riƙe masa ƙafa aka yi.Momma ce dai ke ta addu'a domin tana lura da komai da yake faruwa sai dai bata tantance me ke faruwa a Chainan ba, amma dai rashin gaskiya ya bayyana a tare da Aunty da kuma irin maƙudan kuɗaɗen da take fantamawa da su, har mota gareta amma gamin Abie ma bai kawo komai ita ma ta ja nata bakin ta yi shiru dan akwai lokacin da ta ce za ta bi Auntyn China domin su gano Iftihal ɗin amma Auntyn ta mata gori akan cewa ba ƴarta ba ce ta bari idan ta haifi ɗiyarta ta je amma ba Iftihal ba hakan yasa Momma ba ta ƙara cewa za ta bita su kai wa Iftihal ɗin ziyara ba.

Sanye take da wasu fararen kaya riga da wando wandon ya matuƙar kama mata jiki, sai dogon takalmi mai tsini, babu ɗankwali a kan ta sai dai gashin nata ya sha gyara sai sheƙi yake jelar gashin na reto a gadon bayanta.Idan ka kalleta ba zaka taɓa zaton ta haɗa iri da Hausawa ba bare kuma ka yi tunanin tana ɗaya daga cikin musulmai.A dai dai ƙofar da za ta shigar da ita ƙayataccen Restuarant ɗin ta samu wajen da aka tanada dan yin parking ɗin motoci ta faka motarta kiɗa sai tashi yake tamkar dai motar za ta taka rawa saboda yadda ƙaran bugun kiɗan ke ɗawainiya da motar.

A hankali ta buɗe ƙofar motar cikin yanga da aji tana wani yatsina fuska, bayan ta sanya glases ɗinta ta kashe motar ta ɗakko ƙaramar jakarta, ƙafafunta ta sanyo su ƙasa ta fito tana ɗan bin wajen da kallo kafin ta maida ƙofar ta sanya makulli ta kulle motar.Jakarta ta rataya kafin ta fara takun ta cikin izza da jan hankali, taku ɗaya biyu ta yi wayarta ta shiga ruri tana neman agaji har kiran ya katse bata ma fito da wayar daga jakar ba, sai a karo na biyu da kiran ya sake shigowa ta fiddo wayar sunan Alhajin da Autynta ta turo mata no sa ta gani, daga Nigeri'a yake ya zo ganin likita China shi ne suka yi magana da Autynta akan zai je wurin Iftihal ɗin su haɗu, sunan Restuarant ɗin ya tura mata tare da mata kwatance ashe ma ta san wurin shi ne za su haɗu a nan kafin su gama daidaitawa su wuce Hotel.

Bayan ta ɗaga ya faɗa mata ɓangaren da za ta sameshi, wayar kawai ta kashe ba tare da ta bashi amsa ba, ta nufi ƙofar domin shiga wurin domin ba ƙaramin wuri bane.

" Akwai ƙofa daga damanki ki shigo zaki hangoni zaune wurin bishiya"Ta tsinkayi muryar Alhajin da ya ƙara kiranta waya.Wani haushi da takaici ne ya kama ta wato ma ba cin abincin zai yi ba yana can ciki da yake wurin daga can ciki sai aka ware wurin hutawa haka dai da ƴan shuke-shuke a wurin, wato ma ya ɗauketa wata bagidajiya irin bata san wurin ba har wani kwatance yake mata, ƙwafa kawai ta yi a ranta ta kashe wayar ba tare da ta bashi amsa ba, kai tsaye ta turo ƙofar gilashin ta shiga wurin mutane ne gasu nan birjik suna cin abincin wasu kuma yanzu ake kawo musu abincin kowa dai yana sabgar gabansa.

Cikin takunta ta shigo wurin direct wurin wani farar fata ta nufa ta miƙa masa kuɗi ya ɗauki wata takarda ya yi signing a jiki ya miƙa mata tana karɓa ta juya ta buɗe ƙofar nan ta shige.

Zaune suke akan kukeru a can ƙasan wata bishiya hira suke taɓawa jefi-jefi dan kwata-kwata Hizbullah ba ya son yawan magana, Abulkairi ne ke masa hiran shi kuma iyakarsa "Eh, a'a, hakane"

"Wai Hizbullah kai wane irin mutum ne dan Allah, ya kamata kake sakewa da ni ko da ba za kake sakewa da wani ba, saboda ni abokin ka ne amma kullum da ka saurareni mu yi magana ka gwammace ka rinƙa tunani?"

"Ba haka bane, dama can ni ban fiye son yin magana sai in dai da Ridallah ne, ya kamata ace ka fahimci bani da yawan magana a iya zaman da mu ka yi na shekaru"

"Hakane ni ma na fahimci hakan amma dai a ƙalla kake magana akan shiru dan shiru na haifar da illah ga lafiyar ɗan adam"

"To zan ƙoƙarta in ke yin hakan amma abin da ya ƙara sanyani na ƙara zama shiru-shiru tin hutun da na je gida na ƙara tabbatar da cewa Ridallah ta ɓata babu labarinsu tun daga nan na ƙara jin bana jin daɗin komai wallahi"

"Maganarka hakane ka ga ko lokacin da ka je Kano ka kai min ziyara lokacin da mu ka je hutun na ga ka rame akan zuwanmu, kuma ni ma da na je HaÉ—ejia na kai maka ziyarar na ji Umma na cewa nake maka faÉ—a ka canja hali daha shiru-shirun nan kake sakewa a jama'a"

"Ai ita Umma ko yaushe laifina take gani, tana tunanin kamar da gangan nake sanya kaina a damuwa bata san ba abin daga zuciyata ya...

Shirun da Abulkairi ya ji yasa ya ɗago kai yana kallon Hizbullah domin ya ga abin da ya katse masa maganar ya kasa ƙarasawa, ai kuwa yana ɗagowa ya yi tozali da Hizbullah ya miƙe tsaye daga zaunen da yake ya maida hankali ga kallon wani waje bakinsa a buɗe.Hizbullah kwa hangota da ya yi shi ne abin da ya dakatar da shi daga maganar da yake ya miƙe tsaye yana hangota tana nufowa inda suke, fosta ya yi dan hatta numfashinsa ji ya yi yana barazanar barin gangar jikinsa saboda ɗimaucewa da kuma wani mugun bugawa da zuciyarsa ke yi da ƙarfi kamar ya yi tseran gudu na kilo miter masu yawa.Idanunsa kwa ko ƙiftasu ba ya yi har ruwa taruwa ya yi a cikinsu dan ba ya so ya ƙiftasu ya nemeta ya rasa duk da yana ganin kamar a mafarki yake ganinta.
Abulkairi dai ya tsaya shi ma cikin mamakin abokin nasa sai ya kalli Hizbullah sai ya juya ya kalli wacce ya ga Hizbullah É—in na kallo cikin tsantsar ruÉ—ewa, abin da ke baiwa Abulkairi mamaki wacce Hizbu ke kallo mace ce kuma Hizbu maza ma bai damu da kallonsu ba bare wasu mata ma da ya tsani zancen mace in ba zancen Ridallah ba ko na Ummarsa ba dan ko Abulkairi na yiwa Hizbu zancen tasa budurwar Bilkisu sai ya ce shi fa ba ya son surutu amma yau shi ne ke kallon mace ba Ridallah ba macen ma wannan mai kama da arnan dan gabaÉ—aya jikinta babu alamar da za ta nuna akwai muslunci a tare da ita.
Chapter 16 · 0% Book details