← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 19 OF 29

Sashe 19

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Haka sai suka shiga jajanta abin daga ƙarshe kowa ya koma ɗaki amma b wai dna bacci ba Baba Habiba da Ridallah alwala ma suka yi suka gabatar da sallar nafila suna addu'a tare da godiya ga Allah bisa nasara
da ya basu a kan azzalumai

MMN AFRAH😍

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

page 3️⃣4️⃣&3️⃣5️⃣

ABUJA

Zaune Aunty take a falonta ta ɗora ƙada ɗaya kan ɗaya tana danne waya, da hannu ɗaya ɗayan hannun kuma riƙe da ayaba tana gutsira a hankali Safiya ce ta shigo falon ɗauke da sallama sai da ta zo har gaban Auntyn ta durƙusa har ƙasa ta ce

"Hajiya gashi " Cewar Safiya tana miƙa mata leda mai ɗauke da atamfofi, ta ajiye a gabanta sannan ta ɗora mata mukullin motar motar a kan center table ɗin da ke gabanta.

"Kin kulle min motar?" Auntyn ta tambayeta hankalinta a kan waya.

"Eh na kulle, da na ga na kasa kullewa ma direba nasa ya kulle miki"

"Gaskiya ƙauyencinki ya yi yawa Safiya kullum ke bakya gane abu sau nawa na loya miki buɗe mota da rufewa saboda irin haka idan na yi mantuwa ki ɗakko min, amma ba laifinki bane babu a house shi sa" Ta faɗa tana juyowa ta kalli Safiyar irin kallon raini.Shiru Safiyar ta yi duk da maganar ta mata ciwo amma babu yadda za ta yi tun da aiki take a ƙarƙashinta kuma ma ai gaskiga ta faɗa tun da ba su da ko keke a gidansu bare a yi zancen mota.Amma ita ma Autyn ai ƴar talakawan ce kawai dai samun wuri ne ya sa ta manta da baya.

"Ɗauki ki kai min ɗakina sai ki gyara min gadon dan ɗazu na kwanta aka duk shimdiɗar ta ɓaci" Muryar Aunty ta katse mata tunani

"To Hajiya an gama" Safiya ta faÉ—a tana É—aukan ledar atamfofin da ta É—allowa Aunty a mota ta hau sama da su.

Tana shiga ɗakin ta jefar da ledar kayan a ƙasa ta shiga ƙarewa ɗakin kallo tana ƙada jin wani haushin Auntyn na tokare mata maƙoshi.

"Matar nan baki da hankali amma da sannu nasan za ki gane shayi ruwane, kin bar ƴar cikin ki tana karuwanci saboda tsabar jahilci da son duniya tana aiko miki kuɗi kina bishasharki kin ɓanta cewa amana Allah ya baiwa iyaye ta ƴaƴansu kuma sai ya tambayesu kamar yadda ya faɗa amma ke baki tanadi amsar baiwa ubangiji ba kina hauka sai ranar da aka maƙuraki a kabari mala'iku su shiga jibgarki" Safiya ta faɗa iyo jifa da filillikan kan gadon ta shiga ɗame zanin gadon, dan ita Aunty gani take ba a san me take ba duk da ta fi ƙarfin mijin mata amma kuma bata san gabaɗaya takunta a kan idon Safiya yake ba tana sane da ita ko wayar da take da Iftihal ko Hajiya Wasila tana mata laɓe ko kuma idan Hajiya Suwaida ta kawo mata ziyara duk maganar da za su yi a kan kunnen Safiyar suke ba tarw da sanin suna yin shuka a idon makwarwa ba.

Aunty na ganin Safiya ta haye sama ta kamo number Hajiya Suwaida ta doka mata kira, sai da ta kusa tsinkewa Hajiya Suwaida ta É—auki kiran.

"Hello ƙawata"Cewar Hajiya Suwaida cikin wata murya.

"Na'am aminiyata fatan kina lafiya"

"Lafiya ƙalaw wallah i fatan kema kina lafiya"

"Lafiya ƙalaw, sai na jiki shiru kuma ban ji alert ba" Hajiya Suwaida ta faɗa tana dariya.

"Haba ƙawata ke kwa akwai gajen haƙuri, ai kin san da kuɗin sun shigo da tuni na hankaɗo miki naki kason dan babu sanya kawai dai ni ma ina jiran tsammani ne"

"Bangane jiran tsammani ba, kina nufin ita Iftihal ɗin basu haɗu da Alhajin ba? Ko dai ita ma ta fara sanin kan ta ne ta riƙe kuɗin ba ta baiwa Hajiya Wasila ba bare a turo mana namu?"

"Ba haka bane kinsan dai Iftihal sai abin da na ce take yi kuma ba za ta taɓa riƙe kuɗi ba ko da za ta samu kaɗaɗe malala gashin tinkiya in miki ta yara" Ta faɗa tana dariya.

"To a ina matsalar take?"

"Sai fa yau za su haÉ—u da Alhajin dan mun yi waya ma É—azu ta ce min tana hanyad zuwa inda za su haÉ—u da shi, kinsan kwa komai na kankama za a sanar da ni"

"Yawwa yanzu na ji batu, amma da na ji shiru "

" A haba ƙawata ai kin fi ƙarfin komai a wurina"

A tare suka kyalkyale da dariya, suka faɗa wata hirar daga ƙarshe suka yi sallama a kan idan kuɗin sun sauka da zafinsu za ta tura mata kasonta.Tana ajiye wayar ta shiga magana ita kaɗai tana murmushi.

"Ke ma dai ƙawata da wasa kike amma ke da kika ɗorani a hanya ya za a yi na manta da ke ko na yada ki ai in na yi haka na yi butulci ba na fatan faruwar hakan ma."Ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta

*MOMMA*

"Assalamu alaikum" Suhaila take sallama daga bakin ƙofar ɗakin Momma, amsa sallamar Momma ta yi sannan ta mata izinin shigowa, shigowa ta yi ta ce.

"Hajiya na kammala aikin"

Kauda kai gefe Momma ta yi dan ba ta so Suhaila ta ga idanunta saboda ta sha kuka duk sun yi ja sannan saman fatar idanun ma duk ya kumbura.

"Yawwa dama É—akin can nake so ki tayani mu gyara kamar yadda muka saba"

"To Hajiya ai sai abin da kika ce, sai dai kuma ina da shawara"

"Ina sauraronki Suhaila ki faÉ—a kan ki tsaye dan kin san ba Æ´ar aiki na É—auke ki ba na É—auke ki tamkar Æ´ar da na haifa"

"To Hajiya dama gani na yi ɗakin can ba fa datti yake yi saboda gabaɗaya window da labulayen ɗakin a rufe suke, sannan kuma babu wani wanda yake shiga ciki amma ace duk ƙarshen wata sai mun gyara ɗakin mun juya jeran ɗakin sannan kayayyakin da babu wanda ya taɓa sanyasu kuma yadda muka ajiye haka suke amma sai mun hargitsasu mun sake jerawa?"

Shiru Momma ta yi, wannan karon ta maido kallon ga Suhaila tana nazarin kalamanta kalaman da suka ƙara sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi, wanda hakan ya ƙara sanadiyyar cikowar ƙwalla daga idanunta, hannu ɗaya ta sanya ta rufe fuskarta ta ɗan jima a haka sannan ta murza fuskarta dahannun ta zubawa Suhaila idanu ta ce

"Suhaila shin iya shekarun da muka ɗauka da ke muna aikin nan baki taɓa min wannan tambayar ba sai yau? Sannan kuma baki taɓa tunanin dalilin da ya sanya muke aikin ba sai yau?"

"Ba haka bane Hajiya kawai dai yau ne na ce bari na gwada sa'a ta ko za a dace, domin na san tun daga ranar da kika fara buƙatar na tayaki gyara ɗakin nake yiwa kaina tambayoyi duk da acan baya ke kaɗai ke yin kayanki kafin daga bisani ki sanya nake tayaki muna gyarawa.Ba komai ke bani mamaki na har ya ɗaure min kai irin yadda kike siyan kaya kina jibgewa ba tare da ana amfani da su ba, iya gani na tun daga ranar da aka haifi yaro kawo ya zama saurayi akwai kayan da zai sanya a cikin ɗakin, kayan jarirai, kayan wanda ke rarrafe, kayan mai koyan tafiya kayan yayayyen yaro kawo shekara uku huɗu kai har kawo kayan matashi akwai a ɗakin a tawa fahimtar kayan ne kike siya tun daga jarai har girman yaro akwai kayan da zai sanya a ɗakin jibgi-jibgi, sai dai inaso ki yi haƙuri da tambayar da zan miki, na san dai baki da ɗa, iya sani na dai kin taɓa haihuwa ɗan ya rasu, to shin yaron ne kike siyawa kayan nan kike ajiyewa, ko kuma dai taro ne kike yi abin da bahaushe kan kira kafi ɗa wuya?" Suhaila ta kai ƙarshen maganar tana ɗagowa ta kalli Momma ganin gabaɗaya hawaye ya wankewa Momma fuska jikin Suhaila ne ya yi sanyi har tana ji a ranta bata kyauta ba domin ta shiga hurumin da ba nata ba gashi har ta sanya uwar ɗakin nata kuka wannan dalilin ne yasa tun daɗewa shekara da shekaru ta riƙe tambayar nan bata yiwa Momma ba.

"Suhaila na ji duk tambayoyinki sai dai inaso ki sani duk duniya babu wanda ya san da abubuwan da ke cikin wancan É—akim daga ni sai ke sai kuwa Allahn da ya haliccemu, ko Abie bai san da komai na cikin É—akin ba, ke ma dan na yarda da ke shi yasa na sanar da ke, tabbas bani da É—a kamar yadda kika sani kuma haihuwata É—aya kuma kamar yadda kowa ya sani yaron baya raye, sai dai ni dalilin da ya sa nake ajiye kayan nan Allah ne kaÉ—ai ya sani, kuma ba zan sanar da ke ba kuma ba dan ban yarda da ke ba sai dai na barwa kai na sanin sirrin zuciyata, sai dai zai iya kasancewa taro nake ta bahaushen wato kafi É—a wuya" Momma ta faÉ—a wasu hawaye masu zafi na kwaranyo mata, a lokaci guda kuma tana sakin murmushi mai ciwo.

Wata ajiyar zuciya Suhaila ta sauke tana jin dana sani a kan tambayar da ta yiwa uwar É—akin nata, dan ta ga ta shiga damuwa sosai wajen bata amsa.

"Dan Allah Hajiya ki yi haƙuri da tambayar da na miki, insha Allah ba zan ƙara miki makamanciyar tambayar ba"

"Ba komai Suhaila taso mu je mu fara kar lokaci ya ƙure mana" Cewar Momma tana miƙewa Suhala ta mara mata baya.

Suna zuwa Momma ta sanya mukulli ta buɗe ɗakin ta tura ƙofar suka shiga, wani sanyi ne ya ziyarcesu irin na ɗakin da ya yake a rufe kowane lokaci, ga kuma wani ƙamshi na freshner.
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH
Chapter 19 · 0% Book details