← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 11 OF 29

Sashe 11

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta.

"Ba magana ake miki ba?" Baba Habiba ta faÉ—a tana kallonta.

"Dama fa..."Sai kuma ta yi shiru.

"Dama me?" Ya ce cikin lallashi.

"Dama da na ga uara suna tafiya aji shi ne ni ma na ji inason karatu" Ta kai ƙarshen maganar tana goge hawayen idanunta.

"Kai! Allah sarki Ridallah dama akan karatu ne kika shiga damuwa, ni ma da na yi tunanin cewa Babar taki a sanyaki a makarantar nan maimakon kike zaune, to kuma sai nake tunanin ko bata da ra'ayi, amma yanzu tun da har kina so babu abin fa zai hanaki shiga aji in har ta amince" Ya ce yana goya hannayensa a bayansa.

"Na amince shugaba, ai ni dama daga ni har ita ba mu da burin da ya wuce haka, saboda Ridallah yarinya ce mai matuƙar son karatu, gata da hazaƙa tun da take ko ta biyu bata taɓa ɗauka ba a makaranta kullum ita ce ke ɗauka na farko a ajin su"

"Allah sarki! To insha Allah za a sanyata a J.s 1 ɗin idan an mata interview mun gani, Allah jiƙan mahaifin nata" Principal ɗin ya ce yana mai jin tausayinsu, dan Rahma ce masa ta yi mijinta ne ya rasu ƴan asalin Malam madori ne sanadin mutuwar tasa ce suka dawo Gumel ɗin da zama dan Baba ta hana ace daga Haɗejia suka taho dan bata so kowa ya san daga inda suke saboda wani dalili nata daban wanda ita ce kaɗai ta san hakan.

"To mun gode ƙwarai Allah sa ka fi haka, Allah ɗauka ka, ka ya albarkaci zuri'a" Baba ta faɗa cikin farinciki.

"Amin ya Allah nagode ni ma da addu'a, kuma babu komai ai yiwa kai ne, ni zan mata komai kama daga litattafai da komai da komai"

"Nagode Baba shugaba Allah saka maka da alkairi, ya sanyaka a aljanna" Ridallah da ta tsugunna har ƙasa ta haɗe hannayenta a wuri ɗaya ta ce cikin murna da farinciki.

"Ba komai Æ´a ta taso mu je" Ya ce yana kama hannunta suka tafi can office É—insa.

Baba Habiba kwa tsabar farinciki ma ta rasa bakin magana, haka ta tsaya tana kallonsu har suka ɓacewa ganinta sannan ta ɗauki buhunta ta kama hanyar kicin. Dan so take ta je ta baiwa Rahma labarin wannan abin arziƙi da aka musu.

Sosai Mama Rahma ta ji daÉ—i da wannan albishir

Principal ɗin office ɗinsa ya wuce da ita ya yi mata register da komai da komai, sannan ya ɗakko mata uniform set biyu daga cikin uniforms ɗin da gobnati take bayarwa a rabawa ɗalibai.Ridallah sosai daɗi take ji a ranta baki yaƙi rufuwa sai kallon uniform ɗin take yi tana murmushi sai faman godiya take yiwa shugaba shi kwa sai cewa yake ta daina godiya, wani Malami ya kirawo yasa ya mata interview sosai suka yi mamaki daga Malamin har principal ɗin saboda yadda take bada amsoshi a nutse ko gaga ba ta yi sun gamsu da amsoshinta sosai dan haka principal ɗin ya ce ta je ta sanya kayan makarantar ta dawo, haka ta je ɗakin su Baba da ke can inda ɗakunan ma'aikatan kicin yake, duk da su, su Babar basa kwana a makarantar amma dai akwai ɗakin da suke hutawa, haka ta je ta sanya kayan tana ta murna ta linke wanda ta cire ɗin ta nufi kicin ɗin.

Da murna ta je ta rungume Baba ita ma Babar rungumeta ta yi cike da farinciki dan ji take kamar yau take sallah tana son farincikin Ridallah haka kuma ta tsani baƙinciki ko ɓacin ranta.Kowa a wurin sai dariya yake musu ganin suna murna gwanin sha'awa.Haka ta ce musu ta tafi aji, office ɗin shugaban ta je ya kalleta yana murmushi ya ce

"Ridallah an zama Æ´an makarantar kwana"

Cike da kunya ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana murmushi dan duk daɗi ya cikata ta ƙosa ta ganta zaune cikin aji tana ɗaukan darasi.

"To ga wannan" Ya ce yana miƙo mata wata jaka mai ɗauke da dukkan littattafan da ake amfani da su a ajin da za ta je sai biruka guda biyu da mathset da komai da za ta buƙata har test buke duk a ciki.

Idanu ta É—an zaro dan ita tsabar ruÉ—ewa da kuma murna ta ma manta da wasu abu littattafai.

"Gaskia shugaba ko dai ni za a baiwa nima in shiga ajin"Malamin nan ya ce cikin zolaya yana murmushi.

"Nawa ne waɗannan" Ta ce tana miƙa hannu cike da ladabi ta karɓa, tare da buɗawa ta leƙa ganin abin da ke ciki sai farincikinta ya ƙaru akan wanda take ciki da.

"Allah saka maka da alkairi, ya faranta maka kamar yadda ka faranta mini" Ta ce tana kallon Principal É—in cike da girmamawa.

"Amin ya rabbi, shugaba da da Malamin suka hala baki wajen faÉ—a.

"Mu je na raka ki ajin " Malamin ya ce yana yin gaba ta juya ta bi bayansa.

"Allah bada sa'a" Ta tsinkayo muryar Principal ɗin lokacin da ta kai bakin ƙofar fita.

"Amin" Ta ce tana sanya kai ta fita daga cikin office É—in.

Principal ɗin komawa ya yi ya jingina da jikin kujerarsa yana jin wani irin daɗi da nishaɗi a ransa dan a rayuwarsa yana son ya ga ya taimaki mutane, musamman yara, yaran ma marayu yana son sanya farinciki a zuciyar maraya, kasancewarsa maraya ya san zafi da raɗaɗin maraici hakan yasa yake ta ƙoƙari domin ganin ya cire su daga wani ƙunci ko baƙinciki ya sanya su a farinciki.

_Hizbullah_

Zaune yake a ɗakinsa yana riƙe da handout yana karatu, sai kofin shayi ɗan ƙarami da ke kan ɗan ƙaramin faranti, jifa-jifa yana ɗauka yana kurɓa ya maya ya ajiye, yana cikin karatun sai ya ji Ridallah ta faɗo ɓasa a rai da sauri ya ajiye handout ɗin kamar wanda aka tsikara ya dafe kansa da hannu biyu saboda jin da ya yi ya sara masa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Ya ce yana wani runtse idanunsa da ƙarfi jin yadda zuciyarsa ke buga masa da mugun ƙarfi tamkar wacce ke neman agajin gaggawa, kan nasa ya saka ya sanya hannun nasa a ƙirjinsa saitin zuciyarsa ya dafe tabbas Ridallah ita ce bugun zuciyarsa amma yanzu bai ma san inda take ba bare ya san halin da take ciki ba. Da sauri ya miƙe kamar wanda aka tsikara ya nufi inda ya sanya wayarsa caji ya ɗakko ta maimakon ya dawo ya zauna a kan kujerar sai ya tsaya a jikin bango tare da jingina bayansa da bangon, a hanzarce ya shiga contact ya nemo lambar wayar Ummarsa ya shiga buguwa amma har ta tsinke ba'a ɗauka ba, bai yi wata-wata ba ya sake danna wani kiran a karo na biyu burinsa kawai Umma ta ɗauki wayar cikin sa'a kwa sai aka ɗaga wayar.

"Assalamu alaikum" Umma ta yi sallama daga can ɓangaren.

"Wa alaikumus salam" Ya amsa

"Hizbu na kai ne akan layi"

"Ni ne Umma, ina yini "

"Lafiya ƙalaw, ɗan albarka ya karatu"

"Alhamdulillahi! Umma ina lafiya ƙalaw"

"Masha Allah, ina Abulkairi"

"Yana lafiya"

Nan dai suka suka shiga hira ya tambayi Babansa ta ce ya fita, so yake ya tambayeta labarin su Ridallah amma kuma ba ya so ya ji labarin da ya saba ji kullum dan ya san da ace an samu labarinsu to da tun kafin ya kira da sun kira shi aun shaida masa hakan dan ya san sun san halin da yake ciki na buƙatar jin labarin.

"Hizbu na baka ji na" Muryar Umma ta katse masa tunani.

"Umma ina jinki, dama...dama..."

"Dama me? Ka faÉ—i abin da kake son faÉ—a mana"

"Dama ina so in ce miki ya labarin su Ridallah" Ya ce yana maida kan sa ya jingina a jikin bangon tare da ɗaga kan sa sama ya sauke akan ɗaya daga cikin ƙwan fitilun mai kyau da walwali da aka masa wata walkiya da wani abun walkiya mai ƙyalƙyalin ruwan gwal, tare da sanya haƙori ya danne gefen leɓensa na ƙasa yana jiran jin amsar Ummar.

"Haba Hizbu kullum a rinƙa magana ɗaya? Kasan dai da ace an samu labarinsu sai mun fara kiranka mun sanar maka kafin ka kira ka tambaya amma ace kullum sai ka kira ka tambaya wataran ma sai ka kira ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, ka kwantar da hankalinka ka dage da karatunka insha Allahu Allah zai bayyana su muna nan muna addu'a kai ma ka cigaba da yi"

"To Umma nagode sai an jima a gaishe da Baba" Ya faÉ—i hakan cikin raunin da zuciyarsa ta masa.

"To Hizbullah ka gaishe da Abulkairi"

Da to kawai ya iya amsa mata ya kashe wayar ya tako yana jan ƙafafunsa dakyar ya ƙaraso ya zube akan kujerar ya saki wayar ta faɗa kan handout ɗin da yake karatu.Idanunsa a rufe yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarsa tamkar ya sanya magani paracetamol a ciki haka yake ji, a hankali ya buɗe idanunsa zuwa lokacin sun yi jawur kamar wanda ya kwana yana kuka, cikin sanyin jiki ya tashi ya tafi ya buɗe wardrobe ɗinsa, ya ɗakko wani ɗan ƙaramin kit ya koma ya kwanta akan gadon tare da ɗora kansa bisa filo, ɗan kit ɗin ya buɗe ya saya hannu ya fiddo wata flower da ɗankunne wari ɗaya ya riƙe su akan tafukan hannayen sa tare da zuba musu jajayen idanunsa a hankali maganarta ta shiga dawo masa a ranar da ta bashi waɗannan abubuwan.

" Ya Hizbu wannan flower a jikin flower Baba na ciro a ɗakinta, saboda jiya ina ganin film ɗin kwana casa'in sai na ga Yawale da durƙusa ya baiwa Rayya flower, shi ne nima na ciro na kawo maka" Haka ta durƙusa kamar yadda Yawalen ya yi ta baiwa Hizbullah flower, cikin murna ya karɓa sannan ta miƙe suke dariya su duka, tun daga wannan ranar yake ajiye da flower dan wataran ma idan ta shiga gidan su Hizbullah ɗin sai ta ce "Ya Hizbu ina flower da na baka" Har sai ya ɗakko ya nuna mata sai kuma ta ce
"Dan Allah ka jaiyeta kar ka jefar"

"Babu abin da zai sa na jefar da ita" Ita ce amsar da yake bata.
Chapter 11 · 0% Book details