← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 10 OF 29

Sashe 10

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Alhaji sagiru ɗan asalin garin Dutse ne, kuma ɗa ne ga mai martaba sarkin Dutse, shi kaɗai iyayensa suka haifa sai ƙanwarsa da aka haifa a ranar ta mutu, yana da matar aure Hajiya Suwaida ita ma ƴar cikin garin Dutse ce sai dai Allah bai basu haihuwa ba.

Gidan Alhaji Sunusi

Hajiya Sakina ce zaune a falonta ta sanya kayan marmari a gaba sai tuffa a hannunta wanda ko gutsira bata yi ba, ta yi nisa cikin tunani sai tv da ke ta faman aiki.Hawaye ne ke kwaranya a idanunta amma saboda nisan da ta yi a tunanin ko share hawayen bata yi .

Hafeez ne ya shigo cikin falon sanye yake da t.shirt da wandon jeans baƙi sai ƙamshi yake abinsa.Da sallama ya shigo falon mahaifiyar tasa, amma kuma sai jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ya tsinci mahaifiyar tasa a ciki, cikin sanyin jiki ya ƙaraso cikin falon har ya zo gabanta ya durƙusa amma bata ma san da zuwansa wurin ba.Da ido ya bi plate ɗin kayan marmarin da ke ajiye wanda tun lokacin da zai fita daga falon ya hangi Na'ima mai aikinsu ta fito daga kicin da ta yayyanka mata za ta kawo mata amma abin mamakin gashi har ya je ya yi wanka ya shirya duk ɓata lokacin da ya yi amma har yanzu babu wani abu da ta ci daga cikin kayan marmarin sai tunani da ta tsunduma, a ciki shi yasa kwata-kwata ba ya so ta kaɗaice ita kaɗai saboda yawan tunanin nan gudun kar ma ya yuwa lafiyarta illa.Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya hannu ya ɗan taɓa ta tare da cewa

"Ammi!"

Jin taɓa ta da aka yi da kuma sunanta da aka ambata shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta kai ziyara.

Dubanta ta kai ga Hafeez ɗin, sai kuma ta yi saurin kawar da kan ta gefe jin lemar hawayen da ke kan kumatun ta, da sauri ta ajiye tuffar a kan plate ɗin sai kuma ta sanya hannayen nata ta goge hawayen tare da ɗan jan hanci kaɗan sannan ta ƙaƙalo murmushi tare da cewa

"Hafeez wai kana nufin har ka yi wankan ka shirya, ko dai jiƙa-jiƙa ka yi baka fita ba shi yasa ka yi saurin fitowa" Ta ce cikin zolaya dan kar ya mata zancen halin da ya tsince ta a ciki, saboda ko da zai tafi wankan sai da ya sha lallaɓata akan dan Allah kar ta yi wannan tunanin, har da kunna mata tashar arewa 24 suna shirin mata a yau dan su ɗauke mata kewa amma shi ne ya dawo ya same ta dumu-dumu tana aikin nata da ta saba wato tunani.

" Haba Ammi yanzu duk maganar da muka yi a gefe kika ajiyeta, kinsan ko kaÉ—an bana son ganinki cikin damuwa, domin damuwa tana sanya ciwo, shi yasa in dai ba makaranta zan je ba ko wani uzuri mai muhimmanci ba na son na yi nesa da ke dan kar ki ke yawan tunanin nan"Hafeez ya ce lokacin da yake zaunawa daga tsugunnon da ya yi.

"Hafeez kenan sau nawa kake so na faɗa maka cewa nima ba a son raina nake tunanin nan ba, kuma ma bana sanin lokacin da nake yin tunanin sai dai na tsinci kaina a ciki, dan Allah kake min uzuri mana wannan tunanin ya zame min jiki koma in ce ya zame mini abokin rayuwa!" Cewar Ammi tana sanya hannu ta share ƙwallar da ta kwaranyo mata yanzu.

"Ki yi haƙuri Ammi, nasan da haka tun da abin nan ba ke kaɗai ke yi ba nima ina yi haka Abba ma sai dai naki ne ya fi yin tsauri, Allah ne kaɗai ya san dalilin wannan yawan tunaninnda yake nema ya zame mana kamar gado kuma abin al'ajabin ma babu wanda cikin mu zai ce ga wani abu da yake tunawa a lokacin da yake tunanin, sai dai idan wani tunain ne da ban za ka yi kuma ka tuna abin da kake son tunawa har ma ka yanke hukunci ko sharar idan akan hakan ka yi tunanin..Amma shi wannan dogon tunanin fa da ya zama kamar ibada sji baka taɓa gane inda ka dosa bare ka san inda ka je sai dai ka gama bulayinka, ya tafi ya barka da damuwa a ranka.Tunani ne da ya sha ban -ban da wanda kowane tunanin da mutum zai gane irinsa sai dai mu cigaba da addu'a akan Allah kawo mana mafita"

"Amin ya rabbi" Ammi ta ce tana bin ɗan nata da kallon so da ƙauna tabbas kowacce uwa idan ta samu ɗa mai biyayya irin Hafeez to tabbas ta yi dace.

Ganin kallon da take masa ya sakar mata murmushi tare da miƴa hannu ya ɗakko tuffa ɗin da ta ajiye ya miƙa mata, karɓa ta yi cikin jin daɗi itama tana sakin murmushin ta kai bakinta ta gutsura, haka suka cigaba da hirarsu har aka kira sallar magriba, sannan Hafeez ɗin ya tafi masallaci itama ta shiga domin yin alwala ta gabatar da sallar tana so ta damawa Abban Hafeez kunun gyaɗar da ya ce ta dama masa zai sha idan ya dawo domin ya je gidan abokinsa kuma ta san a gida zai ci abincin dare domin baya iya cin abinci a ko'ina sai a gidansa.

Maman Afrah🥰😍😘

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

PAGE 2️⃣&1️⃣2️⃣2️⃣

_Ridallah_

Tun komawarsu garin Gumel rayuwarsu ta sauya, Mama Rahma kamar yadda Ridallah take kiranta, ita ta sanar wa shugaban Boarding pri & Junior scul da take aikin abinci, akan ya mata alfarma za ta kawo wacce za ta maye gurbinta, cikin ikon Allah kuea sai ya ce dama akwai wacce ta rasu ba' a maye gurbinta ba dan haka ta bashi lokaci zai yi ƙoƙari ya bada sunan Baba Habiba idan Allah ya sa tana da rabo ta za ta samu haka suka masa godiya da ƙoƙarin da ya musu suka dawo gida cikin farinciki.

Bayan mako biyu kwa aka nemi Baba Habiba akan ta fara zuwa wurin aikin, duk da wasu masu aikin acan makarantar suke kwana amma Mama Rahma da yake tana da kula da aikinta tana zuwa akan lokaci ga kuma cika ƙa'idoji hakan yasa idan ta gama aikinta take tafiya gida ta kwana.Ita ma Baba Habiba ta nemi wannan alfarma kima da darajarsu da shugaban makarantar ke gani ya basu dama suke zuwa suna tafiya tun da a cikin gari suke, wannan ya sa su ma suka bada himma da kuma ganin basu yi duk wani abu da zai ruguje duk wata yarda da kuma dama da aka basu ba.

Kullum idan su Baba Habiba suna kicin suna aiki sai Ridallah ta samu wuri ta zauna ta rinƙa kallon ɗalibai idan suna tafiya ajijuwa, gwanin sha'awa kowa sanye da uniform da socks da sandal sai abin ya rinƙa birgeta tana jin inama ita ce, dan tana da son karatu amma gashi sun baro garinsu, hakan ya sa Ya Hizbunta ya faɗo mata yadda suke tafiya makaranta ya kama hannunta ya yi ta siya mata duk abin da take so.Amma yanzu gashi wasu sun shiga tsakaninsu da shi, sun sanya sun baro garinsu sun dawo wani garin da bata ma jin daɗin garin saboda babu Ya Hizbu a cikin garin.

"Kasan me Ya Hizbu?"

"A'a sai kin faÉ—a "

"Inaso in yi karatu mai zurfi idan na gama in samu aiki"

"Allah sarki Ridallah, insha Allahu sai kin yi karatu har ya isheki, ni nan zan tsaya tsayin daka har sai kin cimma burinki, sannan in Allah ya yarda za ki samu aiki"

"Nagode Yaya na" Ta ce tana murmushi, shi ma murmushin ya mata.

Maganar da suka yi ana gobe za su baro Hadejia ta faÉ—o mata, hawaye ne suka zubo mata ta sanya hannu ta share tana jin kewar Ya Hizbunta har cikin ranta, ashe burinta ba zai cika ba.

"Ridallah! Baba Habiba ta kirata da ta fito domin shanya gawayi.Da sauri ta ɗago kan nata ta kalki mahaifiyarta ta da ke kallonta cike da mamaki, duk da dama tun da suka dawo Gumel tana kamata tana kuka idan ta tambayeta sai ta ce Ya Hizbu ta tuno.To itama Babar tana mata uzuri tun da ta san irin shaƙuwar da suka yi, yo kuma abu ne mai wahala ace ta yakice tunaninsa lokaci guda duk da ta san dai ba lallai ne ta manta da shi ba har abada amma dai ta san mawuyaci ne ace sun ƙara haɗuwa ma, sai dai bata taɓa ganin tana yin kuka a wajen da jama'a ke kai kawo ba, ko a gidan takan kamata ne a ɗaki ta ɓoye kan ta tana kuka.

Ajiye ƙaramin buhun hannunta ta yi wanda ra zubo gawayin a ciki, ta ƙarasa wurin da Ridallah ke zaune ta zauna akan dakalin ita ma, hannun Ridallah ɗin ta kama da hannayenta biyu ta ce

"Haba Ridallah, har sai yaushe ne zaki daina yin wannan kukan kina zubar da hawayenki? Bayan kinsan cewa Hizbullah mun baro shi a Haɗejia sannan bai san ma inda muka taho ba, bare ya biyoki amma sai ki zauna ki yi ta zubar da hawaye, abun har ya kai kina kuka a inda mutane suke ficewa kuma za su iya ganinki? Dan Allah ki sanyawa ranki haƙuri da dangana duk da nasan da wuya hakan amma daurewa za ki yi ko nima na daina tunanin halin da kike ciki idan da rabon ganawa wata rana sai ki ga kun gana ke da shi" Baba Habiba ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya tana kallon Ridallah da hawayen suka cigaba da sirarowa daga idanunta.

"Hakane Baba, amma ni yanzu ba wannan ya sanya ni kuka ba"

"Menene?"

"Kawai saboda na ga...

"Baba Habiba waye ya taɓa ƴar lelen naki na ga kina ta faman lallashi?" Maganar principal ɗin makarantar ta katse Ridallah daga abin da take so ta faɗa.

"Wallahi shugaba ka ganni da ita nima ban kai ga jin wanda ya taɓo ta ba"Baba ta ce cikin jin nauyin shugaban makarantar saboda mutum ne shi mai kirki da girmama mutane.

Wurin ya ƙaraso yana murmushi tare da cewa

"Ƴar lelan Baba wa ya taɓa ki?"
Chapter 10 · 0% Book details