← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Iftihal kwa da ta lura da bin da su Alhajin ke mata dan dama tana ganinsa ta mudubi lokacin da ya tsare taxi ɗin, a haka ta yi ta yaudararsu har ta yanke ta wata hanya inda ta ɓacewa ganinsu.Gida ta nufa tana jin zuciyarta ba daɗi, tana yin parking ta nufi ɗakinsu ta shiga ta samu Amal zaune tana a kan gado tana waya jefa jakarta ta yi a kan gadon ta cire kayan jikinta ta ɗakko wata yaloluwar riga iyakar ƙwaurinta ta sanya ta kwanta rubda ciki ta jin ranta na mata wani zafi wanda ta kasa gane dalilin hakan dan ta rasa mai ke damunta, dan ita yau ɗaya kawai ji take duk ta tsani rayuwar da take yi, tun da ta gane saurayin da ta haɗu da shi a restuarant ya gane ta masa kama da wata a fuska amma ba a halayya ba kenan ita halayyarta marar kyau ce? Kenan ita ba dan kama da take masa da wata ba a fuska da bata da wani kyan hali da har zai sa a tunkareta, tabbas ta ji a yau tana sha'awar a ce ita ma wani zai iya yin abin da ta ga saurayin nan na yi a kan wata wato soyayyar gaskiya lallai hali mai kyau shi ne jigo a rayuwa shi kima da kuma martaba, amma ita mai ya sa babu wata hanya da aka nuna mata mai ɓullewa? Sai dai gurɓatacciyar hanya kuma matar da ita ce mahaifiyarta ita ya dace ta sanyata a hanya madaidaiciya amma kuma sai aka samu saɓanin hakan, shin ina mafita a ina amsar tambayarta take mai yasa Aunty ta zaɓa mata wannan rayuwar akan ta sanyata a hanyar da za ta zama abar kwatance kuma abar sha'awa ga kowa da kowa?

Wasu hawaye ne suka shiga zubo mata, bayan hannunta ta sanya ta goge shin mai yasa bata taɓa jin ƙyamatar halayyarta ba sai yau ɗin nan? Mai yasa bata taɓa jin abin da take aikatawa ba dai dai bane sai yau ɗin nan tabbas an sanyata a a hanyar marar ɓullewa.Tana a haka har aka fara kiran sallar magriba.

Wayarta ce da ke cikin jakarta ta shiga ringing amma har kiran ya katse bata É—auka ba, Amal da ta kwanta bayan ta gama wayar da take ta juya mata baya tana chart ta ce

"Wai malama bakya jin wayarki ta cikawa mutane kunne in ba za ki ɗauka ba ya kaɓata ki kashe dan ni ƙaran ya gundureni"

Shiru ta mata bata tanka mata ba, mamaki ne ya cika Amal jin Iftihal ɗin bata ce komai dan ta san dai Iftihal ba ta taɓa barin ta kwana kana faɗa mata mafana za ta baka amsa dai dai da kai, amma kuma abin mamaki yanzu ta shareta.Juyowa ta yi dan ta tabbatar idonta biyu ko kuma bacci take, amma kuma mamakinta bai ƙaru ba sai da ta ga idanunta biyu buɗe.

A dai dai nan wayar ta sake wanj wani ƙaran da alama wani kiran ne ya shigo bayan na farkon ya katse.

"Iftihal ni kam ko dai baki da lafiya ne?" Amal ta jefa mata tambayar tana tsareta da ido dan ita bata ma lura da hawayen da ke ƙara kwaranyowa daga idanuna Iftihal ɗin ba.Baki ta taɓe ta juya ta yi kwanciyarta, ita kuma Iftihal ɗin jin ba a da niyyar daina kiran wayarta ta ne ya sanya ta tashi zaune dan kiran na katsewa wani ke shigowa kuma ta san babu mai mata wannan kiran a kai- a kai sai Auntyn ta dan samarinta da abokan hulɗarta kowa ya sani ba ta son damu dan in ka dameta da kira ma tana iya yanke alaƙa da kai saboda ita ƙa'idarta ce idan har ka mata kira ɗaya biyu ka ga bata ɗauka ba to ka bari idan ta ga dama za ta bi kiran.

Cikin sanyin jiki ta tashi ta buÉ—e jakarta ta É—akko wayar, tana shirin danna ok kiran ya katse sai ga wani koran ya shigo a take, kamar yadda tunanin nata ya bata kuwa Aunty ce tana kallon sunan sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata.ÆŠaukan kiran ta yi ta kai wayar kunnenta amma ba ta ce komai ba.

"Iftihal haba ina kika shiga tun ɗazu sai kiranki nake amma shiru babu amsa, shi ma Alhajin na masa kira ya fi goma amma bai ɗauka ba daga ƙarshe ma wayar aka kashe, ko har yanzu baku baro Hotel ɗin bane kuna hutawa?"

Wani takaici ne ya rufe gabaɗaya zuciyar Iftihal jin wai mahaifiyarta ce ke mata tambaya a kan cewa har yanzu tana Hotel tana hutawa tare da dadironta, shin mai yasa bata taɓa jin zafin tambayar nan ba sai tau tun da ba yau ne ta fara mata makamanciyar tambayar nan ba? Shin ita wace irin mahaifiya gareta shin anya kuwa Aunty ta cancanta ta zama uwa, duk da an ce mahaifiyarka ko mahaukaciya ce uwa ce a gareka amma maj yasa ita tata mahaifiyar na da hankali amma ba na tunani ba tun da duk wata uwa ta gari ba za ta so ta ga rayuwar ƴarta ta lalace ba, lallai kowacce uwa mahaifiya ce amma ba kowa ce mahaifiya ba ce ke zama uwa ta gari ga ƴaƴanta.

"Wai Iftihal ya kika yi shiru ina ta sauraren ki fara min bayanin yawan kuÉ—aÉ—en da kika cafko mana a wurin Alhajin Allah, amma sai in ji kin yi shiru" Aunty ta katse mata tunanin.

"Ni fa ba ma tare da shi" Ta bata amsa a taƙaice.

"Allah sarki my Ifti ki ce har kin koma gida wato kun rabu da shi kowa ya kama gabansa, yo ai dama tun da kowa ya samu abin da yake so sai a raba garun, shi ya samu biyan buƙatarsa ke kuma kin samo mana kuɗi, wato kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba" Ta ƙarasa faɗa rana wata dariya.

"Ni fa Aunty ba mu aiwatar da wani abu ba, dan ni ko Hotel É—in ban je ba kawai dai na fasa yi...

"Ke! Dakata dallah ya ina miki magana kina sako min wani zancen banza da wofi" Auntyn ta katseta cikin ƙaraji.

Shiru Iftihal É—in ta yi ba ta ce komai ba.

"Wato duk yadda na shirya wannan haɗuwar taku sai da kika yi yadda kika yi kika ruguzata, wato duk irin yadda na so mu samu abin arziƙi mai tarin yawa sai da kika yi fatali da damar da kika samu, shin kin san waye wannan mutumin kin san irin tarin dukiyar da yake da ita, shin wai ma wace mai hure kunne kika haɗu ta hure miki kunne dan tana baƙinciki ko kuwa Amal ɗin ce ta hanaki dan tana ganin bata da irin waɗannan Alhzan?" Saurin juyawa ta yi ta kalli Amal da ke danne- danne a wayarta ba ta ma san me ake yi ba.

"Ni fa babu wanda ya hanani ni ce kawai na ga hanyar ba ta da ƙofar da za a bi a ɓulle shi yasa na fasa ...

"Shin yau shaye-shaye kika yi Iftihal? Ni kike faÉ—awa wannan maganar?"

"Aunty abin nan fa ba na zafi bane, kawai dai ni yau na duba lamarin nan ne na ga babu wani alfanu a ciki sai ɓata tarihin rayuwa yanzu na gane babu wani abu da ya dace da ƴa mace sai ɗakin mijinta, ga uwa uba neman ilimi da ni ko cikin cokali ban samu ba shin ni a haka rayuwata za ta dawwama? Shin ni haka zan zauna cikin jahilci babu arabi babu boko? Sai dai in bayar da kaina a biyani kuɗi na zama kamar wata motar haya sai dai a hau a biyani? Shin bakya jin ciwo a kan halin da nake ciki ko kuwa bakya hango mana da na sani a gaba, ko kuma bakya tunanin maganin hana ɗaukan cikin da nake sha wataran Allah zai iya jarabta ta da samun ciki shin idan cikin yaƙi zubuwa na haihu ya kike so na yi? Haka yaron zai tashi babu wani tsayayyen uba, babu wani kyakkyawan tarihi a rayuwarsa da tawa baki ɗaya mai zan cewa yaron?"

Amal da ke kwance ba ta san lokacin da ta tashi zaune ba, ta ajiye wayarta ta maida hankalinta kwacakwam kan Iftihal da ke wasu maganganu da ta kasa gane inda ta samo su, duk da ba ta jin mai ake faɗawa Iftihal ɗin amma tana jin mai Iftihal ɗin ke faɗa, maganganu masu ɗinbin kyau da dacewa maganganun da ya dace a ce fala musu su ake ba wai Iftihal ɗin ke faɗa ba, ba komai ya fi tafiya da gabaɗayan hankalinta ba sai kukan da Iftihal ɗin ke yi yayin da take maganar waya, a hankali ta ƙaraso kusa da ita ta miƙa hannu ta dafa kafaɗar Iftihal ɗin tana jin tausayin su ita da Iftihal ɗin dan yadda rayuwar Iftihal ɗin ke dabaibaye da tarin ƙalubale da aikin da na sani haka ita ma tata rayuwar ke a ƙudundune babu komai sai abin Allah wadai.

Aunty kwa da ke ƙoƙarin haɗo kalmomi da haruffan da za ta yi amfani da su wajen shawo kan Iftihal ɗin dan gabaɗaya ta ma rasa ta inda za ta fara, ta rasa mai za ta faɗa wanda zai jawo hankalin Iftihal ɗin kar ta ɗora zargi a kan ta a matsayinta na mahaifiyarta, gabaɗaya zufa ta gama wanketa sai wani zazzare idanu take tana wani kame-kame take.

"Aunty ki bani amsoshin tambayoyina"

"Uhmm haba Iftihal kinsan dai ai ba zan taɓa sanyaki a hanyar da babu wata mafita ko kuma hanyar da za ki cutu ko ki samu kan ki cikin halin da na sani, kar fa ki manta ni mahaifiyarki ce ba zan taɓa son wani abu da zai cuceki ba bare har...

"Wato yanzu wannan soyayya ce?"

"Ina zuwa bari in shiga bayi" Aunty ta faɗa cikin rawar murya dan ta san bata da amsar tambayoyin da Iftihal ke mata idan kuma suka cigaba da magana to tabbas za ta ƙureta ta yadda ma ba za ta samu bakin magana ba, tana gama faɗar hakan ta kashe wayar da sauri.
Chapter 25 · 0% Book details