Sashe 29
Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 2 min read
"Hafiz kira min mai gadi" Alhaji Sagiru ya faɗa rai ɓace.
D a sauri Hafiz ya juya tun kafin ya ƙarasa wurin mai gadin yake ƙwalla masa kira, mai gadi jin ana masa kiran mafarauta ya taso da sauri ya nufo Hafiz tun kan ya ƙaraso Hafiz ɗin ya juya ba tare da ya ce masa komai, bin bayansa ya yi cikin ruɗani dan sai yake ganin ko garin buɗe musu get ɗin ne ya yi laifi yana tsoron kar ya rasa aikinsa.
Suna ƙarasowa Alhajin ya jefawa mai gadin tambaya.
"Mai gadi yaushe Hajiya Ruƙayya ta bar gidan nan? Kai ne a bakin ƙofa dan haka nasan kasan duk mai shiga da mai fita a gidan na domin sanin hakan ya rataya a wuyanka, yaushe rabon da ka ganta yaushe ta fita da wane lokaci ta fita tau tsawon wane lokaci?
Ido mai gadin ya fara rarrabawa jin duk tambayoyin nan shi ake jiran amsar su daga gareshi, ta ina zai fara bayanin wannan dan baya so shi ma ya shiga ciki mace mai tsohon ciki tana ɗauke da cikin hakimi kuma jikokin sarki sannan babanta hakimi ƴar gata gaba da baya amma matuƙar ya shiga cikin cakwakiyar nan babu mai fitar da shi sai Allah amma tabbas zai faɗi gaskiya ko dan karamcin matar a gareshi.
"Ana tambayarka ka yiwa mutane shiru?" Abba ya faÉ—a yana kallon mai gadin ganin duk ya tsorata hakan na nuna masa akwai wani abu.
Hajiya Suwaida kwa fakar idanunsu ta yi take yiwa mai gadin gargaɗi tare da nuna masa za ta bashi kuɗaɗe masu yawa in bai faɗi gaskiya ba dan ta san ya san lokacin da Ruƙayya ta bar gidan amma kuma ba zai taɓa ambata wani abu ba har sai an nemi hakan saboda wanda za su nemi sanin haka an mantar da su ba sa cikin hayyacinsu.
Mai gadin kallon Hajiya Suwaida yake yana kuma bin fuskokin sauran mutanen da ke wurin yana tunanin mai ya dace ya faɗa gaskiya ko ƙarya?
MMN AFRAH🥰ðŸ˜ðŸ˜˜