← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Da yammaci ne garin ya yi luf kamar akwai haddiri saboda lillimi da ake yi, zaune suke a ƙarƙashin wata bishiyar maina suna kan sallayar da suka shimfiɗa ga litattafan da suka ɗakko nan domin yin karatu, saidai Ridallah ta buɗe nata littafin a zahiri idan ka ganta zaka ɗauka karatun take amma a baɗini ba wai karatun take ba kawai dai tana kallon littafin ne amma ko rubutun bata iya karantawa sai hoton Ya Hizbullah kawai take gani yana mata murmushi hakan yasa idanunta suka ciko da ƙwalla saboda kwana biyun nan sosai tunaninsa ke addabarta tana ta ƙoƙari ta yakice tunaninsa da son ganinsa daga zuciyarta amma hakan baya samuwa.Anisa da ta ga wani wuri bata fahimta ba a cikin littafinta tana so Ridallah ta mata bayani ta ɗago tana mata magana tare da nuna mata rubutun. Amma duk maganar da take mata bata ko da kalli inda take ba bare kuma ta san ran za ta bata amsa.

Sororo ta tsaya tana kallonta ganin hawaye na ɗiga a kan littafin da ke hannunta, hannu ta sanya ta taɓota, figigit ta yi tana kallon Anisa tare da sanya hannu ta goge hawayenta.

"Haba ƙawata mai yake damunki ne haka har da kuka, ko Babanki kika tuno da ya rasu?"

"Allah sarki! Addu'ar da nake yiwa Babana ba ta bari na masa kuka, sai dai kawai idan na tuna da Yaya na ina jin a jikina yana can cikin damuwa kamar yadda nake jin damuwar rashin sa"

"Dama kina da Yaya amma baki taɓa bani labarinsa ba? To yana ina?"

"Ya Hizbullah ba iyayen mu ɗaya ba, maƙotanmu ne sai dai na shaƙu da shi yadda bakya zato"

"Allah sarki ! Amma wata rana zai zo ki daina damuwa ki maida hankali muke karatun mu"

"To shikenan nagode" Ridallah ta ce tana goge hawayen nata, ta nunawa Anisa inda bata gane ba suka cigaba da yin karatunsu abin sha'awa dan basu da wata damuwa kuma ma da yake su ƴan J.s 1 ne babu mai takura musu komai ma musu ake barw da aka san Ridallah akwai mahaifiyarta a makarantar ba a takura mata ga kuma an ga Malamai da Shugaban makarantar suna ji da ita saboda ƙwazo da kuma girmama mutane.

_Aunty_

Gobe ne jirgin su Iftihal zai ɗaga zuwa ƙasar Chaina ita da Abie za su je idan ya kaita akwai wani abu da zai gabatar sai ya dawo.Dan haka sai shirye-shirye ake tsakanin uwa da ƴa, saboda tsabar dabbanci irin na Auntyn har kayan mata ta haɗawa Iftihal ɗin domin ta gyara kan ta na kasa gane Aunty wace irin uwa ce da ta zama mabuɗin lalacewar ƴarta da hannunta saboda aon abin duniya. Ita kuma Iftihal saboda Auntyn na nuna mata wannan ita ce hanya mai ɓullewa hakan yasa take ganin kamar daidai ne ga kuma uwa uba yarinta da ke damunta ga rashin ilimi hakan yasa ta kasa gane gaskiya kamar yadda mahaifiyarta ta kasa ganewa.

Dama tun anan tana bata kayan mata tasha domin Alhazan da ke nemanta su ke bata kuɗaɗe marar misali su kuwa da yake ƴan akuyoyi ne haka suke more yarintarta da kuma kayan matan da ke ƙara musu armashin wajen yin saɓon Allah, Allah ka tsaremu ka tsare mana zuri'a baki ɗaya amin.Komai ta sanya mata a jakarta sannan ta ƙara koya mata abubuwan da za take ɗauke hankulan maza dan haka sai da ta shirya komai sannan kuma sun yi magana da Hajiya Suwaida akan Hajiya Wasila za ta ɗora daga inda aka tsaya.

Washe gari haka su Aunty suka raka su Airport basu dawo ba har sai da suka ga tashin su, sosai Aunty ke cike da farinciki dan tana ganin wannan wani cigaba ne da ya shigo rayuwarsu tabbas tana ganin nasara yanzu a duk abubuwan da ta sanya a gaba bata ganin duhu saidai haske!.

Sun sauka a Chaina lafiya, a inda Alhaji Sani da da Hajiya Wasila suka je taryensu Airport ɗin, sun yi murnar ganinsu saboda sun ga yarinya kyakkyawa duk da ita Hajiya Wasila haihuwarta biyu amma sun rasu sai ƴar mijinta da take a hannunta ita ma kuma ba wai tana mata riƙo bane na tsakani da Allah, ita ma ta maida yarinyar jarinta ba tare da sanin uban ba.Sun ƙaraso gidan a inda aka nunawaSun ɗakkosu sosai Amal ke murna ganin ta samu ƙawa sai janta take da hira da yake motoci biyu suka je da su ɗaya mai gidan ne a baya direba yana jan sa, sai Abie ya shiga baya, ɗayar motar kuma Amal ce a gaba sai Hajiya Wasila a baya ita da Iftihal ta kwantar da Iftihal ɗin a gefen kafaɗarta murna fal ran Hajiya Wasila da ta ga Iftihal ɗin ganin tsantsar kyau kamar ita ta yi kan ta ko ina a cike hakan yasa take hango ɗinbin nasara a tafiyar tasu dan ta lura tabbas yarinyar za ta kawo haske sosai sama da hasken da ta samu a tafiyarta da Amal tun da tana ga manyan mutane sun fi son ƙananun yara a Barker bariki hakan ya kan sanya su fitar da kuɗaɗe dan biyan buƙatarsu.

Iftihal sai ƙarewa ko ina kallo take tana mamakin yadda kowa yake sabgar gabansa ba tare da ya damu da kowa baDuk da cewa ba wannan ne karonta na farko ba zuwa China amma lokacin da ta taɓa zuwa tana ƙatama sosai suka zo, shi yasa bata iya tuno komai game da ƙasar dan ko umra ma da suka taɓa zuwa yanzu ba z a ta ce ga yadda saudiyya take ba shi yasa yanzun ma take ganinta a China kamar a cikin mafarki.Ta shagaltu da ganin garin sosai har dai suka ƙaraso gidan Alhaji Sani Habu ƙayataccen gida ne dan haka irin tsarin ginin ya burgeta, tun tsayuwar motocin mai gadin yana buɗe get ɗin ta shiga ƙarewa gidan kallo dan lokacin da ta taɓa zuwa China a Hotel suka sauka kuma ko ma a nan gidan suka sauka to babu abin da za ta iya tunawa duk da yanzun ma ba wani girma gareta na azo a gani ba amma dai tana jin kan ta kamar yadda kowacce mace ke jin kan ta.

Part ɗin da aka sauki Abie da ban ita kuma Amal ta kai ta wani ɗakin da ke ɗauke da komai na buƙata, bayan ta ɗana watsa ruwa ta shirya Amal da ke zaune kan gado tana ta danna waya ta kalleta ta ce

"Masha Allah rigar nan da kika sanya ta matuƙar miki kyau kamar dama dan ke aka ƙerata"

Tsayawa Iftihal É—in ta yi, tana bin Amal da kallo kafin daga bisani ta É—an yatsina fuska cikin halin ko in kula ta ce

"Thanks"

Murmushi Amal ta yi dan ita har ran ta take jin ƙaunar Iftihal dan haka bata ga laifinta ba.

"Ya gajiyarki"

"Bani da gajiya"

"Haka ake so"

Wayar Amal ce ta ahiga ruri tana dubawa ta ga Mummy, É—auka ta yi.

"Ku fito aci abinci" Ta tsinkayi muryar Hajiya Wasila.

"To Mummy gamu nan fitowa" Tana gama faÉ—in hakan Mummyn ta katse wayar kallonta ta maida kan Iftihal da ke gyara ribbon É—in kan ta ta ce

"Mummy ta ce mu je mu ci abinci"

"Okay" Ta ce tare da miƙewa tsaye tana ɗaura ɗankwalin doguwar rigar a kan ta, ta kama hanyar ƙofa Amal ta bi bayanta suka fito. A dinnig area suka samu gabaɗaya mutanen gidan har da Abie kowacce kujera ta ja ta zauna kowa ya zuba abin da yake so Mummyn kuma ta zubawa su Abie itama ta zuba nata aka shiga cin abincin, bayan sun kammala Abie da Daddy Alhaji Sani suka fita domin su ɗan zagaya gari sai murna suke domin sun ɗan kwana biyu basu haɗu ba.Suna fita Mummy ta kira su Iftihal ɗin falonta ta shiga kora musu bayani kamar haka.

"Amal ga ƙawa nan kuma ƴar uwa inaso ku zama tamkar abu ɗaya, bana so wani abi marar daɗi ya shiga tsakaninku dan sai kun haɗe kan ku sannan komai zai tafi kamar yadda nakeso na tsara" Cewar Mummy tana bin dukkanninsu da kallo.

"To Mummy insha Allah babu wata matsala da za a samu dan ni tun da na ganta na ji ta shiga raina sosai" Amal ta ce tana murmushi.

"Yawwa Amal haka nake son ji"Mummy ta ce tana maida hankalinta kan Iftihal da babu alamun za ta ce wani abu ta lura yarinyar Æ´ar rainin wayo ce kuma da ganin idonta ta wanke a bariki dan kar take kallon mutane.

"Babu abin da zai haÉ—amu"Iftihal ta ce tana maida hankalinta kan wayarta.Shiru ne ya É—an biyo baya Mummy kuwa a ranta tana cewa

"Yarinya za ki shigo hannu ne, dole na moreki tun da a hannu na za ki zauna dole na samu kuÉ—aÉ—e ta dalilinki.

"Mummy ina son na É—an huta" Amal ta ce cikin girmamawa, dan dama Amal yarinya ce mai biyayya duk da yanzu Mummy ta yi nasara wajen kassara mata rayuwa ba tare da sanin mahaifinta ba amma dai ha yanzu tana girmama na gaba da ita.

"To Amal ku je maza ku huta "Mummy ta ce tana murmushin yaƙe, haka suka tashi suka juya suka bar falon Mummy na bin su da ido tana girgiza kai tare da yin ƙwafa.

Sati guda Abie ya yi ya dawo Nigeri'a dan sai da aka gamawa Iftihal komai da komai na makaranta sannan ya taho dan har lesson teacher aka ɗaukar mata dan yake koya mata karatu a gida saboda duk babu abin da ta iya saboda rashin halartar makaranta da ba ta yi. A makarantar da aka sanyata ma ta su Amal da ƙer suka yarda suka sanyata a J.s 1 shima dan su Abie sun ɗan musu magiya akan za su ɗaukar mata da wanda zai ke koya mata a gida dan da suka mata interview duk ba ta ci ba, gashi kuma duk ta fi ƴan sauran ajijiwan bayan girma da yake tana da girman jiki doke dai haka aka sanyata a J.s 1 ɗin.
Chapter 15 · 0% Book details