← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 24 OF 29

Sashe 24

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Amal da ke kwance ba ta san lokacin da ta tashi zaune ba, ta ajiye wayarta ta maida hankalinta kwacakwam kan Iftihal da ke wasu maganganu da ta kasa gane inda ta samo su, duk da ba ta jin mai ake faɗawa Iftihal ɗin amma tana jin mai Iftihal ɗin ke faɗa, maganganu masu ɗinbin kyau da dacewa maganganun da ya dace a ce fala musu su ake ba wai Iftihal ɗin ke faɗa ba, ba komai ya fi tafiya da gabaɗayan hankalinta ba sai kukan da Iftihal ɗin ke yi yayin da take maganar waya, a hankali ta ƙaraso kusa da ita ta miƙa hannu ta dafa kafaɗar Iftihal ɗin tana jin tausayin su ita da Iftihal ɗin dan yadda rayuwar Iftihal ɗin ke dabaibaye da tarin ƙalubale da aikin da na sani haka ita ma tata rayuwar ke a ƙudundune babu komai sai abin Allah wadai.

Aunty kwa da ke ƙoƙarin haɗo kalmomi da haruffan da za ta yi amfani da su wajen shawo kan Iftihal ɗin dan gabaɗaya ta ma rasa ta inda za ta fara, ta rasa mai za ta faɗa wanda zai jawo hankalin Iftihal ɗin kar ta ɗora zargi a kan ta a matsayinta na mahaifiyarta, gabaɗaya zufa ta gama wanketa sai wani zazzare idanu take tana wani kame-kame take.

"Aunty ki bani amsoshin tambayoyina"

"Uhmm haba Iftihal kinsan dai ai ba zan taɓa sanyaki a hanyar da babu wata mafita ko kuma hanyar da za ki cutu ko ki samu kan ki cikin halin da na sani, kar fa ki manta ni mahaifiyarki ce ba zan taɓa son wani abu da zai cuceki ba bare har...

"Wato yanzu wannan soyayya ce?"

"Ina zuwa bari in shiga bayi" Aunty ta faɗa cikin rawar murya dan ta san bata da amsar tambayoyin da Iftihal ke mata idan kuma suka cigaba da magana to tabbas za ta ƙureta ta yadda ma ba za ta samu bakin magana ba, tana gama faɗar hakan ta kashe wayar da sauri.

Kallon wayar kawai Iftihal ke yi hawaye na kwaranya daga idanunta, dan ta san da gangan Auntyn ta kashe wayar dan ko amsarta ba ta jira ba a kan neman uzurin shiga bayin da ta yi na ƙarya.Ajiye wayar ta yi jikinta sanyi ƙalau, ta juya ta kalli Amal da ke dafe da kafaɗarta wacce ita ma tuni hawayen sun wanke mata tata fuskar.

Rungume juna suka yi suna kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.Sai da suka yi kukan su suka ƙoshi sannan Iftihal ɗin ta ce su tashi su yi sallah, sallar da duk cikinsu babu wacce za ta iya tuna rabonta da ta yi sallah dan a taƙaice ma ba yin sallar suke ba.

Haka suka yi alwala suka zo yin sallah abin takaicin duk su biyun babu wacce ta iya karatun sallar dan babu ilimi dan dama ba a san a je makaranta ba sai tsantsar jahilci.Bayan sun duddugura suka zauna suka yi shiru kamar daga sama sai ganin Mummy suka yi ta hankaɗo ƙofar kamar an jefota, tana shigowa ta maida ƙofar ta rufe ta tsaya tare da kama ƙugu ta ce

"Wai dama Iftihal kin dawo gidan nan amma shi ne saboda tsabar kin raina ni shi ne baki neme ni ba, wato ni za ku rainawa wayo daga ke har uwar taki, shi ne kuka riƙe kuɗin ita ma ko kirana ba ta yi ba shi ne ke ma kika shigo ɗaki har da wani yin sallah da ban da munafurci sallah kuke? Ki tashi ki ɗakko nawa kuɗin ki bani kaso na"

Tashi tsaye Iftihal ɗin ta yi ta cire mayafin doguwar rigar da ta sanya tare da doguwar rigar ta gabatar da sallah, ɗaurawa ta yi a kan ta ta tako har gaban Mummyn ta tsaya ta ce cikin ƙaraji da ɗaga murya.

"Kowa kuÉ—i, maganarku É—aya kuÉ—i, baku da magana sai ta kuÉ—i, shin ku bakwa tunanin yadda rayuwarmu za ta kasance ku dai burinku ku saku kuÉ—i"

Baki sake Mummyn ke kallonta dan gabaÉ—aya kalaman yarinyar sun kusa sanyawa ta nuna rashin gaskiyarta a fili

"Wace magana kike yi ne wai Iftihal?"

"Ba kuÉ—i kika zo in baki ba wanda na samo a yawon karuwanci!"

MMN AFRAH🥰😍❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

Page 4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣

*IFTIHAL*

Suna fitowa ita da Alhajin daga Restuarant ɗin ta ja ta tsaya, shi kuma ganin tana wani shan ƙamshi tana haɗe rai sai duk ya ji ba daɗi, amma hakan bai sanya ya ji ko da haushinta ba shi dai kawai so yake buƙatarsa ta biya.

"Kinsan fa wani abokina da ke zaune a nan ne ya sanya direbansa ya kawoni yanzu kuma sai dai mu shiga taxi mu je Hotel ɗin in kama mana ɗakin da za mu huta ko baby?" Ya faɗi hakan yana wani murmushi tare da washe haƙora sai wani lasar baki yake kamar wani tsohon maye.Ƙasa ta yi da glases ɗin nata ta masa kallon up nd down ta sauke idanunta a kan ƙaton tumbinsa tari guda kamar mai cikin wata tara, ɗauke kai ta yi gefe tare da maida glases ɗin nata yadda yake ta ɗago wayarta ta duba time.

"No kar ma ki yi la'akari da wannan cuki ba wai tsufa bane ya sanya y yi girma hakan tsabar cin daÉ—i ne da kwanciyar hankali kinsan idan akwai kuÉ—i to mutum bashi da matsala sai wacce ba a rasa ba"

"Ok ni ai ka san daga gidan talauci na fito"

"Ba haka nake nufi ba baby, inaso na sanar da ke yau idan ki ka tashi tafiya za ki tafi da maƙudan kuɗaɗe wanda kowa sai ya san kin yi tarayya da wanda ke matashin kai da kuɗi" Ya faɗa yana washe baki.

Jin ba ta ce komai ba ya sanya ya ƙara cewa

"Mu je ko muna ɓata lokaci" Dan shi gabaɗaya wannan shan ƙamshin da take burgeshi take yi sabod yana son ya ga mace mai aji ya fi son hakan dan an fi daidaitawa da shi.

Ita ta fara yin gaba, ganin ta nufi wajen wata mota da ke fake a wurin ya gane cewa da mota ta zo, hakan ya ƙara tabbatar masa da babban yarinya ce saboda har mota gareta ta kan ta.Suna isa ta sanya mukullin ta buɗe ta shiga wurin direba ta zauna sai dai ƙafafunta a waje suke, jakarta ta jefa kan ɗaya sit ɗin mai zaman banza, shi kuma cikin sauri ya nufi ɓangaren mai zaman banzan zai buɗe ya shiga sai washe haƙora yake kamar gonar auduga.

Iftihal na ganin ya gewayo ta maida ƙafafunta cikin motar ta rufe ƙofar, gabaɗaya ta kulle motar Alhajin na kama ƙofar zai buɗe ya ji ta a kulle, ƙwanƙwasawa ya yi amma maimakon ta buɗe sai ta sauke glass ɗin ta sanya hannu ta yi ƙasa da glases ɗin fuskarta ta masa wani kallon ƙasƙanci ta ce

"Malam ka bar min jikin mota tun kafin in tasheta in yi gaba in kuma yi reverse in kwasheka kuma na kwashe banza wallahi"

"Haba baby wace irin magana kike haka? Idan ma wasa kike ki bari kar kisa ruwana ya hau, dan na gama É—ora rai a kan ki wallahi"

"Za ka ga wasa da zarar na take ka, kuma sai dai hawan jininka ya tashi ba wai hawan ruwa ba"

"Dan Allah ki buÉ—e in shigo mu tafi...

"Kai na fasa zuwa ko ina da kai" Ta katse shi.

"A haba dai haba baby ya zaki min haka"

"Bani da lokacinka" Tana gama faɗar hakan ta ɗaga glass ɗin motar, ta mata key, Alhajin kuwa ya daddafe motar har sai da ya ji ta fara tafiya, ya ja baya ganin ta fisgeta da sauri ya tare taxi ya bi ya ce mai taxi ɗin ya bi bayan motar, tun suna bin bayansu har suka nemi inda motar ta yi suja rasa aikuwa Alhajin kamar ya cinye direban taxi ɗin sai masifa yake masa da turanci dan ba jin hausa yake ba daga chinanci sai ko turanci.Shi dai haƙuri yake bashi yana faɗa masa cinkoson motoci ne ya sanya motar ta ɓace masa, haka dai ya kaishi wani hotel ya yiwa wata waya dan ya rage zafi da ita saboda ɗora rai Allah sa mu fi ƙarfin zukatanmu.
Chapter 24 · 0% Book details