← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 4 OF 29

Sashe 4

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Wata tsawa da Hajiya Hauwa ta dokawa Safiya ita ta dakatar da ita daga shirin dukan da take ƙoƙarin ta kaiwa Iftihal, wani tsoro ne ya ziyarci Safiya dan sai a lokacin ta ji a ranta cewa lallai da ta kaiwa Iftihal dukan to tabbas da ta yi babban kuskure, dan wataƙila kafin ta rasa aikin nata sai ta fara rasa ranta dan tsaf Hajiya Hauwa za ta mata dukan mutuwa akan Iftihal.

"Wace irin marar hankali ce ke in ban da jakanci da jahilci maimakon ki yi saurin tafiya ɗaukan mopa da ruwa ki zo ki goge wurin shi ne kika tsaya kina kallon Iftihal ɗin sai ka ce wanda ta yi wani abu, ko dan baku san darajar kuɗi ba saboda baku da su shi yasa za ki bar min capet da ruwan shayi a jiki sai ya dafe yaƙi fita" Aunty ta ce tana wani zazzare ido tana bala,i.

"Ki yi haƙuri Hajiya yanzu zan gyara" Safiya ta ce tana ɗaukan kanukan ta nufi kicin domin ta ajiye su, ga wani zafi da raɗaɗi da fuskarta da ƙirjinta ke yi dan shayin akwai zafi amma saboda rashin imani na Hajiya Hauwa maimakon ta tausaya mata shi ne take mata faɗa bayan Iftihal ya kamata ta yiwa faɗan amma saboda sangarci da kuma ganin suna da kuɗi za su iya taka kowa ma hakan ya sa ta zamar da ƴarta ta sangartacciya.Sai da Safiya ta tsaya ta share ƙwallar da ta zubo mata tana da na sani akan aiki a ƙarƙashin Hajiya Hauwa da bata da mutunci ko kaɗan bare tausayi, bata koyi da sobar zamanta Hajiya Azima mata mai kima da darajanta ɗan adam pan aikinta tamkar ƴaƴanta haka ta ɗaukesu ba kyara ba tsangwama.

Tana ta saƙar zuci ta dawo falon ɗauke da mopa da burket da ta haɗo ruwa mai ɗauke da morning fresh, ta shiga goge wurin, lokacin Auntyn na lallashin Iftihal akan ta yi haƙuri za a haɗa mata wani tea ɗin marar zafi sosai marar madara da yawa.Wani haushi da takaici ne ya turnuƙe Safiya tana Allah wadaran naka ya lalace ace maimakon uwa ta zama turba na gina rayuwar ƴaƴanta akan hanya daidaitacciya mai ɓullewa wajen basu kyakkywar tarbiya amma shi ne ita Aunty ta zama mai bada gudunmuwa wajen taɓarɓarewar tarbiyar ƴarta, babu abin da yarinyar ta sanj sai sangarta.

"Dalla malama ki yi sauri ki gama ki haÉ—a mata wani tea É—in"Cewar Auntyn cikin zafin rai.

"To Hajiya" Safiya ta amsa mata, bayan ta ɗakko freshner ta fesa a wurin saboda ƙarnin madarar sannan ta ɗauke kayan da ta yi amfani da su wajen gyara wurin, kicin ta koma ta ɗauki gishiri ta shafa a wurin da aka watsa mata shayin dan da alama ma kamar wurin zai tashi, bayan ta shafa sai kuma ta wanke hannunta ta sake haɗa shayin marar zafi sai dai yana da ɗan ɗumi sannan ta fito ta zo ta durƙusa ta miƙawa Iftihal ɗin, tun da ta ce da kan ta za ta sha.

Ƙin karɓar shayin ma ta yi tana kallon tv, kamar ma ba ita ake baiwa shayin ba, Auntyn kwa tana kallo ko ta yiwa Iftihal ɗin magana.

"Ga shayin na sake haɗa miki"Safiya ta ce da ta fahimci bata da niyyyar karɓa.

Banza ta yi da ita, can kuma a shelaƙe ta karɓa, kurɓa ɗaya ta yiwa shayin ta ɗaga ta watsar da shi, ta yi jifa da kofin ya tarwatse dan dai ma akan tiles ne ba akan capet ba.Safiya kai ta sunkuyar tana jin a ranta cewa lallai neman halal da wuya musamman a ƙarƙashin wanda ba su san kima da darajar ɗan adam ba.Hatta Hajiya Hauwa ranta ya matuƙar ɓaci da abin da Iftihal ɗin ta yi amma saboda bata so ta nuna mata hakan duk da cewa ita ce ta ɓata yarinuar gashi bata son kwaɓarta sai kawai ta danne zuciyarta ta ce.

"Wai Safiya baki san aikin ba? Komai sai an faÉ—a miki kenan? Ba za ki kula ki gyara wurin ba sai ki wani sunkuyar da ka kamar mai yin zaman tahiya yayin gabatar da salla.

"Ki yi haƙuri Hajiya yanzu zan gyara" Haka Safiya ta share wurin wurin ta goge tas, sannan ta ɗore wasu ayyukan dan wuni ake ana aiki ba kama hannun yaro.

Da daddare zaune suke su duka iyalin gidan a dinning area domin gabatar da dinner, Hajiya Azima sanye take da wani leshi purple colour an mata ɗinkin buba ta ɗaura ɗankwalinta ta sanya sarƙa da ɗankunne na gwal sai sheƙi suke ga warwaraye da zobuna sai zuba ƙamshi take tamkar dai mai shirin zuwa wani gagarumin biki ko suna. Hajiya Azima mace ce mai son ado da kwalliya gata da matuƙar tsafta, hakan shi ke ƙara wutar soyayyarta a wurin mijinta yake kuma ƙara rura wutar tsanarta a wurin sobar zamanta Hajiya Hauwa dan ta tsani duk wasu abubuwan da Hajiya Azima ke yi.

Alhaji, Hajiya Azima sai Hajiya Hauwa su ne a wurin kowa zaune yake Iftihal kawai ake jira a fara cin abincin domin komai ya kammala dan kuku ya shirya musu komai da komai duk da kasancewar Hajiya Azima mai son take yin girki da kan ta amma fitinar da Hajiya Hauwa ke tadawa yasa Alhajin dakatar da ita, dan dama ita duk ranar girkinta ita ce ke yin girki, ita kuma Hajiya Hauwa sai dai aci girkin kuku dan dama bata wani ƙware a girki ba gata kuma da son jiki, to idan Hajiya Azima ta yi girki ranar girkinta sai Hajiya Hauwa ta ringa sanabe tana cewa gishiri ya yi yawa ko dai an cika yaji ita ulcer ta za ta tashi kuma duk gassada ce dan ta ga Alhajin yana ta yabon abincin idan ana ci.Irin fitintinun da take yasa ya dakatar da Hajiya Azima da yun girki akan a bar kuku yana yi domin shi ma kukun nasu gwani ne a wurin iya girki babu abin da bai iya ba.

"Ke dai bakya gajiya da caɓa ado kamar mai shirin zuwa gidan biki"Alhajin yace yana yiwa Hajiya Azima wani kallo ƙasa-ƙasa.

Murmushi ta yi kafin ta ce

"Ai indai abu ne zan yi dominka bana taɓa gajiyawa da shi, bare kwalliya ai ni kai ne gidan bikin nawa, matuƙar na yi abin da ya birgeka to tabbas kwalliya ta biya kuɗin sabulu"

"Ai ba ma kuɗin sabulu ba harda kuɗin soso" Yace suna dariya su biyun ban da Hajiya Hauwa da ta cika ta yi fam sai bin jikinta take da kallo sanye take da baƙar doguwar riga sai ɗankwalin rigar da ta ɗaura shi ya yi baya,ko ɗankunne babu a kunnenta, ita dama ta gaji da yin wata kwalliya duk shigar da za ta yi ko wacce irin sutura za ta sanya sai ta ga bata yi mata kyau kamar yadda kayan ke yiwa Hajiya Azima.

Ji ta yi kamar ta tashi ta bar wurin saboda tsabar takaici kamar sun manta cewa tana zaune a wurin.Wata hararar ƙasan ido take bin su da ita su duka biyun.

"Assalamun alaikum" Safiya da ke goye da Iftihal ta yi sallama.

Hajiya Azima ce ta amsa mata sallama, ƙarasa shigowa ta yi sai da ta zo har wurin nasu sannan ta sauke Iftihal ɗin ta ja kujera ta zaunar da ita sannan ta juya ta fita dan idan Alhaji yana nan ba ya bari a baiwa Iftihal abinci a baki cewa yake a barta ta ci da kan ta.

"Iftihal É—ina barkan ki da dare" Alhaji ya ce yana kallonta da murmushi.

"Abie ina yini" Ta faÉ—a tana rufe fuska dan ta san ya fala mata cewa yaro ne yake fara gaishe da babba amma ita mantawa take in ma ba Abie ya faÉ—a mata ba idan sun haÉ—u, mantawa ma take akwai wani abu gaisuwa saboda Hajiya Hauwa bata koya mata gaishe da mutane.

"Lafiya ƙalaw my daughter bakya gaishe da mutane sai sun roƙa ko?"

Shiru ta yi tana rufe fuska da hannayenta.

"To ni kaÉ—ai za a gaishe dani ?"Abie ya jefa mata tambayar dan shi mutum ne shi mai son ya ga yaronsa ya tashi cikin tarbiya.

"Momma ina yini" Iftihal ta gaishe da Hajiya Azima dan dama Momma take kiranta.

"Lafiya law iftihal" Cewar Hajiya Azima tana sakar mata murmushi.

"Aunty ina yini" Ta juya tana gaishe da Hajiya Hauwa.

"Lafiya" Hajiya Hauwa ta amsa a taƙaice, a wani daƙile kamar an mata dole.

Daga haka Hajiya Azima ta shiga zubawa kowa abincin amma Hajiya Hauwa da kan ta, ta zuba nata, aka shiga ci Iftihal na ci da kan ta ashe dama rainin wayo ne ace komai sai an bata a baki dan tsabar sangarta.

A haka suka kammala cin abincin, Hajiya Hauwa ta riga kowa tashi ta bar part ɗin ma baki ɗaya, su kuma suka koma cikin falon suna hira abin su cikin farinciki Abie na tambayar Iftihal batun zuwa islamiya ta ce bata je ba anan take faɗa masa yadda suka yi da Aunty da safe da ra mata zancen zuwa school.Ran shi ta ɓaci sosai da ya ji bata je islamiya ba hakan yasa ya ɗauki alƙawarin gobe da wuri zai fito domin Iftihal ɗin ta tafi makaranta dan ya fahimci cewa Hajiya Hauwa da gaske ba ta son barin yarinyar ta raɓi ilimi kowane iri sai nuna mata soyayyar banza da shagwaɓata na wofi wanda hakan bashi da wani amfani.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Page 11&12

_Washe gari_

Tun wajen ƙarfe shida da rabi Abie ya sakko ƙasa, ko Hajiya Azima bata sani ba dan bayan ya dawo daga masallacin asuba da suka ɗan taɓa karatun qur'ani sai suka koma suka kwanta shi ne bacci ya ɗauketa.Part ɗin Hajiya Hauwa ya nufa, nocking ƙofar ya shiga yi amma shiru ba a buɗe ba dan babu alamar motsin mutum ma bare ya sa ran za a buɗe, wayarsa ya koma ya ɗakko sannan ya dawo ya shiga kiran Hajiya Hauwa, sai da ya kira sau uku amma ba a ɗauka ba.
Chapter 4 · 0% Book details